Editor

9513 Posts
Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta bada belin Emefiele

Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta bada belin Emefiele

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Abuja ta bada belin tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele. Kotu ta bada belin yayin zaman da ta yi a ranar Laraba domin sauraren ƙarar neman beli da Emefiele ya shigar. Mai Shari'a Olukayode Adeniyi ne ya bada belin tare da miƙa Emefiele ga lauyoyinsa inda ake sa ran su gabatar da shi a Babbar Kotun Abuja a ranar 15 ga Nuwamba kotun da a nan ne EFCC ta shigar da ƙara a kan Emefiele da wani. Lauyoyin da kotun ta miƙa wa Emefiele su ne Matthew Burkaa (SAN)…
Read More
Bayan tsaftace ƙasa daga fasadi sai a waiwayi yunwa

Bayan tsaftace ƙasa daga fasadi sai a waiwayi yunwa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A lokacin da nake wannan rubutun, jami'an Hukumar Hisba ta Jihar Kano na can na aikin tantance matasan da jami'anta suka kama bisa laifin aikata fasadi, yawon dare, da mu'amala a wuraren da suke ɓata tarbiyyar al’umma, biyo bayan samame da suke kai wa a wasu gidajen karuwai, kulob-kulob, da ɓoyayyun wuraren da ɓatagari ke fakewa suna aikata ɓarna cikin dare a sassa daban-daban na cikin birnin Kano. Sannan a wata tattaunawa da tashar rediyon Freedom ta yi da wasu daga cikin waɗannan matasa sun bayyana wuraren da aka kama su, da abubuwan da suka ce…
Read More
Asara ce mace ta riƙe wayar N50,000 ba ta kawo mata N5,000 – Ayat Adamu 

Asara ce mace ta riƙe wayar N50,000 ba ta kawo mata N5,000 – Ayat Adamu 

"Idan ka ji shiru a gidan aure, ba ƙorafi, matar na sana'a" Daga AISHA ASAS  (Ci gaba daga makon jiya) Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Idan ba ku shafa'a ba, a satin da ya gabata, mun ɗauko tattaunawa da fitacciyar 'yar kasuwa mai kishin matan Arewa, Ayat Uba Adamu. Inda muka soma da jin tarihin rayuwarta, zuwa irin sana'ar da take yi, kafin mu tsunduma kan yadda take gudanar da kasuwancin nata. A tattaunawar, Hajiyar ta sheda wa Manhaja irin yunƙurin da ta yi na kafa ƙungiya musamman domin mata masu kasuwanci da ke tu'ammali da…
Read More
Zaɓuɓɓukan 11 ga Nuwamba: Za mu yi watsi da ƙuri’un duk rumfar zaɓen da aka samu hayaniya – INEC

Zaɓuɓɓukan 11 ga Nuwamba: Za mu yi watsi da ƙuri’un duk rumfar zaɓen da aka samu hayaniya – INEC

Daga BASHIR ISAH Yayin da rage 'yan kwanaki ƙalilan kafin zaɓen gwamna a wasu jihohin Nijeriya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta yi gargaɗin ba za ta kula ƙuri'un duk wata rumfar zaɓe da aka fuskanci tashin-tashina ba. Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya yi wannan gargaɗi yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar ranar Talata a Yenagoa, babban jihar Bayelsa. Ya zuwa ranar 11 ga Nuwamban da ake ciki ne ake sa ran INEC za ta gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin Bayelsa, Kogi da kuma Imo. Yakubu, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan INEC mai lura yankunan…
Read More
Zuwa ga mata: Bayan rabuwar aure (2)

Zuwa ga mata: Bayan rabuwar aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon. Sannunku da jimirin karatun filinku na Zamantakewa a jaridar Manhajarku mai farin jini. A makon da ya gabata na yi magana a kan zawarawa da barazanar da suke fuskanta. Yanzu za mu ɗora daga inda aka tsaya a wancan mako. A sha karatu lafiya. Yanzu za mu daga inda muka tsaya a cikin jerin dalilan da wasu zawarawan suke kauce hanya. Ko na ce suke yin ayyuka na rashi kamun kai. *Rashin haƙuri: Wasu matan da ma Allah ya halicce su da ɗabi'ar rashin haƙurin iya zama ba…
Read More
Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya kan rasuwar Sheikh Yusuf Ali

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya kan rasuwar Sheikh Yusuf Ali

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Yusuf Ali, wanda ya rasu a safiyar ranar Litinin, yana da shekaru 73 a duniya. Shugaban ya aike da saƙon alhini zuwa ga iyalai, ɗalibai, da kuma mabiya wannan malami da ke Kano, da ma Masarautar Gaya wanda wannan malami ke kan karagar Sarkin Malamanta a lokacin rayuwarsa. Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyar ne ta hannun mai magana da yawunsa, wato Ajuri Ngelale. Ya bayyana rasuwar jagoran addinin a matsayin wani babban abun alhinin da ya karaɗe muryoyin jama'a a faɗin ƙasar nan, duba da irin…
Read More
An kammala ɗaukar shirin fim ɗin ‘Princess Of Galma’

An kammala ɗaukar shirin fim ɗin ‘Princess Of Galma’

DAGA MUKHTAR YAKUBU A ƙarshen satin da ya gabata ne aka kammala ɗaukar shirin fim na Turanci mai suna 'Princess Of Galma' wanda aka shafe tsawon kwanaki 12 ana gudanar da shi. Shirin wanda kamfanin da ya saba shirya finafinan Turanci a Kannywood na Jammaje Productions ya ɗauki nauyin shirya shi kuma aka yi aikin sa a cikin garin Kano a wannan lokacin, kuma ƙwararren darakta Galadima Muhammad ne ya bayar da umarni yayin da jarumai irin su Magaji Mijinyawa na 'Gidan Badamasi', Ishak Sidi Ishak, Hajara Makama, Faruk Sayyadi, Mustapha Musty, Zainab Bichi, Aisha A Musa, da sauran jarumai…
Read More
Mafi yawan samarin da ke nuna ra’ayi kaina, kuɗina suke so ba ni ba, inji jarumar barkwanci Ashmusy

Mafi yawan samarin da ke nuna ra’ayi kaina, kuɗina suke so ba ni ba, inji jarumar barkwanci Ashmusy

Daga AISHA ASAS Shahararriyar 'yar wasan barkwanci Ashmusy, ta bayyana cewa, kaso mai yawa na samarin da ke matsowa wurinta da sunan soyayya sun zo ne su yi kuɗi da ita. Jarumar ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da ita, inda ta faɗi hakan a matsayin dalilin da ya sa har yau ba ta da saurayin da za ta iya kira da masoyinta. Sannan ta ƙara da cewa, a nata ra'ayi za ta so ta samu saurayin da yake da abin yi, yake amsar albashi kowanne wata, amma fa ba wanda ya fi ta samu ba.…
Read More
Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta maida martani kan jan hankalin da Amurka ta yi wa ‘yan ƙasar mazauna Nijeriya

Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta maida martani kan jan hankalin da Amurka ta yi wa ‘yan ƙasar mazauna Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta maida martani kan gargaɗin da ƙasar Amurka ta yi wa 'ya'yanta mazauna Nijeriya game da zama a otel-otel na ƙasar, tana mai jaddada buƙatar da a daina biye wa batutuwan da ka iya haifar da rarraba kawuna. Kazalika, Gwamnatin Nijeriya ta bada tabbacin cikakken tsaro ga rayukan 'yan ƙasar da ma baƙi mazauna ƙasar. Har wa yau, ta ce ta ɗauki ingantattun matakan tsaro da suka haɗa da tattara bayanan tsaro, haɗa ƙarfi da hukumomin ƙasashen duniya da sauransu domin tabbatar da tsaron rayukan baƙi. Waɗannan bayanai sun fito ne daga bakin Ministan Larabai…
Read More
Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA (2)

Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA (2)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Cigaba daga makon da ya gabata. Ya na iya zama abin farin ciki sanin cewa, Sheikh Ibrahim Saleh ya yi shekaru ashirin ne kacal (1944-1964) a matsayin ɗalibi, kuma ya samu kusan dukkan horon da ya yi a Nijeriya. Duk da haka, wannan ba ya na nufin cewa dukkan malamansa ’yan Nijeriya ne ba. Amma duk da haka, ya kasance masani na gida, wadda aka samar a cikin gida ta hanyar tsarin Tsangaya. Watau, horon da ya samu a cikin tsarin karatun gida ne ya ba shi damar kasancewa mashahuri a ƙasashen duniya, da kuma karrama…
Read More