20
Jan
Saga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi ganawar sirri da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje. Ganduje ya jagoranci wata tawaga da ta kunshi shugabannin jam’iyyar APC reshen Jihar Kano domin ganawa da Tinubu a fadar shugaban qasa ta Aso Rock Villa da ke Abuja, ranar Alhamis. Taron na ranar Alhamis ya zo ne mako guda bayan da Kotun Koli ta yanke hukuncin amincewa da Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar da korar karar dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna. A watan Maris din da ya gabata ne dai mulki ya…
