Editor

9513 Posts
Sanata Barau zai jagoranci kafa cibiyar zamani ta horar da jami’an shige-da-fice a Bichi

Sanata Barau zai jagoranci kafa cibiyar zamani ta horar da jami’an shige-da-fice a Bichi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Tarayyar Nijeriya, Sanata Barau I. Jibrin zai kafa cibiyar horas da jami'an shige da fice ta kasa (NIS) a karamar hukumar Bichi da ke shiyyar jihar Kano ta Arewa.  Sanata Barau ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayin da Kwanturola-Janar na hukumar NIS, Wuraola Adepoju, ta kai ziyarar ban girma zuwa ofishinsa a majalisar dokokin tarayya dake Abuja. A cikin wata sanarwar manema labarai da mai ba shi shawara akan harkokin yada labarai Ismail Mudashir ya fitar, Sanata Barau ya bayyana yunkurinsa kan samar da cibiyar horaswa ta zamani.  “An…
Read More
Makamashi: Maraba da shekara ta 2024

Makamashi: Maraba da shekara ta 2024

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI Mun yi bankwana da shekara ta 2023, shekarar da duk dan Nijeriya ba zai mantata ba Saboda tsanani da kuncin rayuwa na rashin kudade a hannun jama’a ga kuma tsada da hauhawar farashi na fatara da kuma zama cikin zulumi saboda masu kai hare-hare domin kama mutane domin yin garkuwa da su, sai amfanshesu da madukun Kudade, amma Idan bah aka ba kai da dan uwanka sai a Darul-Salam, wato Lahira. To, Alhamdulillah, Allah ya nuna mana wannan Shekara ta 2024, Saboda haka muke yi mata maraba lale da fatan Allah ya kawo mana dauki…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya naɗa jarumi Ali Nuhu da wasu 10 shugabancin hukumomin fasaha da al’adu

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya naɗa jarumi Ali Nuhu da wasu 10 shugabancin hukumomin fasaha da al’adu

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada jamrumi a masana’antar  Kannywood, Ali Nuhu, a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Harkoki Fina-finai ta Nijeriya. Kazalika, nadin ya shafi wasu mutum 10 wadanda za su jagoranci sassa daban karkashin Ma’aikatar Fasaha, Raya Al’adu da Karfafa Tattalin Arziki. Bayanin nadin na kunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta hannun Kakakin Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale, a ranar Juma’a. A cewar sanarwar, Tinubu ya bukaci wadanda nadin ya shafa su aiki da kwarewa don cigaban kasa. Wadanda nadin ya shafa sun hada da: (1) Tola Akerele — Director-General, National Theatre (2) Dr. Shaibu Husseini —…
Read More
Ba ƙaramar kasada Tinubu ya yi ba wajen naɗa ni minista – Wike

Ba ƙaramar kasada Tinubu ya yi ba wajen naɗa ni minista – Wike

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana irin salon siyasa da kalubalen da ya fuskanta a nadin da shugaba Bola Tinubu ya yi masa. Wike ya yarda cewa Tinubu ya yi kasada sosai wajen nada shi ministan Abuja, inda ya nuna cewa akwai adawa sosai a matakin. Wike ya jaddada muhimmancin ajiye adawa a gefe don cigaban kasa. Ya kuma bukaci jama’a da su amince da matakin da shugaba Buhari ya dauka, yana mai cewa duk da cewa ba shi ne zabi mafi kyau ba, amma babu wani zabi. Wike ya kuma nuna godiya…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen ba da tallafi ƙarƙashin NSIPA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen ba da tallafi ƙarƙashin NSIPA

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen ba da tallafin da ke karkashin kulawar Hukumar Shirin ba da Tallafi ta Kasa (NSIPA). A cewar Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Taryya, Segun Imohiosen, an dauki wannan mataki ne domin ba da damar gudanar da bincike yadda ya kamata kan zargin almundahana a hukumar. Sanarwar ta ce, Fadar Shugababn Kasa ta bayyana cewa, an dakatar da baki daya shirye-shiryen bayar da tallafi guda hudun da ke karkashin NSIPA, na tsawon makonni shida. Shiryen-shiryen da lamarin ya shafa sun hada da Shirin N-Power, Shirin Conditional Cash Transfer, Shirin…
Read More
Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamnonin Filato, Ebonyi

Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamnonin Filato, Ebonyi

A ranar Juma’a Kotun Koli ta yi watsi da hukuncin Kotun Daukaka Kara na soke nasarar da Gwamna Caleb Mutfwang na Jam’iyyar PDP ya samu a zaben 2023. Kotun Kolin ta ce kotun farko ta yanke hukunci a kan abin da ba shi da hurumin kotu ta saurare shi. Don haka Kotun a karkashin jagorancin Mai Shari’a Emmanuel Agim, ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraren Kararrakin Zabe wanda ta ayyana Mutfwang a matsayin zababben Gwamnan Filato. Alkalin ya ce Muftwang ya cancanci tsayawa takara saboda sahihin zaben fidda gwani aka yi kafin ya samu tsayawa takarar gwamna. Kotun ta ce…
Read More
Abba Yusuf ya kai bantensa a Kotun Ƙoli

Abba Yusuf ya kai bantensa a Kotun Ƙoli

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kotun Koli ta battabar da nasarar da Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya samu a zaben 2023 a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kano. A ranar Juma’a Kotun Kolin ta kawo karshen gardamar da ake yi tsakanin Abba Kabir da Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC dangane da shugabancin Jihar Kano. Yayin yanke hukuncin, alkalan kotun sun tabbatar da cewa, Kotun Daukaka Karar ta yi rashin fahimta na soke kuri’u 165,616 na Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta yi. Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Okoro, ya kuma bayyana cewa batun kasancewar Gwamna Yusuf ba dan jam’iyyar…
Read More
Rundunar sojoji ta kama jami’an da suka azabtar da fararen hula

Rundunar sojoji ta kama jami’an da suka azabtar da fararen hula

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar Sojojin Nijeriya ta kama wasu jami’anta biyu bayan da wani bidiyo ya nuna suna azabtar da farar hula a Jihar Ribas. Bidiyon wanda ya karade shafukan sada zumunta, ya nuna wani sanye da kakin soji da kuma wani cikin kayan farar hula suna azabtar da wani mutum, duk da hakuri da ya yi ta ba su. Mutumin ya yi ta kuka yana fadin cewa, “A’a, don Allah ku yi hakuri, zan fadi gaskiya.” Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ranar Laraba, ta nuna bacin ranta kan abin da jami’an biyu suka aikata inda ta…
Read More
RTEAN ta ƙaddamar da kayan bada kariya

RTEAN ta ƙaddamar da kayan bada kariya

•Yayin da kamfanin Masar ke shirin saka hannun jari na dala miliyan 10 Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar Masu Motocin Sufuri ta Nijeriya (RTEAN) a ranar Alhamis, ta kaddamar da wasu kayayyakin kariya ga direbobi, yayin da wani kamfanin kasar Masar ke shirin zuba jarin sama da dala miliyan 10 don kafa kamfanin kera kayan kariya a Nijeriya. Da yake jawabi a lokacin kaddamar da kayyakin kariya na motoci, Shugaban RTEAN, Alhaji Musa Mohammed Maitakobi ya ce kungiyar na hada kai da West Africa Automobile Services Limited, wani kamfani mai rijista a kasar Masar domin samar da kayayyakin…
Read More
’Yan bindiga sun sake kashe dagaci da mutum 10 a Katsina 

’Yan bindiga sun sake kashe dagaci da mutum 10 a Katsina 

Daga UMAR GARBA a Katsina ’Yan bindinga sun kashe mutane 10 ciki har da Maigari a kauyen Kukar Babangida da ke Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina. Shugaban Karamar Hukumar Bishir Sabi'u, ya tabbatar wa DW Hausa kashe mutanen, inda ya ce 'yan bindingar sun shiga kauyan ne da misalin karfe daya da rabi na daren ranar wannan Alhamis din. 'Yan bindigar na ci gaba da kashe mutanen da ba su ji ba su gani a wasu daga cikin kauyukan kananan hukumomin jihar duk da kokarin da jami'an tsaro da ma gwamnatin jihar ke cewa suna yi don dakile matsalar.…
Read More