An kashe ƙananan yara 2,515 a shekarar da ta gabata – Majalisar Ɗinkin Duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya za ta gudanar da bincike game da kisa da kuma raunin da aka yi wa ƙananan yara a ƙasashen Ukraine da Habasha da Mozambique.

Babban Magatakarda na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana haka a cikin wani sabon rahoto da aka fitar, wanda ya gano cewa, ƙananan yara 2,515 ne aka kashe, sannan aka raunata dubu 5,555 sakamakon tashe-tashen hankulan da suka auku a bara.
Rahoton na shekara-shekara mai taken ƙananan yara da rikici’ wanda aka wallafa a Litinin ɗin nan, ya kuma tabbatar cewa, lallai yara dubu 6, 310 ne aka tilasta musu taka rawa a yake-yaken da aka gani a bara a sassan duniya.

Kazalika rahoton ya ƙara da cewa, akwai wasu nau’ukan keta haƙƙoƙin yara da aka yi kamar sace su ko kuma lalata da su, baya ga ƙaddamar musu da farmaki a makarantu da asibitoci, sannan kuma aka qi ba su agajin gaggawaa a lokacin tashe-tashen hankulan.

Sai dai keta haƙƙoƙin ƙananan yaran da aka tabbatar, ya fi ƙamari a ƙasashen Yemen da Syria da Afghanisan da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Congo da Somalia da Isra’ila da kuma yankin Falasdinu.

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce, nan da shekara mai zuwa, za su bada tabbacin irin girman cin zarafin da aka yi wa ƙananan yaran a ƙasashen Ukraine da Habasah da Mozambique a sabon rahoto na gaba da za a saki a badi.