Editor

9513 Posts
Yadda Ganduje ya daidaita sahu wajen kaɗa ƙuri’a, ya yaba wa na’urar BVAS

Yadda Ganduje ya daidaita sahu wajen kaɗa ƙuri’a, ya yaba wa na’urar BVAS

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Kyamarar wakilinmu a Kano ta samu sa'ar ɗaukar Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, a lokacin da ya daidaita sahu ya bi layi kamar sauran jama'a wajen kaɗa ƙuri'arsa. Ganduje ya jefa ƙuri'ar tasa ce a mazaɓarsa ta Cikin-gari mai lambar akwatu 008 da ke garin Ganduje, Ƙaramar Hukumar Dawakin-Tofa, Kano. Ganduje a wajen zaɓe Gwamnan ya yaba tare da jinjina wa hukumar zaɓe ta INEC bisa matakin yin amfani da na'urar BVAS wajen tantance masu zaɓe. Ya ce, amfani da na'urar zai taimaka wajen damun sahihin zaɓe a Nijeriya.
Read More
HOTUNA: Gwamnan Nasarawa ya jefa ƙuri’a

HOTUNA: Gwamnan Nasarawa ya jefa ƙuri’a

Daga TIDZALLA ZACCHAEUS a Nasarawa Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya kaɗa ƙuri'arsa a mazaɓarsa mai lamba 001 da ke Gudi, cikin Ƙaramar Hukumar Akwanga. Ya kaɗa ƙuri'ar ce da da misalin ƙarfe 11:49 tare da matansa biyu. Gwamna Sule na daga cikin jerin gwamnonin da ke neman wa'adin mulki na biyu.
Read More
Yanzu-yanzu: Shugaban PDP na Abuja ya mutu a haɗarin mota

Yanzu-yanzu: Shugaban PDP na Abuja ya mutu a haɗarin mota

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP, a babban birnin tarayya Abuja, Sunday Dogo Zaka ya rasu. Blueprint Manhaja ta samu labarin cewa, Zaka ya mutu sa'o'i kaɗan kafin zaɓen Shugaban Ƙasa da ake gudanarwa a yau Asabar a wani hatsarin da ya rutsa da shi a ƙaramar hukumar Kuje. Kamar yadda wata majiya ta kusa, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana, motar Zaka ta yi karo da falwayar wutar lantarki a kusa da gidansa da ke Kuje a lokacin da yake dawowa daga ganawa da Sanata Philip Aduda da misalin ƙarfe 3 na…
Read More
Yadda zaɓe ke gudana a Mazaɓar Gwammaja

Yadda zaɓe ke gudana a Mazaɓar Gwammaja

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano A Mazabar Gwammaja da ke Firamaren Masaƙa a Ƙaramar Hukumar Dala cikin birnin Kano. Inda al'umma wannan yanki suka fito maza da mata suke kaɗa ƙuri'arsu, Kayan zaɓe da malaman zaɓe sun isa tun ƙarfe 8 da 'yan mintoci. Da misalin ƙarfe 8:40 na safe ne dai aka fara kaɗa ƙuri'a. Jama'ar wannan yankin suna ci gaba da shigowa cikin wannan mazaɓa domin gudanar da zabensu. Haka dai labarin yake game da akwati na 27 da ke wannan makaranta.
Read More
Laifukan zaɓe da yadda za a ƙaurace musu

Laifukan zaɓe da yadda za a ƙaurace musu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau Asabar miliyoyin ’yan Nijeriya masu katin zaɓe za su fita rumufunan zaɓe domin kaɗa ƙuri’ar zaɓen shugaban da zai gaji Muhammad Buhari. Baya ga shugaban ƙasa, ’yan ƙasar za su zaɓi ’yan Majalisar Wakilia 360 da kuma sanatoci 109 a zaɓen yau ranar Asabar. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro sun bayyana shirinsu na tunkarar babban zaɓe na yau. Za a gudanar da zaɓukan ne a mazaɓu 1,491 da ke ƙananan hukumomi 774 da ke jimillar rumufunan zaɓe 176, 846 a kasar mai jihohi 36 da kuma Babban Birnin…
Read More
Gwamnan Kogi ya kaɗa ƙuri’arsa a Okene

Gwamnan Kogi ya kaɗa ƙuri’arsa a Okene

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello tare da mai ɗakinsa, sun bi sahun sauran 'yan Nijeriya wajen kaɗa ƙuri'arsu a bababban zaɓen da ke gudana a faɗin Nijeriya a wannan Asabar. Bello ya kaɗa ƙuri'ar tasa ne a rumfar zaɓe ta 11 da ke Agasa Uvete, Okeneba, Okene. Bayanai sun tabbatar Gwamnan ya isa rumfar zaɓen ne da misalin ƙarfe 9.40 na safe inda shi ma ha shiga layi ya tsaya a bayan waɗanda suka riga shi zuwa. Bayan tantance shi da na'urar BVAS, Bello ya kaɗa ƙuri'arsa da misalin ƙarfe 10. Jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri'ar tasa,…
Read More
Sanata Lawan ya kaɗa ƙuri’arsa

Sanata Lawan ya kaɗa ƙuri’arsa

Daga WAKILINMU Shugaban Majalisar Dattawa kuma ɗan takarar sanata na APC a Yobe ta Arewa, Ahmed Ibrahim Lawan, ya kaɗa ƙuri'arsa cikin nasara. Ya kaɗa ƙuri'ar tasa ce a rumfar zaɓen da ke makarantar firamaren Katuzu da ke Gashua, Ƙaramar Hukumar Bade, Jihar Yobe. Lawan ya kaɗa ƙur'ar ne da misalin ƙarfe 11:01 na safe, inda ya yaba wa hukumar zaɓe INEC dangane da ƙoƙarin da ta yi wajen shirya wannan zaɓe.
Read More
Kano: An samu jinkirin kayan zaɓe a rumfar zaɓen ƙofar gidan mai unguwa ta mazaɓar Dakata

Kano: An samu jinkirin kayan zaɓe a rumfar zaɓen ƙofar gidan mai unguwa ta mazaɓar Dakata

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai shaɗayan rana ta wuce ana cigaba da dakon kayan aikin zave daga INEC don fara gudanar da zaɓe a mazaɓar dakata ta jihar Kano. Inda abin yake faruwa kuwa shi ne, akwatin da yake ƙofar gidan mai unguwa na wannan yanki na mazaɓar dakata. A halin yanzu dai al'umma sun yi dafifi sun fito domin kaɗa ƙuri'unsu a wannan rumfar zaɓe mai akwati tara, amma shiru kake ji kamar an shuka dusa. Wani shaidar gani da ido mai suna Malam Jibril wanda shi ma ɗan mazaɓar ta dakata ne ya bayyana cewa,…
Read More