Atiku ya kai ziyarar sallah ga tsofaffin shugabannin Najeriya a Minna

Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya kai ziyara ga tsofaffin shugabannin ƙasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar da Janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidajen su da ke minna babban birnin jihar Neja.

Atiku, shine ya wallafa wannan labarin da kuma hotunan ganawarsu ta shafin sa na sada zumunta.

Atiku Abubakar tsohon mataimakin Shugaban ƙasar Najeriya ne daga shekarar 1999 zuwa 2007.