Daga CMG HAUSA
Babban darektan hukumar kula da manyan tituna ta ƙasar Aljeriya Mohamed Khaldi ya yaba da ingancin aikin babbar hanyar mota da wani kamfanin ƙasar Sin ta shimfiɗa a ƙasar, da kuma gudummawar da kamfanin yake bayarwa wajen raya zamantakewa da tattalin arzikin mazauna yankin.
Babban darektan ya bayyana cewa, hanyar mai tsawon kilomita 53 da kamfanin gine-gine na ƙasar Sin CSCEC ya aiwatar, ya sauƙaƙa ci gaban zamantakewa da tattalin arziki yadda ya kamata, da rage kudin sufuri, da kuma inganta harkokin tafiye-tafiye na mazauna yankin.
Khaldi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da mambobin kwamitin tuntuɓar juna a kan babbar hanyar Sahara, yayin rangadin wani kaso na mashigar hanyar da ta wuce zuwa yankin Sahara mai tsawon kilomita 53, aikin da ya shafi nahiyar da ya haɗa ƙasashen Afirka shida, wato Aljeriya, da Chadi, da Mali, da Nijar, da Najeriya, da ƙasar Tunisiya.
Baya ga ƙarin jimillar tsawon sama da kilomita 9,000, babbar hanyar ta ƙunshi sashin Algiers-Lagos, wanda ke da tsawon kusan kilomita 4,500.
Domin gina sashen, kamfanin CSCEC ya samar da ayyukan yi sama da 10,000 a Aljeriya tare da horar da kwararru sama da 2,000 a fannin gine-gine, kamar yadda alƙaluman da kamfanin ya fitar suka nuna.
Fassarawar: Ibrahim