Editor

9513 Posts
Falasɗinawa sun yi zanga-zanga kan ziyarar Blinken a Ramallah

Falasɗinawa sun yi zanga-zanga kan ziyarar Blinken a Ramallah

A ranar Laraba da ta gabata, dubban Falasdinawa sun gudanar da wani gangami a Ramallah don nuna adawarsu da ziyarar sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a yankin yayin ziyarar da ya ke kaiwa gabas ta tsakiya dangane da yanqin Isra’ila da zuwa yanzu ya kashe Falasdinawa fiye da dubu ashirin da uku. Galibin Falasdinawan sun rike allunan da ke dauke da rubutun ‘‘ba ma maraba da zuwanka Blinken’’ sun yi dafifi akan tituna gabanin jami’an tsaro su tarwatsa su. Wannan ne ziyara ta biyu da Blinken ke kaiwa gabas ta tsakiya tun bayan faro yaqin na Isra’ila a Gaza…
Read More
Kotun Ƙoli ta yi fatali da ƙarar PDP kan nasarar Gwamnan Benuwe 

Kotun Ƙoli ta yi fatali da ƙarar PDP kan nasarar Gwamnan Benuwe 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun Koli ta yi fatali da karar da aka daukaka kan zaben gwamna Hycinth Alia na jihar Benuwai. Matakin na zuwa ne bayan janye karar da lauyan Mr Titus Uba na Jam'iyyar PDP, Sebastian Hon ya yi. Titus Uba ya kalubalanci nasarar gwamna Hyacinth ne na jam'iyyar APC. Sai dai kotun kararrakin zabe da ta daukaka kara a Abuja sun tabbatar Alia ne halastaccen gwamnan jihar ta Benue bayan da hukumar zabe INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben ranar 18 ga watan Maris. Kotun daukaka karar ta ce…
Read More
Gwamnonin G5 na PDP za su mara wa Tinubu baya a 2027 – Ortom

Gwamnonin G5 na PDP za su mara wa Tinubu baya a 2027 – Ortom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom ya ce, gwamnonin G5 na Jam’iyyar PDP za su sake marawa takarar Shugaban Kasa Bola Tinubu baya a 2027 idan ya ce zai sake tsaya wa takara. Mista Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata liyafar cin abinci ta murnar shiga sabuwar shekara da ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya shirya a Jihar Ribas. Gwamnonin G5 sun hada da Mista Ortom, Mista Wike, tsohon gwamnan Jihar Inugu, Ifeanyi Ugwuanyi, tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, da gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde. Mista Ortom…
Read More
Tsohon ɗan ƙwallon Jamus Franz Beckenbauer ya mutu

Tsohon ɗan ƙwallon Jamus Franz Beckenbauer ya mutu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwarzon dan kwallon tawagar Jamus, Franz Beckenbauer ya rasu, yana da shekara 78 a duniya. Ya dauki kofin duniya a matakin kyaftin din Jamus a 1974, da kuma a matsayin koci a 1990. Tsohon mai tsaron baya ya buga wa Bayern Munich wasa 582, kuma ya lashe babban kofin gasar Jamus a matakin dan wasa da kuma a matsayin koci. Dan kwallon wanda ake yi wa lakabin Der Kaiser, ya lashe European Championship a matakin dan wasa a 1972, kuma ya lashe Ballon d'Or karo biyu. Beckenbauer, wanda ya fara taka leda a matakin dan wasan…
Read More
Mun yi na’am da hukunce-hukuncen Kotun Ƙoli – APC

Mun yi na’am da hukunce-hukuncen Kotun Ƙoli – APC

Daga BASHIR ISAH Jam’iyyar APC ta ce ta yi na’am da hukunce-hunkuncen da Kotun Koli ta yanke kan kararrakin da aka daukaka na kalubalantar sakamakon zaben gwamnoni na 2023 a jihohi guda takwas. APC ta bayyana gamsuwarta ne cikin sanarwar da ta faitar ranar Juma’a mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na Kasa, Felix Morka. Jam’iyyar ta ce ta yi matukar farin ciki kan yadda kotun ta tabbatar da nasarar da ‘ya’yanta kuma gwamnonin Legas, Ebonyi Kuros Riba suka samu a zaben 2023 da ya gabata. Morka ya ce duk da dai APC ta fadi a shari’ar  Kano,…
Read More
AFCON: Nijeriya ta kira Terem Moffi don maye gurbin Victor Boniface

