16
Jan
Daga BASHIR ISAH Wasu bata-garin matasa a Jihar Ekiti sun kai hari Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jihar (EKSUTH) da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar inda suka sace wata gawa. MANHAJA ta kalato cewar wannan al’amari ya auku ne a ranar Litinin lamarin da ya haifar da tsaiko a ayyukan asibitin. Bayanai sun ce, gawar da aka sace din ta mahaifin daya daga cikin bata-garin ne. Sai dai, babbu cikakken bayani kan dalilin da ya sa matasan daukar wannan mataki. Faruwar wannan al’amari ya sanya kungiyar likitoci a jihar ta bai wa mambobinta umarnin fara yajin aikin sai-baba-ta-gani domin nuna rashin…
