Editor

9513 Posts
Ali Nuhu ya yi wa Tinubu godiya kan naɗin da ya yi masa

Ali Nuhu ya yi wa Tinubu godiya kan naɗin da ya yi masa

Daga BASHIR ISAH Jarumi a masana'antar shirya finafinai ta Kannywood, Ali Nuhu, ya mika godiyarsa ga Shugaban Kasa Bola Tinubu kan nadin da ya yi masa a gwamnatinsa. A wannan makon mai karewa ne Tinubu ya nada jarumin a matsayin Shugaban Hukumar Fina-finai ta Kasa tare da wasu a karkashi Ma'aikatar Al'adu ta Tarayya A ranar Juma'a Ali Nuhu ya wallafa sakon godiyar a shafinsa na facebook inda ya ce, "Godiya ta tabbata ga Allah Subhanahu wa ta’ala, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah Salallahu alaihi wa sallam. *Ina mika sakon godiyata ga Shugaban Kasa Bola Tinubu da…
Read More
Shekara 70 da kafa GTC: Ƙungiyar KANTOBA ta yi rawar gani – Salisu Dala

Shekara 70 da kafa GTC: Ƙungiyar KANTOBA ta yi rawar gani – Salisu Dala

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano An bayyana cewa ƙungiyar tsoffin ɗalibai ta makarantar fasaha ta Kano wato Kano Government Technical College GTC ta yi rawar gani musamman ganin yadda aka ɗauki kwanaki uku ana hidimar bikin cika shekara 70 da kafuwar makaranta GTC wacce aka kafa a shekarar 1952 yadda a ranar farko ɗalibai suka taru aka yi addu’a da sauke Ƙur’ani domin ci gaban makaranta da yin addu’ar ga wanda ya kafa makarantar mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero dama sauran wadanda suka taimakawa makarantar daga Shugabannin ta da malaman ta har zuwa yau dinnan. sai kuma ranar…
Read More
Tinubu ya rage yawan masu rakiya a tafiye-tafiyensa

Tinubu ya rage yawan masu rakiya a tafiye-tafiyensa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da sanarwar rage yawan jami'an da za su rika yi masa rakiya a duk tafiye-tafiyen aiki da zai je ciki da wajen kasar. Matakin ya shafi dukkan ministoci da manyan jami'an gwamnatinsa ciki har da mataimakin shugaban kasa da uwargidan shugaban kasa. Sanarwar wadda Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaban Nijeriya kan harkar yada labarai ya fitar ranar Talata na cewa matakin, wani yunkuri ne na rage yawan kudaden da jami'an gwamnati ke kashewa kan harkokin tafiye-tafiye. Ta ce yawan jami'an da za su rika yi wa…
Read More
Gwamna  Abba ya kammala shirye-shiryen kafa Majalisar Dattawan Kano

Gwamna  Abba ya kammala shirye-shiryen kafa Majalisar Dattawan Kano

*Ganduje, Kwankwaso, Shekarau za su kasance mambobin farko Daga BASHIR ISAH Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta kammala shirin kafa Majalisar Dattawan Kano a jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne sa’ilin da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar a Abuja, inda ya ce Majalisar za ta kasance a mazaunin mai bai wa gwamnatin jihar shawarwari wadda za ta kunshi tsofoffin gwamnoni da mataimakansu. Abba ya ce bayan kafa majalisar, dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Dokt Abdullah Umar Ganduje da…
Read More
Hukuncin Kotun Ƙoli, siyasa da tsaro a Kano

Hukuncin Kotun Ƙoli, siyasa da tsaro a Kano

*Yadda gwamnonin wasu jihohi ma ke fuskantar makomarsu Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A safiyar Juma’a, 12 ga Janairu, 2024, Kotun Kolin Tarayyar Nijeriya ta yanke hukunci mafi sarkakiya, tsumayi da zulumi a babban zaben kasar na 2023, wato shari’ar zaben Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin kasar. Bugu da kari, a Juma'ar ce kuma Kotun Kolin ta yanke hukunci kan zaben kujerun gwamnan jihohin da suka hada da Legas, Zamfara, Filato, Ebonyi, Bauchi da Kuros Ribas, kamar yadda alkalan kotun suka sanar. A karshen watan Disamba ne dai Kotun Kolin ta jingine hukunci akan karar da Gwamnan Jihar…
Read More
NSIPA: Tinubu ya naɗa Malagi da wasu Kwamitin Bincike

NSIPA: Tinubu ya naɗa Malagi da wasu Kwamitin Bincike

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris Malagi mamba a kwamitin bincike da zai binciki shirye-shiryen yaki da talauci karkashin hukumar NSIPA.  Kafa kwamitin binciken da Tinubu ya yi ya biyo bayan dakatar da shirye-shiryen yaki da talauci guda hudun da ke karkashin NSIPA da ya yi ne na tsawon wata shida bisa zargin aikata ba daidai ba a hukumar. Kwamitin zai gudana ne karkashin jagorancin Minista mai kula da Tattatilin Arziki kuma Ministan Kudi, Mr. Wale Edun, in ji sanarwar da Kakakin Shugaban Kasa, Cif Ajuri Ngelale…
Read More
Badaƙalar Ma’aikatar Jinƙai: Babu ’yan mowa a wajen Tinubu – Shugaban ICPC

Badaƙalar Ma’aikatar Jinƙai: Babu ’yan mowa a wajen Tinubu – Shugaban ICPC

*Yadda Hukumar EFCC ta ƙwace fasfon Sadiya, Edu da Halima Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sabon Shugaban Hukumar Yaki da Ayyukan Almundahana Mai Zaman Kanta (ICPC), Malam Musa Aliyu, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai ware wani ko wasu ya ce ‘yan mowansa ba ne ko shafaffu da mai. Ya ce, duk wanda aka kama da laifin cin rashawa a gwamnati, duk girmansa kuma duk matsayinsa, to za a kama shi kuma a hukunta shi. Aliyu, wanda babban lauya ne, wato SAN, ya yi wannan bayani a ranar Laraba, a yayin da ya ke ganawa da manema labarai…
Read More
’Yan ta’adda sun gama yawo, inji Hedikwatar Tsaro

’Yan ta’adda sun gama yawo, inji Hedikwatar Tsaro

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hedikwatar Tsaron Nijeriya a ranar Alhamis ta sha alwashin bin diddigin 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuka a fadin kasar har sai an fatattake su ko kuma su mika wuya. Rundunar ta tabbatar da cewa a makon farko na shekarar 2024 dakaru sun kai hare-hare ta sama da dama kan yankunan 'yan ta'adda tare da yin amfani da karfin soji a dukkan yankunan da 'yan ta'adda suka addaba a kasar. Daraktan Yada Labarai Na Tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a Abuja, inda ya ce rundunar ta kara zage damtse wajen farautar…
Read More
Morocco ta karɓi jagorancin Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta MDD

Morocco ta karɓi jagorancin Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta MDD

Morocco ta yi nasarar lashe kujerar shugabancin Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta MDD bayan da ta doke abokiyar hamayyarta a wannan mukami wato Afirka ta Kudu. Bayan da aka bayyana nahiyar Afirka a matsayin wadda za ta shugabancin hukumar a wannan shekara ta 2024, duk da haka kasashen biyu wato Afirka ta Kudu da Morocco sun gaza cimma jituwa a tsakaninsu sai da aka je ga kada kuri’a. A quri’ar da aka kada a asirce ranar Laraba a birnin Geneva, dan takarar Kasar Morocco Omar Zniber ya samu kuri’u 30 yayin da abokin karawarsa Mxolisi Nkosi na Afirka ta…
Read More