Editor

9513 Posts
An cafke limami da wasu dauke da sassan jikin mutum a Legas

An cafke limami da wasu dauke da sassan jikin mutum a Legas

An cafke wani limami tare da wasu mutun hudu da ake zargin matsafa ne dauke da sassan jikin mutum a jihar Legas. An gano su ne dauke da kwarangwal na kan mutum da kuma wasu sassan jiki. Majiyarmu ta ce mazauna yankin Adamo a Ikorodu ne suka gano wadanda lamarin ya shafa kafin daga bisani aka mika su ga 'yansandan yankin. Majiyar ta kara da cewa, limamin da aka kama din ya bayyana wa 'yansanda cewa wani maigidansa yake yi wa aiki. A cewar mazauna yankin da lamarin ya faru, a ranar Alhamis da ta gabata ne 'yansanda sashen yaki…
Read More
Fargabar tsaro ta dawo a hanyar Abuja

Fargabar tsaro ta dawo a hanyar Abuja

*Mutane sun fara hijira a yankin Bwari*’Yan bindiga sun kashe magidanci, sun sace ’ya’yansa 13*An ceto wanda aka sace daga Abuja zuwa Kano Daga MAHDI M. MUHAMMAD Daga dukkan alamu al’umma sun sake fadawa cikin fargabar rashin tsaro a yankin kewaye da hanyar Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja biyo bayan yadda a kwana-kwanan nan masu garkuwa da mutane ke yi wa mutane dauki dai-dai. Rahotanni sun nuna cewa, wasu magidanta mutane sun fara yin hijira daga yankin Bwari, wanda ke kan iyakar Abuja ta vangaren Jihar Kaduna tun bayan shigowar sabuwar shekarar nan ta 2024, bayan kashe wani magidanci da…
Read More
Abba na buƙatar addu’ar sauke nauyin al’ummar Kano – Dr. Salihun-nur Adam

Abba na buƙatar addu’ar sauke nauyin al’ummar Kano – Dr. Salihun-nur Adam

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano An bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, yana buqatar addu'ar milyoyin al'ummar Kano don ya samu damar sauke nauyin shugabancin da ya rataya a wuyansa. A ranar Juma'ar makon jiya ne dai Kotun Ƙoli ta tabbatar wa Abba Kabir Yusuf da sahihancin nasararsa a zaben gwamnan Kano da aka yi a 2023. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Dakta Salihun-nur Adam wanda aka fi sani da Salihanur Shugaban Cibiyar Bincike akan Ganyayyaki da sauyoyi da tsire-tsire domin maganin cututukan da ke damun dan Adam dake Kano. Haka kuma ya bayyana cewa,…
Read More
 Alhaji Ƙarami da ASUSS sun jagoranci ƙaddamar da littafin tarihin Fadar Bege da Hafiz Abdallah

 Alhaji Ƙarami da ASUSS sun jagoranci ƙaddamar da littafin tarihin Fadar Bege da Hafiz Abdallah

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Alhaji Ƙarami Isyaka Rabiu da ASUSS sun jagoranci kaddamar da littafin tarihin shahararrun sha’iri na Manzon Allah da sahabban sa da Ahalinsa wato Marigayi Abdulaziz Fadar Bege bayan rasuwar fadar bege shekaru 10 da suka wuce. Littafan biyu wanda fitaccen marubuci Malam Bilyaminu Abul-warakat Ayagi, wanda ya rubuta litattafai sama da 100 wanda kuma shi  ne ya rubuta litafin tarihin Marigayi Fadar Bege da kuma na sha’irin mawakin Manzon Allah wato Ambasada Dakta Hafizu Abdullah wanda Alhaji Karami Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu ya kaddamar da sayen litattafan hudu akan Naira miliyan biyu domin qarfafa gwiwa…
Read More
Wike ya ɗora alhakin yajin aikin malaman Abuja kan shugabannin ƙananan hukumomi

Wike ya ɗora alhakin yajin aikin malaman Abuja kan shugabannin ƙananan hukumomi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya zargi shugabannin kananan hukumomin shida da laifin yajin aikin da malaman makarantun firamare ke cigaba da yi a yankin. Wike, wanda ya yi wa ’yan jarida jawabi a ranar Talata a Abuja jim kadan kafin wani taron gaggawa da hukumomin tsaro, ya ce jami’an kananan hukumomin ba su cika aikin da aka dora musu ba. A ranar Lahadin da ta gabata ne Kungiyar Malamai ta babban birnin tarayya Abuja ta umurci malaman firamare da su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar 15 ga watan Janairu. Yajin aikin…
Read More
Ɗan APC da ɗan PDP Ɗanjuma da Ɗanjummai ne – Sule Lamiɗo

