Anambra: ‘Yan sanda sun bankaɗo gidan da ake safarar jarirai

Daga AISHA ASAS

Rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra, ta ce ta gano wani gida da ake yi zargin ana safarar jarirai a cikinsa a Nnewi cikin ƙaramar Nnewi ta Arewa a jihar.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, CSP Haruna Muhammed ne ya bada sanarwar haka, yana mai cewa wadda ake zargin ita ce mai masana’antar jariran, Ms Gladys Nworie Ikegwuonu ta tsere sannan an kuɓutar da ‘yan mata masu juna-biyu su huɗu.

Jami’in ya ce sun yi nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargin suna da alaƙa da harƙallar. Ya ci gaba da cewa sun gano masana’antar ne biyo bayan binciken da suka gudanar a lokacin da aka yi ƙoƙarin yin garkuwa da wani yaro ɗan shekara huɗu a kan hanyarsa ta dawowa daga makaranta a ranar 11 ga Maris.

Bayanan ‘yan sandan sun nuna kwanankin baya babban ofishin ‘yan sanda da ke Nnewi, ya samu rahoton wasu mutum biyu a kan babur sun yi awon gaba da wani yaro ɗan shekara huɗu. Sai dai an samu wasu da suka taimaka suka bi sawun ɓarayin wanda a ƙarshe suka kama su a ƙauyen Akamili, Nnewi.

Mutum biyun da aka cafke su ne, Abuchi Ani, ɗan shekara 32 daga yankin Ohaozora, jihar Ebonyi, da kuma Emeka Ikegwuonu mai shekara 49, ɗan asalin yankin Akabukwu, Nnewi, jihar Anambra.

Sai kuma ‘yan mata huɗu masu ɗauke da juna-biyu da aka kuɓutar da su, wato Chisom Okoye, ‘yar shekara 20, daga Mgbaneze Isu a ƙaramar hukumar Onicha, jihar Ebonyi, da Chinecherem Clement, mai shekara 18, ita ma daga Agbaebo Isu a jihar Ebonyi.

Sauran su ne, Blessing Ogbonna da Blessing Njoku, dukkansu ‘yan shekara 21 daga yankin ƙaramar hukumar Onicha, jihar Ebonyi.

Rundunar ta ce za ta zurfafa bincike tare da tabbatar da ta zaƙulo Gladys Nworie Ikegwuonu, wadda ake zargin ita ce mai wannan masana’anta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *