Editor

9513 Posts
Ƙidaya: Majalisa za ta binciki yadda aka kashe Naira Biliyan 200

Ƙidaya: Majalisa za ta binciki yadda aka kashe Naira Biliyan 200

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Wakilai ta ce za ta binciki Naira biliyan 200 da aka kashe kan ƙidayar da aka ɗage a shekarar 2023 da Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa NPC ta yi. Ƙudurin binciken yadda NPC ta kashe ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da ɗan majalisa Dominic Okafor (APGA- Anambra) da ɗan majalisar wakilai Patrick Umoh (APC-Akwa Ibom) suka ɗauki nauyi a zauren majalisar ranar Laraba. Okafor, wanda ya gabatar da ƙudirin, ya ce “ƙidayar jama’a ta samar da sahihin bayanan yawan jama’a yana da amfani ga tsare-tsaren ci gaba, tsara manufofi, rabon albarkatu, da aiwatar…
Read More
Gidauniyar Isah Wali ta jagoranci ƙungiyoyi wajen koya wa masu tallace-tallace sana’o’i

Gidauniyar Isah Wali ta jagoranci ƙungiyoyi wajen koya wa masu tallace-tallace sana’o’i

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Gidauniyar Isah Wali Empowerment Initiative IWEI ta gajoranci gamayyar ƙungiyoyi bakwai na tallafa wa al'umma musamam matasa mata da maza koyawa 'yan talla 50 a bakin titi mata da maza, sana'oi'n dogaro da kai domin rabasu da talla da barace-barace akan titi kamar dai yadda jami'ar ayyuka na musamman a gidauniyar IWEI Madam Bridget Idoko ta bayana a lokacin horas da 'yan talla 50 sana'o'in dogaro da kai da aka gabatar a makon da ya gabata a ɗakin karatu na Murtala Muhammad dake Kano. Daga cikin gamayyar qungiyoyin da suka horas da waɗannan matasa akwai…
Read More
Matawalle ya zargi Gwamna Dauda da yaɗa tsofaffin bayanai

Matawalle ya zargi Gwamna Dauda da yaɗa tsofaffin bayanai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya zargi gwamnatin jihar da yaɗa tsofaffin hotunan gidajen masauki gwamna 14 a faɗin jihar da gwamnatin baya ta bayar da ayyukansu. Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa Gwamna Dauda Lawal ya zargi Matawalle da biyan bashin sama da Naira biliyan 1 ga ɗan kwangilar ayyukan da ba a kammala ba. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Suleiman Idris, ya fitar, ta bayyana cewa, savanin qa’idar aikin gwamnati, tsohon gwamnan ya amince da biyan cikakken kuɗin aikin tun kafin a fara. Amma…
Read More
Yadda ɗan haya ya ɗirka wa ‘yar mai gida ciki

Yadda ɗan haya ya ɗirka wa ‘yar mai gida ciki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani fasto mai shekara 61 ya bayyana a kotun da ke sauraren ƙararrakin cin zarafin mata da yara ƙanana a Ikeja da ke Jihar Legas cewa, Mista Godwin Emmanuel, wanda yake haya a gidansa, ya yi wa ‘yarsa mai shekara 16 fyaɗe kuma har ya firka ma ta ciki. Ɓangaren da ya shigar da ƙarar ya bayyana cewa, Emmanuel ya yi wa yarinyar fyaɗe a watan Afrilu da Yuni 2021 a gidan da yake yin haya a Ajangbadi dake Badagry. Sai dai kuma Emmanuel ya musanta laifin da ake zarginsa da shi. Faston ya…
Read More
Mataimakin Gwamnan Kebbi ya yi kira a ƙara ƙaimin tsaro kan iyakoki

Mataimakin Gwamnan Kebbi ya yi kira a ƙara ƙaimin tsaro kan iyakoki

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Mataimakin Gwaman jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi ya yi kira ga hukumar kula da kan iyakokin Nijeriya da su ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro kan iyakokin. Ya yi wannan kiran a garin Sakkwato ranar Talatar da ta gabata a wajen wani taron ƙara wa juna sani da aka shirya don daƙile ayyukan ta'addanci a kan iyakokin ƙasashen da jihohin da ke maƙotaka da Nijeriya. Sanata Umar Tafida wanda shi ne ya jagoranaci shi rin ya ce ba shakka ƙirƙiro wannan kwamiti zai zaƙulo hanyoyin samar da tsaro da  zai taimaka wajen magance…
Read More
Ƙarancin kuɗi: Ƙarin albashin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya haɗu da tsaiko

