Asabar mai zuwa za a yi muƙabala tsakanin Abduljabbar da malaman Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta tsayar da Asabar mai zuwa a matsayin ranar da za a yi muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da wasu malaman jihar.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar, Muhammad Tahar Adamu wanda aka fi sani da Baba Impossible, yayin wata tattaunawa da BBC Hausa ya yi da shi a yau Alhamis.

Kwamishinan ya ce za a gudanar da muƙabalar ce ranar Asabar, 10 ga Yulin da ake ciki a Hukumar Shari’a ta jihar Kano.

Ya ce ya miƙa gayyatar yin muƙabalar ga malamin da malaman da za su fafata da shi.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da malaman jihar suka zargi gwamnatin jihar da jan ƙafa dangane da batun muƙabalar.

Malaman Kano sun buƙaci yin muƙabala da Abduljabbar ne bayan da suka zarge shi da cin zarafin Manzon Allah (SAW) da sahabbansa wanda Abduljabbar ɗin ya yi ta musanta zargin.

A Larabar da ta gabata wata Babbar kotun Kano ta amince da buƙatar lauyoyin Sheikh Abduljabbar kan sauraren hujojinsu na neman soke umarnin wata kotun Majistire da ke jihar na rufe masallaci da makarantar malamin.

Alƙalin kotun, Jastis Nura Sagir ne ya bayar da umarnin, bayan la’akari da ƙorafin da malamin ya yi na rashin ba shi damar kare kansa daga wasu zarge-zargen da ake yi masa.

Da ma dai Sheikh AbdulJabbar ya bayyana dakatarwar da gwamanatin ta yi masa daga yin wa’azi da rufe masallacinsa da cewa hakan zalunci ne.