Editor

9513 Posts
Mahaifin Gwamnan Anambra ya rasu yana da shekara 92

Mahaifin Gwamnan Anambra ya rasu yana da shekara 92

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya rasa mahaifinsa, Pa Simon Soludo. Pa Soludo ya rasu ne a ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya, inda ya bar duniya yana da shekara 92. Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan, Mr Christian Aburime ne ya sanar da rasuwar marigayin cikin wata gajeriyar sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta ce, Pa Soludo ya rasu ya bar 'ya'ya takwas da jikoki 22 da tattaɓa kunne shida.
Read More
Yadda za ki gyara nononki ta hanyar amfani da tumfafiya

Yadda za ki gyara nononki ta hanyar amfani da tumfafiya

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, Allah Ya ƙara mana lafiya da zaman lafiya. Da yardar mai kowa da komai, shafin Kwalliya na jaridar Manhaja na wannan makon zai waiwayi mata da ke neman hanyar gyara nonuwansu, kamar yadda muka sani a gyaran jiki, nono zai shiga a layin farko ga mata, kasancewar sa babban alama da ka iya bambanta mace da namiji, kuma kamar yadda matar manzoni rahma, Nana Aisha Allah Ya ƙara yarda da ita ta ce, gemu ne adon maza, yayin da nonuwa suke kwalliyar mata. Kenan gyara nono zai iya…
Read More
Dandalin shawara: Iyayena sun kai ni gidan mai mata huɗu a matsayin kuyanga da ya siya

Dandalin shawara: Iyayena sun kai ni gidan mai mata huɗu a matsayin kuyanga da ya siya

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Anti Aysha Asas ina yini, ya lamura? Don Allah kar ki ambaci sunana, ko garin da nake. Wallahi na matsu ne, shi ya sa zan fallasa wannan sirrin don Ina son na samu mafita, saboda yanzu kaina ya yi zafi kan lamarin, ban san inda zan fuskata ba. Ina da shekara sha uku, uwata da kawuna da mai unguwarmu da wanda uwata take zaune gida nai, tana taya matansa aiki, suka shirya da ni, muka taho cikin garin………….da kayana da komai nau. Muka taho gidan wani babban mutum da yake da mata huɗu, sai a gidan…
Read More
Shari’ar Gwamnan Kano: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jinkirtar da yanke hukunci zuwa gaba

Shari’ar Gwamnan Kano: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jinkirtar da yanke hukunci zuwa gaba

Daga BASHIR ISAH Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta Abuja ta jinkirtar da yanke hukunci kan ƙarar da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na Jam'iyyar NNPP ya shigar zuwa wani lokaci da ba ta bayyana ba. Abba ya ɗaukaka ƙara ne inda yake ƙalubalantar hukuncin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe wadda ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na Jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe gwamnan zaɓen jihar Kano. Idan za a iya tunawa, Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe a jihar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Oluyemi Akintan Osadebay, ta soke nasarar da Abba ya samu a zaɓen bayan da ta zabtare ƙuri'u 165,663 daga…
Read More
Magajin Rafin Haɗejia, Alhaji Babandede ya kwanta dama

Magajin Rafin Haɗejia, Alhaji Babandede ya kwanta dama

Daga ABUBAKAR MUHAMMAD TAHEER Magajin Rafin Haɗejia, Alhaji Muhammad Babandede Sarkiki ya rasu a daren Lahadin da ta gabata a ƙasar Misra bayan shafe tsawo lokaci yana fama da jinya. Marigayin shi ne Mahaifin Tsohon Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa CG. Muhammad Babandede. A halin rayuwarsa, alumma ta amfana da marigayin ta fannoni da da dama, kuma ya kasance uba ga al'ummar ƙasar Haɗejia da ma jihar Jigawa baki ɗaya. Zuwa yanzu Masaurautar Haɗejia ba ta sanar da lokacin jana'izar sa ba har sai an kawo gawarsa daga ƙasar Misra.
Read More
Kawo ƙarshen matsalar fyaɗe a Nijeriya

