Editor

9513 Posts
Alƙalan gasa na duba abubuwa da dama wajen ingancin labari – Sulaiman Ibrahim 

Alƙalan gasa na duba abubuwa da dama wajen ingancin labari – Sulaiman Ibrahim 

“Ka na ƙara karatu hikimarka na ƙara faɗi kan rubutu” Daga IBRAHIM HAMISU, Kano  Idan a na maganar gogewa da kwarewa a harkar rubutun littafi da kuma aikin jarida, dole a ambaci sunan Sulaiman Ibrahim Katsina, wanda littafin da ya rubuta na 'Turmin Danya' ya lashe kyautar littafin da ya fi kowane inganci a Nijeriya a cikin shekaru 41 da ta gabata. A zanyawarsa wakilin Blueprint Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, mai karatu zai san ko wane ne marubucin littafin 'Turmin Danya', tun daga tarihinsa, zuwa gwagwarmayar da aka yi, da kuma nasarorin da ya samu a rubutu da ma…
Read More
Kano ta ware N8bn don gina makarantun firamare na musamman guda uku

Kano ta ware N8bn don gina makarantun firamare na musamman guda uku

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin jihar Kano ta ware Naira biliyan 8 domin gina manyan makarantun firamare guda uku a fadin jihar. A cewar Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf, makarantun za su kasance da cikakkun kayan aikin koyarwa, za kuma a samar da isasshen yanayi ga yaran da suka fito daga iyayen marasa galihu domin samun ingantaccen ilimi duka dai don samun ci gaba a nan gaba. Gwamnan ya ce za a kafa makarantun ne a kowace mazabar majalisar dattawa da kayayyakin koyo na zamani don samar da ingantaccen ilimi a matakin farko. Ya kuma ce an ware Naira…
Read More
Iftila’in Oyo: Dole a binciko masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba don fuskantar hukunci – Tinubu

Iftila’in Oyo: Dole a binciko masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba don fuskantar hukunci – Tinubu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ce dole ne a binciko tare da hukunta masu harkar haƙar ma'adinai ta haramtacciyar hanyar da suka yi sanadiyar aukuwar fashewa mai karfi a Ibadan, Jihar Oyo. MANHAJA ta ruwaito Tinubu ya bayyana haka ne cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba ta hannun kakakinsa, Ajuri Ngelale. Sanarwar ta ce “Abin damuwa ne ainun jin cewa aukuwar fashewar na da nasaba da ayyukan masu hakar ma'adina ba bisa ka'ida ba. "Dole a binciko masu hannun cikin wannan halin gangancin da ya haifar da wannan mummunan al'amari don su fuskanci hukunci." Shugaban Kasar…
Read More
Ni ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin shugabar matan Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa – Hajara Ɗanyaro

Ni ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin shugabar matan Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa – Hajara Ɗanyaro

"Ina yin shigar mutunci don 'yan baya su koya" Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Daya daga cikin mata da suka kafa tarihi a Jihar Nasarawa, jajirtacciyar mace da ta tabbatar wa duniya mata ma za su iya a bangaren siyasa, Hajiya Hajara Danyaro Ibrahim ta samu damar amsar gayyatar da jaridar Manhaja ta yi mata, don tattaunawa da ita a wannan shafi na Mata A Yau. Mace ce mai kamar maza, da ta iya shanye kalubalen da ke tattare da kutsawa cikin maza don neman abinda suke rike da shi, don haka rayuwarta zata iya zama abin koyi ga…
Read More
Babbar mota ta markaɗe wata mata a yankin Abuja

Babbar mota ta markaɗe wata mata a yankin Abuja

Daga BASHIR ISAH Wata tipa makare da yashi ta markade wata mata a cikin motarta a hanyar zuwa filin jirgin sama a yankin Lugbe, Abuja. Binciken MANHAJA ya gano wannan mummunan al’amari ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata biyo bayan akasin burki da motar ta fuskanta. Hatarin ya haifar da tsaiko na wani lokaci a hanyar wanda hakan ya haifar da samun jerin gwanon motoci masu zaman jira a bude hanya. Wani faifan bidiyon hatsarin da aka yada ya nuna yadda yashin da tipar ta dauko ya zuba a kan karamar motar da aka markade wanda jama’a…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Sakkwato

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Sakkwato

Kotun Koli da ke Abuja, ta kebe yanke hukunci kan karar da jam'iyyar PDP da dan takararta, Saidu Umar, suka daukaka na kalubalantar nasarar da Gwamna Ahmad Aliyu ya samu a matsayin zababben gwamnan jihar a zaben 2023. Kwamitin akalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun, ya dauki wannan mataki ne yayin zaman shsari'ar da ya yi a ranar Laraba. Kotun ta dage yanke hukunci kan shari'ar ne zuwa wani lokaci wanda ba ta ayyana ba. Kuma ta yi hakan ne bayan da ta karbi bayanai daga lauyoyin bangarorin da shari'ar ta shafa.
Read More

An samu aukuwar gobara a Kasuwar Panteka a Kaduna

Daga BASHIR ISAH Da safiyar wanna Laraba aks samu aukuwar gobara a fitacciyar kasuwar nan ta Panteka da ke Kaduna. Wani ganau mai suna Malam Isiyaku, ya ce gobara ta fara ne da misalin karfe na dare 12. Ya kara da cewa, ya zuwa lokacin da aka nemi jin ta bakinsa ba a kai ga gano dalilin aukuwar gobarar ba. MANHAJA ta tattaro cewa, gobarar ta kone shaguna masu yawa wanda hakan ya haifar da asarar dimbin dukiya. Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomi a jihar ba su ce uffan ban kan iftila'in gobarar. Ga wani bangare na bidiyon…
Read More
Badaƙala da haƙƙoƙin talakawa, ya isa haka!

Badaƙala da haƙƙoƙin talakawa, ya isa haka!

Tate da ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ƙarshe dai tsohuwar Ministar Ma’aikatar Jinkai da Yaki da Talauci Betta Edu ta yi gaba, sai dai tashin zance. Amma ’yan Nijeriya za su dade ba su manta da ita ba a matsayinta na minista mai gajeren kwana, wacce cikin kankanin lokaci son zuciya da rashin gaskiya suka yi awun gaba da kujerarta. Dama a cikin jawabinsa na sabuwar shekara, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa da ’yan Nijeriya cewa kamar yadda ya dauki rantsuwar kama aiki na yin dukkan abin da ya kamata don inganta cigaban kasar nan. Shi da ministocinsa da…
Read More
Ministan Abuja ya kira taron gaggawa kan matsalar tsaro

Ministan Abuja ya kira taron gaggawa kan matsalar tsaro

Daga BASHIR ISAH Ministan Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kira taron gaggawa a ranar Talata kan matsalar tsaron da ke addabar babban birnin kasa. Ministan ya bayyana haka ne sa'ilin da yake jawabi a wajen wani taro a Abuja, inda ya bai wa mazauna yankin tabbacin ba su kariya yadda ya kamata. Ya kara da cewa gwamnati na yin mai yiwuwa wajen karfafa wa hukumomin tsaro ta hanyar samar musu da dukkan abubuwan da suke bukata don dakile matsalar tsaro a fadin birnin. MANHAJA ta kalato cewa, wadan suka halarci taron gaggawar sun hada da shugabannin hukumomin tsaro na…
Read More