Editor

9513 Posts
Jama’a sun shiga firgici sakamakon fashewa mai karfi da ta auku a Ibadan

Jama’a sun shiga firgici sakamakon fashewa mai karfi da ta auku a Ibadan

Daga BASHIR ISAH Al'umma mazauna Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun shiga firgici da tashin hankali biyo bayan fashewa mai karfi da ta auku da yammacin Talata a birnin. Mazauna yankunan Awolowo, Bodija, Akobo da sauransu sun ce, hatta gidaje da wasu motocin da ke kusa sai da suka amsa sakamakon karfin fashewar. A wani sako da ta wallaffa a shafinta na X, Gwamnatin Jihar Oyo ta ce ta samu rahoton fashewar da ta auku. “Ana kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu kasancewar hukumomin tsaro sun sunkuya bincike domin gano musababbin fashewar," in ji Gwamnatin Jihar. Jaridar…
Read More
Cin zarafi a aure: Ina mafita (2)?

Cin zarafi a aure: Ina mafita (2)?

Tare da AMINA YUSUF ALI Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Blueprint manhaja. Yau ma ga mu a wani makon mai albarka. A wannan makon muna tafe ne da bayani a kan yadda matan auren da suke fuskantar cin zarafi a gidan aure musamman a kasar Hausa. Inda za ka ga cewa, mace ana cin zarafinta, ana hana ta abinci, da sauran hakkokinta na aure ga uwa uba kuma duka da wulakanci. Amma ta kafe ta haqura ta zauna a gidan. Me yake kawo hakan? Kuma meye mafita? Yawanci sukan dauki matakin hadiye komai su cigaba da…
Read More
An gano gawarwaki biyar a hatsarin jirgin ruwan da ya auku a Neja

An gano gawarwaki biyar a hatsarin jirgin ruwan da ya auku a Neja

Daga BASHIR ISAH Akalla gawarwaki biyar ne aka gano yayin da wasu dama sun bace sakamakon hatsarin jirgin ruwan da ya auku ranar Litinin a yankin Karamar Hukumar Borgu a Jihar Neja. Jami’in kula da iftila’i a yankin Borgu, Malam Musa Said, shi ne ya bayyana haka, inda ya ce a ci gaba da binciken da masu aikin ceto ke yi sun gano gawarwaki guda biyar, kuma ana ci gaba da neman ragowar mutanen da ba a gan su ba bayan aukuwar hatsarin. Haka shi ma Shugaban Hukumar ba da Agajin Gaggawa na Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar…
Read More
Edu ba ta cinye Baitulmali du ba

Edu ba ta cinye Baitulmali du ba

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Batun almundahana a Nijeriya ai ba sabon abu ba ne don kama daga lokacin mulkin soja har dawowa farar hula da a ke ciki yanzu daga 1999, kalubalen ya zama ruwan dare a Nijeriya. A baya an dau abun ba wani babba ba ne da ya wuce wasu baragurbi a jami'an 'yan sanda da kan karbi kudi 'yan kalilan daga direbobi a kan tituna don kyale su su wuce ba tare da wani bincike ba. Hakanan in mutum na son a bar shi ya ketare wani shinge da ba shi da hurumi sai ya riqe…
Read More
Kotun Ƙoli: Zamfarawa sun yi fitar farin dango don taya Gwamna Lawal murna

Kotun Ƙoli: Zamfarawa sun yi fitar farin dango don taya Gwamna Lawal murna

Daga BASHIR ISAH A ranar Litinin da ta gabata dubban Zamfarawa cike murna suka yi dandazo a Gusau, babban birnin jihar domin tarbar Gwamna Dauda Lawal in Gusau, bayan dawowa daga Kotun Ƙoli. A ranar Juma'ar da ta gabata Kotun Ƙoli mai zamanta a Abuja ta tabbatar  da Gwamna Lawal a matsayin wanda ya lashe zabe Gwamnan Zamfara, tare da yin watsi da karar da bangare hamayya ya daukaka na kalubalantar nasarar tasa. Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar, Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce masoyan gwamnan sun yi fitar farin dango don nuna farin cikinsu dangane da…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Kebbi