Kawo ƙarshen matsalar fyaɗe a Nijeriya

A kwanakin baya ne alqalin kotun da ke shari’ar laifukan fyaɗe da cin zarafin cikin gida da ke Ikeja, ya yanke wa daraktan kula da lafiya na gidauniyar kula da cutar daji, Dokta Olufemi Olaleye, hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan laifin yi wa ’yar uwar matarsa fyaɗe. An tuhumi Olaleye da laifuka biyu na lalata da kuma keta haddin ’yar uwar matarsa, laifukan da ake zarginsa da aikata tsakanin Maris 2020 da Nuwamba 2021. An gurfanar da wanda ake tuhuma a ranar 30 ga Nuwamba, 2022 kuma ya musanta aikata laifin. Kwana ɗaya da faruwar, kotun da ke zamanta a Legas,…
Read More
Kotun Allah ya isa: Tsakanin Allah ya isa da Allah ya yi albarka

Kotun Allah ya isa: Tsakanin Allah ya isa da Allah ya yi albarka

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Fassara ce ta Hausawa ko a ce kirari da a ke yi wa Kotun Qoli cewa “KOTUN ALLAH YA ISA” bisa ma’ana duk hukuncin da ta yanke sai dai a yi haƙuri wanda bai gamsu su ba ya ja Allah ya isa ko ya bar wa Allah wanda shi ne babban mai hukunci ga dukkan talikai kuma ya na ba wa wanda ya so matsayi ya kuma sauke wanda ya iso. Kazalika wanda ya gamsu da hukunci ya kan iya yi wa kotun kirrai a lokacin da kotun “ALLAH YA YI ALBARKA” don shari’a ta…
Read More
ASIKO ya ƙaddamar da shirin sauya wa ababen hawa amfani da fetur zuwa iskar gas

ASIKO ya ƙaddamar da shirin sauya wa ababen hawa amfani da fetur zuwa iskar gas

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano A daidai wannan lokaci da tsadar man fetur ke ta'azzara tsadar harkokin sufuri wani kamfanin iskar gas mai suna ASIKO Holding Energy ya vullo da tsarin sauyawa ababen hawa masu aiki da fetur zuwa na gas. Da yake zantawa da 'yan jarida, Manajan kasuwanci da hulɗa da jama'a na kamfanin Kwamared Haruna Wakili ya ce tun sama da shekaru 15 suke harkar gas a ƙara nan sun zo da wannan tsari ne saboda zamani ya zo ana taƙaita amfani da man fetur saboda yana gurɓata muhalli, shi ya sa ake cire masa tallafi da ya…
Read More
Faransa za ta maido wa Nijeriya $150m wadda Abacha ya wawushe

Faransa za ta maido wa Nijeriya $150m wadda Abacha ya wawushe

Daga BASHIR ISAH Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana a ranar Juma'ar da ta gabata cewa, ƙasar Faransa za ta maido wa Nijeriya kuɗi har Dala miliyan 150 wanda tsohon Shgugaban Ƙasa marigayi Janar Sani Abacha ya wawushe a halin rayuwarsa. Cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Faransa da matakin maido da kuɗin da ta ɗauka. Da yake karɓar baƙuncin Ministar Harkokin Wajen Faransa, Catherine Colonna, Shugaba Tinubu ya yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Faransa, yana mai cewa, fahimtar juna da ke…
Read More
JIBWIS ta raba wa iyayen marayu 500 miliyan biyar a Gombe

JIBWIS ta raba wa iyayen marayu 500 miliyan biyar a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Kimanin naira miliyan biyar Ƙungiyar Izala ta ravawa mata 500 da ke riqe da marayu a Gombe inda kowacce ta samu naira dubu goma a matsayin tallafi. Ƙungiyar Izala ta raba tallafin ne a ƙarƙashin Kwamitin Nisa'us Sunnah da ta kafa a Gombe ta zaƙulo mata iyayen marayun suka ci gajiyar shirin. Da yake jawabi a wajen taron Babban Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, jan hankalin iyaye mata ya yi da cewa su maida hankali wajen kula da tarbiyyar 'ya'yan da aka mutu aka bar su da su domin Allah…
Read More