AFCON: Nijeriya ta kira Terem Moffi don maye gurbin Victor Boniface

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An gayyaci dan wasan Nice Terem Moffi a gasar kofin Afrika da za a fara a karshen mako mai zuwa a maimakon Victor Boniface da ya ji rauni, inji Super Eagles a ranar Talata. Wannan koma-baya ne ga Super Eagles, wadda ta ke fatan daukar kofin babbar gasar qwallon kafa ta Afirka karo na hudu. Mai shekara 23, shi ne na baya-bayan nan da ya ji rauni a tawagar Nijeriya da ta ke cikin wadanda za su fafata a gasar da za a fara ranar 13 ga watan Janairu a Abidjan. An kira dan kwallon Nice,…
Read More
Zan tabbatar da bai wa duniya labarin Nijeriya da Afirka – Shugaban Muryar Nijeriya

Zan tabbatar da bai wa duniya labarin Nijeriya da Afirka – Shugaban Muryar Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Hukumar Muryar Nijeriya, Mallam Jibrin Baba Ndace, ya ce hukumar za ta hada kai da masu ruwa da tsaki wajen bai wa duniya labaran Nijeriya da Afirka. Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da ya jagoranci ma’aikatan hukumar a ziyarar ban girma da ya kai hedikwatar Media Trust da ke Abuja. Yayin da ya bayyana Nijeriya a matsayin kasar da ba ta cika dari bisa dari, ya ce akwai labarai masu kyau da yawa da za a fada game da Nijeriya. “A Muryar Nijeriya abin da nake yi tun lokacin da…
Read More
Gwamnan Kebbi ya rantsar da Alƙalin-alƙalai da shugabannin wasu hukumomi 

Gwamnan Kebbi ya rantsar da Alƙalin-alƙalai da shugabannin wasu hukumomi 

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi  Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya rantsar da Mai shari'a Umar Abubakar a matsayin babban alqali da Khadi Sadiq Usman Mukhtar a matsayin Grand Khadi na jihar. Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ne ya kaddamar da bikin rantsarwar a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Birnin Kebbi a ranar Litinin. Da yake gabatar da mutanen biyu ga gwamnan domin rantsar da shi, sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Bala Tafida ya kuma karanta sunayen shugabanni da mambobin hukumar da Parastatals da za a kaddamar. Bayan rantsuwar, Gwamna Nasir…
Read More
CBN ya rushe shugabancin bankunan Union, Keystone, Polaris da kuma Titan Trust

CBN ya rushe shugabancin bankunan Union, Keystone, Polaris da kuma Titan Trust

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya fara kaddamar mataki a kan rahoton da mai bincike na musamman na Babban Banki Nijeriya (CBN) da sauran abubuwan da suka dangance shi, Jim Obazee ta hanyar rushe shugabancin gudanarwa na Bankin Titan Trust da wasu guda uku. Majiyarmu ta bayyana ragowar bankunan da aka kaddamar wa wannan hukuncin kansu sun hada da Bankunan Union, Polaris, da kuma Keystone. The kwamitin daraktoci da shugabannin zartarwa na bankunan an gayyace su wani taron ganawa a ranar Larabar da ta gabata 10 ga watan Janairu 2024 inda mataimakin CBN a bangaren tsarin kudi…
Read More
MOPPAN ta taya Ali Nuhu murna kan sabon naɗin da Tinubu ya yi masa

MOPPAN ta taya Ali Nuhu murna kan sabon naɗin da Tinubu ya yi masa

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar shirya finafinai ta MOPPAN ta nuna farin cikinta tare da taya murna ga jarumi Ali Nuhu dangane da naɗin da Shugaba Bola Tinubu ya yi masa a matsayin Shugaban Hukumar Finanai ta Kasa. Sakon taya murnar na kunshe ne cikin wasiƙar da kungiyar ta aike wa jarumin mai dauke da kwanan wata 12 ga Janairun 2023 da kuma sa hannun Shugaban Kungiya na Kasa, Ahmad Sarari. Wasikar ta ce, "Muna taya ka murna dangane da nadin da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi maka a matsayin Manajin-Darakta na Hukumar Finanai ta Nijeriya. "Muna matukar alfahari…
Read More