Editor

9513 Posts
Zaɓen 2023: Buhari ya kaɗa ƙuri’arsa

Zaɓen 2023: Buhari ya kaɗa ƙuri’arsa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari tare da mai ɗakinsa, Aisha, gami da sauran ahalinsa sun kaɗa ƙuri'arsu a rumfar zaɓe ta 003, a Sarkin Yara A, Ƙofar Baru da ke Daura, Jihar Katsina. Bayanai sun nuna Shugaba Buhari da ahalin nasa sun isa rumfar zaɓen ne da misalin ƙarfe 9.57 na safe. Ba da ɓata lokaci ba aka tantance Buhari kana aka ba shi damar kaɗa ƙuri'arsa. Buhari ya yi kira da a yi zaɓe cikin lumana kana 'yan takara kowa ya yarda da sakamakon zaɓen bayan kammalawa.
Read More
Da ɗumi-ɗumi: INEC ta ɗage zaɓen kujerar Sanatan Enugu ta gabas

Da ɗumi-ɗumi: INEC ta ɗage zaɓen kujerar Sanatan Enugu ta gabas

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, (INEC), ta sanar da ɗage zaɓen kujerar Sanata na Enugu ta gabas zuwa 11 ga watan Maris na wannan shekarar. Hakan ya biyo bayan kisan ɗan takarar wannan kujerar na jamiyyar LP, Barista Oyibo Chukwu, wanda aka yi a ranar Laraba, 22 ga Fabrairun 2023. Shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a yayin taron 'yan jarida ɗazu a Abuja. A cewar sa, wannan sanarwa ta dogara ne da dokar zaɓe ta kundin mulkin ƙasar nan da ta ba wa jamiyyar da ta rasa ɗan takararta…
Read More
Zargin ƙulla maguɗin zaɓe: Atiku ya fayyace komai

Zargin ƙulla maguɗin zaɓe: Atiku ya fayyace komai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga wani faifan murya da aka yi masa na zargin cewa yana shirin yin maguɗi a ranar Asabar, 25 ga Fabrairu, 2023, a zaɓen shugaban ƙasa. An zargi abokin takarar Atiku kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, tare da shugaban jam'iyyar PDP na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa (PDPPCC), da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal. Da yake mayar da martani, kakakin jam’iyyar PDP, Phrank Shuaibu, a wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce aikin jam’iyyun adawa ne. Sanarwar ta ce, “mun yi gargaɗi…
Read More
Mu guji sayar da ‘yancinmu a ranar zaɓe

Mu guji sayar da ‘yancinmu a ranar zaɓe

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Kwanci tashi ba wuya ga mai yawan rai. Idan Allah ya kai mu gobe Asabar cikin rayayyu, ’yan Nijeriya miliyan 93 da dubu ɗari 5 ake sa ran za su fita su kaɗa ƙuri'unsu a rumfunan zaɓe 176,606 a dukkan faɗin ƙasar nan. Kamar yadda muke sane wannan zave da za a yi ya shafi matakin ƙasa ne, wato Shugaban Ƙasa, Ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya, da kujerar Ɗan Majalisar Dattijai. Yayin da zaɓe na gaba zai shafi kujerar Gwamna, da ’Yan Majalisar Jihohi. Wani batu mai muhimmanci da ya ke ɗaukar hankalin ’yan Nijeriya musamman…
Read More
Sarkin Kano, Aminu Bayero ya yi fatan a yi zaɓuɓɓuka lafiya

Sarkin Kano, Aminu Bayero ya yi fatan a yi zaɓuɓɓuka lafiya

Daga RABIU SANUSI a Kano Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya buƙaci al'ummar Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya da su kasance masu ƙaunar zaman lafiya yayin zaɓuɓɓukan da za a gudanar da ma bayansu. Sarkin ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da jawabi na musamman ga manema labarai a fadarsa. Ya ce sai da zaman lafiya ake iya aiwatar da komai, don haka ya buƙaci matasa su guji furta munanan kalamai da ta'ammali da makamai da shaye-shaye don kaucewa daga fadawa mummunan hali. Basaraken ya kuma jaddada buƙatar hakimai da dagatai da…
Read More
‘Yan sanda sun cafke gomman ‘yan daban siyasa a Kano