Ƙarancin kuɗi: Ƙarin albashin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya haɗu da tsaiko

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ana ƙara nuna damuwa kan yadda batun alƙawarin Gwamnatin Tarayya na ƙara wa ma’aikatanta albashin Naira 35,000 na tsawon watanni shida ke fuskantar ƙalubalen kuɗi. Bincike ya nuna cewa, Gwamnatin Tarayya ba ta da isassun kuɗaɗe da za ta cika alƙawarin da ta ɗauka na ƙara wa dukkan ma’aikatan tarayya albashi, alƙawarin da ta ɗauka a lokacin da aka cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023. A lokacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da Ƙungiyoyin Kwadago ta Nijeriya NLC da TUC a ranar 2 ga watan Oktoba…
Read More
Manyan jam’iyyu sun bayyana matsayarsu kan shawarwarin Atiku

Manyan jam’iyyu sun bayyana matsayarsu kan shawarwarin Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Manyan jam'iyyun Nijeriya sun bayyana mabambantan ra'ayoyinsu game da shawarwarin da tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya ƙarƙashin Jam'iyyar PDP Atiku Abubuakar ya bayar. Atiku Abubakar ya bayar da shawara kan tursasawa hukumar zaben Nijeriya INEC amfani da naurar zaɓe da kuma daura sakamako a Internet kafin sanar da wanda ya samu nasara. Ya ce kamata ya yi a riƙa yanke hukuncin shari'un zaɓe gabanin rantsar da wanda aka ayyana ya ci zave idan akwai ƙalubalantar da yake fuskanta ta shari'a. A ganinsa kamata ya yi a mayar da mulkin shugaban ƙasar zango ɗaya na…
Read More
Marasa ƙaunar talaka ne ke sukar auren zawarawa da kai ɗaliban Kano waje karatu – Dabinai

Marasa ƙaunar talaka ne ke sukar auren zawarawa da kai ɗaliban Kano waje karatu – Dabinai

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Alhaji Zubairu Suleman Dabinai, Shugaban ƙungiyar 'yan kasuwa ta Ɗan Tunku Traders Association, ya bayyana cewa su dai suna goyon bayan auren zawarawa wanda ake kira da auren 'yan gata da kuma kai ɗalibai 'ya'yan talakawa marasa ƙarfi karatu ƙasashen waje duk da suna da cikakkiyar masaniyar cewa wasu masu ƙarfi da madafan iko marasa ƙaunar talaka ba sa goyon bayan wannan al'amari na alkairi a Musulunce da al'adance da zamantakewa ta mutanen kirki masu ƙaunar talaka da 'ya'yansa na a ga an cigaba an yi ilimi mai zurfi kuma an taimakawa marasa ƙarfi ta…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaron farin kaya huɗu a Ribas

‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaron farin kaya huɗu a Ribas

Daga BASHIR ISAH Ana fargabar wasu jami'an tsaro Civil Defence Corps (NSCDC) sun riga mu gidan gaskiya sakamakon kwanton ɓauna da wasu 'yan bindiga suna yi musu a ƙauyen Bakana, Jihar Rivers. Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana wa majiyarmu cewar wannan ɗanyen aikin ya faru ne da safiyar ranar Juma'a. Majiyar ta ce an bindige jami'an ne a Rafin Bakana cikin Ƙaramar Bukumar Degema. “Biyu daga cikin jami'an da lamarin ya shafa Musulmi ne, kuma tuni aka yi musu jana'iza kamar yadda Musulunci ya tanada," in ji majiyar. Jaridar News Point Nigeria ta rawaito…
Read More
A daina yi wa ‘yan Arewa barazana ko mu hana ci gaba da jigilar kayan abinci zuwa Kudancin Nijeriya – Ƙungiya

A daina yi wa ‘yan Arewa barazana ko mu hana ci gaba da jigilar kayan abinci zuwa Kudancin Nijeriya – Ƙungiya

Daga BASHIR ISAH Wata ƙungiyar Arewa mai suna Northern Consensus Movement of Nigeria, ta yi barazanar dakatar da ci gaba da jigilar kayan abincin zuwa Kudancin Nijeriya. Wannan gargaɗi na mazaunin martani ne ga wa'adin kwana 10 da mai rajin kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bai wa al'ummar Fulani makiyaya a baya-bayan kan su fice daga ƙasar Yarabawa. Da wannan, ƙungiyar Arewar ta ce ta sha alwashin ɗaukar dukkanin matakan da suka dace domin hana ci gaba da kwashe kayan abinci daga Arewa zuwa Kudu. Ta ƙara da cewa, dole Yarabawa mazauna…
Read More