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Kebbi

Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan karar da aka dauka ta neman a sauke Dr Nasir Idris na jam'iyyar APC a matsayin Gwamnan Jihar Kebbi. Kotun ta dauki wannan matsaya yayin zaman ci gaba da sauraren shari'ar da ta yi ranar Talata karkashin jagorancin Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun, bayan ta karrbi bayanan lauyoyin duka bangarorin. Kotun ta ce za ta sanar da bangarorin da lamarin ya shafa baya ta tsayar da lokacin da za ta yanke hukunci kan shari'ar. Jam'iyyar PDP a Jihar Kebbi da dan takarar gwamnanta a zaben 2023, Manjo Janar Aminu Bande, su ne suka daukaka…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Nasarawa

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Nasarawa

Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa da ke gabanta. Kotu ta yi hakan ne a zaman ci gaba da sharilar da ta yi a wannan talatar. Ta ce za ta sanar da bangarorin da shari'ar ta shafa ranar da za raba gardama idan ta tsayar da rana nan gaba. Ana fafata shari'ar ne tsakanin Gwannan jihar, Injiniya Abdullahi Sule da kuma Jam'iyyar PDP a jihar tare da dan takararta na gwamna, David Ombugadu
Read More
‘A Tribe Called Judah’: Fim ɗin Nollywood da ya yi fito-na-fito da Hollywood 

‘A Tribe Called Judah’: Fim ɗin Nollywood da ya yi fito-na-fito da Hollywood 

Daga AISHA ASAS Idan a na maganar masana’antar finafinai da ta yi wa kowacce masana’anta irinta zarra ta fuskar shahara, kwarewa, da kuma samun cigaba, to tabbas masana’antar finafinai ta Turai, wato Hollywood ce za a ambata. Dalilin kenan da suka fi kowacce masan’antar fim samar da kudaden shiga, wanda ya sa jarumai da ma’aikatansu suka zama mafi arziki daga cikim masu aikin fim na duniya bakidaya. A vangaren amfanar da kasa kuwa, Hollywood na daya daga cikin wuraren da kasar ke amfana da su, sakamakon yawan mutanen da ke da ra’ayin kallon su, dalilin bajinta da kwarewa da suke…
Read More
Asalin yadda aka samo sunan Hausa Bakwai da Banza Bakwai

Asalin yadda aka samo sunan Hausa Bakwai da Banza Bakwai

Wasu sun san garuruwan da ake kira 'Hausa Bakwai' da 'Banza Bakwai' amma ba su san dalilin da ya sa ake kiransu da waxannan sunayen ba. Wannan ne ya sa naga dacewar yin wannan dan takaitaccen bayanin kamar yadda na tava karantawa a littafin 'Kano Ta Dabo Cigari' na Marigayi Wazirin Kano Alhaji Abubakar. Bayan Bayajidda ya gudo daga kasar Borno shi da matarsa mai suna Magaram saboda yunkurin kashe shi da Sarkin (Shehu) Borno ya yi, sai suka zo wani gari da ake kira Garun Gabas a kasar Hadeja. A nan ya bar matarsa saboda tsohon cikin da take…
Read More
Messi ya lashe kambun “Gwarzon Ɗan Wasan” shekara na FIFA

Messi ya lashe kambun “Gwarzon Ɗan Wasan” shekara na FIFA

A karo na uku, shararren dan wasan kwallon kafar nan, Lionel Messi, ya lashe kambun Hukumar Kwallon Kafa ta duniya (FIFA) na "Gwarzon Dan Wasa" a 2023. A ranar Litinin FIFA ta mika dan wasan wanda dan asalin Argentina ne kambun a birnin bayan da ya doke dan wasan Manchester City, Erling Haaland. Haaland ya samu damar lashe kambun bayan da ya zira kwallo sau 52 a raga a matsayin dan wasan Manchester City. Amma Messi ya lashe zaben ne bayan ya lashe gasar Ligue 1 a Paris Saint-Germain da kuma gasar Leagues Cup 'yan wstanni bayan da ya koma…
Read More