‘Yan sanda sun cafke gomman ‘yan daban siyasa a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano A tsaka da shawartar shugabanin jami'iyyu daban daban a Jihar Kano wajen tausar su game da ƙudurin fitowar neman goyon bayan jama'a daga masoyansu da sabon Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, CP Muhmmad Yakubu ya gana da su. Kamar yadda aka sani a ranar Alhamis ne 23 ga wannan watan dokar yakin neman zaɓe ta haramta ci gaba da yawon neman goyon baya ga duk wani ɗan siyasa, wanda a Kano ma haka abin yake daga ranar babu wanda zai ƙara fitowa a rana ta gaba kenan. Duk da haka wasu daga cikin jam'iyyu ba…
Read More
Zaɓen 2023: An zo wajen!

Zaɓen 2023: An zo wajen!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Da gani ko da duba agogo an zo wajen gudanar da babban zaɓen Nijeriya na 2023. Duk wasu shirye-shirye na wannan zaɓe sun kammala. Ko ma dai yaya lamarin zai kasance a tsarin zaɓen Nijeriya da a kan gudanar bayan shekaru 4 ko a ce yayin da wanda ya ke kan kujera ya cika shekaru 4 kan mulki zai sauka a sanadiyyar faɗuwa zave ko kuma kammala wa’adi biyu na tsawon shekaru 8. Shugaban Nijeriya da ke kan gado Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa a ranar 29 ga watan mayu mai zuwa. Don haka za…
Read More
INEC ta gargaɗi marasa katin zaɓe kan halartar rumfunan zaɓe

INEC ta gargaɗi marasa katin zaɓe kan halartar rumfunan zaɓe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta gargaɗi ’yan Najeriya da ba su da katin zaɓe, da su ƙaurace wa rumfunan zaɓe a ranar zaɓe. Kwamishinan INEC na Ƙasa, Festus Okoye, ne ya bayyana haka a lokacin da yake karɓar kayayyakin gudanar da zaɓe a ranar Alhamis a Abuja. Okoye wanda shi ne shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, ya ce babu wata hanyar tantancewa da za a yi amfani da su a ranar zaɓe, in ban da katin zaɓe na dindindin ba. “Yayin da ’yan Nijeriya ke fitowa…
Read More
Zaɓe: Tarihi ya maimaita  kansa a Kebbi

Zaɓe: Tarihi ya maimaita  kansa a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Tun lokacin da iskar guguwar siyasa ta soma kaɗawa dai 'yar manuniya ta nuna tarihi zai maimaita kansa bisa irin cin kashin da aka yi wa jam'iyyar PDP a lokacin mulkin shugaban Goodluck Ebele Jonathan. Jihar Kebbi ma bisa ga dukkan alamu ta bi sahun waɗansu jihohi inda a kullum safiya ta Allah al'umma sai tururuwa suke yi suna canza sheƙa daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa PDP ta adawa. Alhaji Ibrahim Kunne Gulma wani jigo ne a jam'iyyar APC da babban hadimin tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Alhaji Bilyaminu Bawale Sardaunan matasan…
Read More
Yadda zaɓen 2023 ya sha bamban da sauran

Yadda zaɓen 2023 ya sha bamban da sauran

*Addinanci, ƙabilnci da ɓangaranci ba baqi ne a siyasar Nijeriya ba!*Shin za a iya zuwa zagaye na biyu? Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja A gobe Asabar ne za a gudanar da Babban Zaɓe a Nijeriya bayan shafe kusan shekaru huɗu na zango na biyu da shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, ya yi a kan kujerar mulkin ƙasar. Kowane zaɓe ya kan zo da yanayinsa kuma ya kan sha bamban da na bayansa. Siyasar addinanci da ɓangaranci ko ƙabilanci ba baƙin abubuwa ba ne a Nijeriya. Don haka ba su daga cikin abubuwan da zaɓen 2023 ya bambanta da na…
Read More