Ɗan APC da ɗan PDP Ɗanjuma da Ɗanjummai ne – Sule Lamiɗo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a Jam'iyyar PDP ya ce zargin da tsohon shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC Chief Bisi Akande ya yi cewa idan PDP ta dawo mulki 'yan Nijeriya za su sake shiga qunci ba gaskiya ba ne. Alhaji Sule Lamido ya ce duk dan APCn da yake ganin PDP ce ta lalata Nijeriya to da shi a ciki, kasancewar shi ma asali dan PDP ne. Sule Lamido ya ce ya yi mamakin kalaman Bisi Akande kan cewa PDP musiba ce, annobar bala'i ce azaba ce, amma duk da hakan…
Read More
Daina biyan kuɗin fansa shi zai kawo ƙarshen garkuwa da mutane — Ministan Tsaro

Daina biyan kuɗin fansa shi zai kawo ƙarshen garkuwa da mutane — Ministan Tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan tsaron Nijeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya ce lokaci ya yi da za a daina biyan kudin kansa saboda haka ne kadai hanyar kawo karshen masu garkuwa da mutane. Ministan ya bayyana haka ne a taron majalisar zartaswa ta kasa da aka gudanar a ranar Laraba. Ya ce Shugaban Kasa ya bai wa dukkan hafsoshin tsaro goyon baya da ta kamata don ganin an kawo karshen garkuwa da mutane da ya yi kamari a kasar. Ministan tsaron ya ce dokar Nijeriya ta hana bayar da kudin fansa kuma bai kamata mutane su rika biyan…
Read More
CBN ya mayar da manyan sassansa zuwa jihar Legas

CBN ya mayar da manyan sassansa zuwa jihar Legas

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya shiraya don mayar da manyan sassansa zuwa jihar Legas. Wannan jawabi yana ƙunshe ne a cikin wata takardar yarjejeniyar cikin gida wacce aka ba wa majiyarmu damar samu. Wannan yunkuri a cewar wani jami’in CBN ɗin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa, an yi ne domin a rage cinkoso a babbar shalkwatar bankin da ke Abuja. Kodayake wasu daga cikin ma’aikatan na CBN ɗin sun yi tirjiya a kan komawa legas ɗin saboda suna ganin cewa wannan lamari an yi shi ne saboda qabilanci zalla ba don wani…
Read More
Ba zan yarda da cin hanci da rashawa a gwamnatina ba – gargaɗin Gwamnan Zamfara ga ma’aikatansa

Ba zan yarda da cin hanci da rashawa a gwamnatina ba – gargaɗin Gwamnan Zamfara ga ma’aikatansa

Daga MAHDI M. MUHHAMMAD Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da duk wani nau'i na cin hanci da rashawa ko rashin tausayi daga mambobin majalisarsa ko ma'aikatan gwamnati a jihar Zamfara ba. A ranar Alhamis ne gwamnan ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa na musamman a zauren majalisar a gidan gwamnati da ke Gusau. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce majalisar ta kasance taron zartarwa na farko na gwamnatin Zamfara a shekarar 2024. Ya qara da cewa, Gwamna Dauda Lawal ya bukaci dukkan masu rike da manyan…
Read More
Tinubu ya gana da Majalisar Koli ta Shari’ah bisa nadama takarar Musulmi da Musulmi

Tinubu ya gana da Majalisar Koli ta Shari’ah bisa nadama takarar Musulmi da Musulmi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da ’Yan Majalisar Koli ta Shari’a a Nijeriya a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Ganawar da aka yi tsakanin shugaban kasar da majalisar na zuwa ne kimanin sa’o’i 48 bayan shugaban majalisar, Sheikh Abdur-Rasheed Hadiyyatullah, ya nuna nadamar goyon bayan takarar mabiya addinin faya da Tinubu da Shettima a bara. A ranar Talata, Sheikh Hadiyyatullah, a wata hira da manema labarai a Abuja, ya haifar da sabon cece-kuce kan tsayawa takarar jam’iyyar APC Musulmi da Musulmi a zaben 2023, wanda a cewarsa, ya gaza yadda ake tsammani. Ya…
Read More