An cafke mutum 15 kan zargin fashi da ƙwacen waya a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a, Gusau

Kwamitin Yaƙi da ‘Yan Daba na Jihar Zamfara ya kama wasu mutum 15 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da fashi da makami, sace-sacen waya da sauransu a Gusau, babban birnin jihar.

Kwamandan kwamitin, Bello Mohammed Bakyasuwa ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ofishinsa ranar Litinin.

A cewarsa, an gabatar da waɗanda ake zargin a gaban majalisar tuntuɓar malamai ta jihar domin yi musu nasiha da ja-gora domin su zama jakadu nagari a yankunansu.

Bakyasuwa ya bayyana cewa, kwamitinsa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an kassara duk wani nau’in ‘yan daba, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran laifuffukan da ke da alaƙa da su.

“Kwamitin Yaƙi da ‘Yan Daba na jiha da ke ƙarƙashina gwamnatin jihar ce ta kafa kwamitin zartarwa mai lamba biyu wanda ya bai wa Gwamnan jihar ikon magance duk wani nau’i na rashin tsaro ko wasu batutuwan da ke da alaƙa da su da ka iya haifar da tarzoma a jihar,” in ji shi.

Da yake jawabi ga waɗanda ake zargin domin bayar da shawarwari a madadin Majalisar Tuntuɓar Malamai ta jihar, Mashawarci na Musamman ga Gwamna Bello Mohammed Matawalle kan Ƙungiyoyin Addinin Musulunci da Hukumar Karatun Alƙur’ani, Sheik Balarabe Zawiyya, ya shawarci waɗanda lamarin ya shafa da su ji tsoron Allah a dukkan ayyukansu.

A cewarsa, Musulunci bai goyi bayan duk wani nau’i na aikata munanan dabi’u ba, ko kuma tarnaki a tsakanin Musulmi a cikin al’umma, inda ya buƙace su da su ji tsoron Allah a kodayaushe, su lura cewa rana za ta zo da kowa zai yi lissafin abin da ya aikata a gaban Allah na alheri ko akasin haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *