04
Nov
Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Guinea na nuni da cewa, ana zargin yunƙurin juyin mulki a ƙasar bayan da aka jiyo ƙazamar musayar wuta a Conakry, babban birnin ƙasar, a wannan Asabar ɗin. Shaidu sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, jami'an tsaro sun yi wa yankin ƙawanya, ba shiga ba fita. Wata majiya da aka sakaya sunanta ta ce, “Ana musayar wuta daga tsakanin ɓangarorin da lamarin ya shafa tare da harba makaman yaƙi a Kaloum." “Tun da asuba aka kulle garin, ba shiga, ba fita," in ji wani ɗan kasuwa a yankin. Guinea na ɗaya…
