Editor

9513 Posts
2023: An cafke shugabannin ƙananan hukumomi biyu da bindigogi a Kano

2023: An cafke shugabannin ƙananan hukumomi biyu da bindigogi a Kano

*’Yan daba sun farmaki magoya bayan Kwankwaso Daga IBRAHIM HAMISU a Kano An cafke wasu shugabannin ƙananan hukumomi guda biyu na Jihar Kano sakamakon zargin da ake yi na kama su bindigogi da aka yi a yayin gangamin siyasa jiya, Alhamis. Bugu da ƙari, wasu ’ƴan daba da ake kyautata zaton ’ƴan bangar siyasa ne, sun farmaki magoya bayan ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar adawa ta NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, a Jihar Kano. Rahotonni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a unguwar Na’ibawa da ke kan titin zuwa Zariya. Blueprint Manhaja ta rawaito cewa, yayin farmakin, magoya…
Read More
Buhari ya isa Katsina domin kaɗa ƙuri’a gobe

Buhari ya isa Katsina domin kaɗa ƙuri’a gobe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya isa Jihar Katsina, inda daga nan ne zai zarce zuwa Daura, mahaifarsa, domin halartar zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi gobe Asabar.Jirgin shugaban ya sauka a filin jirgin saman Umar Musa Yar’Adua da misalin ƙarfe 4:40 na yammacin jiya Alhamis, 23 ga Fabrairu, 2023. A gobe Asabar ne ake sa ran zai kaɗa ƙuri’arsa ga ‘yan takarar da yake so a Daura. Kafin ya bar Abuja zuwa Katsina, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, Buhari ya kira taron majalisar tsaro, inda ya…
Read More
Yadda gwamnonin Nijeriya suka butulce wa Shugaba Buhari bayan ya fitar da su kunya

Yadda gwamnonin Nijeriya suka butulce wa Shugaba Buhari bayan ya fitar da su kunya

Daga BASHIR AHMAD Yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ceto gwamnonin Nijeriya daga halin ni-`ya-su na matsin tattalin arziki a yayin da jihohinsu suka shaƙi ƙamshin mutuwa ta hanyar bijiro da tallafin Gwamnatin tarayya ba voyayyen abu ba ne a ƙasar nan, kowa ya sani. Shakka babu jama’a na ankare da yadda gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari, ta samu Nijeriya a cikin wani mayuwacin hali a shekarar 2015, baya ga fama da matsaloli masu nasaba da rashin tsaro da ayyukan tayar da ƙayar baya na Boko Haram, akwai kuma matsalar tattalin arziki da sauran matsalolin da suka tilasta wa ƙasar…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan sanda sun cafke ɗan majalisa ɗauke da $500,000 a Ribas

Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan sanda sun cafke ɗan majalisa ɗauke da $500,000 a Ribas

Daga WAKILINMU 'Yan sanda a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, sun cafke ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Chinyere Igwe, da safiyar Juma'a ɗauke da kuɗi sama da Dala dubu 500 ($500,000.00), yayin da ya rage sa'o'i 24 kafin zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisar tarayya a Nijeriya. Binciken Blueprint Manhaja ya gano cewa, kuɗin da aka kama Igwe da shi ana zargin ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya ba shi tare da wata takarda mai ɗauke da sunayen ƙananan hukumomi 23 na jihar da hukumomin tsaro da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC). Sai dai…
Read More
‘Yan sanda sun kama magidanta biyu da su ka yi garkuwa da amarya a Adamawa

‘Yan sanda sun kama magidanta biyu da su ka yi garkuwa da amarya a Adamawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu magidanta su biyu, Suleman Adamu da abokinsa Amadu, sun shiga komar 'yan sanda a Jihar Adamawa bisa zargin su da yin garkuwa da amarya a ranar da aka kai ta ɗaki. Rahma Radio FM ta rawaito cewa mutanen sun shiga gidan ne lokacin da angon amaryar, Abubakar ya fita ya sayi kazar sayen baki. Da ya ke zantawa da manema labarai, angon ya ce mutane biyun, ɗaya makwabcinsa ne, ɗayan kuma ma surukinsa ne. A cewarsa, ya fita ne ya sayo wa amarya kaza, shi ne sai su ka afka gidan na sa,…
Read More
Zargin sayen ƙuri’u: Jami’an EFCC za su sanya ido a wuraren kaɗa ƙuri’a

Zargin sayen ƙuri’u: Jami’an EFCC za su sanya ido a wuraren kaɗa ƙuri’a

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC, ta tura jami’anta zuwa jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya, domin sanya ido a zaɓen da za a gudanar gobe Asabar. Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ce tura sojojin wani ɓangare ne na ƙoƙarin tabbatar da sahihancin zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023. Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya buƙaci jami’an da su kasance masu lura da maslahar al’umma tare da nuna ƙwarewa…
Read More
2023: Kano ta zarce ko’ina yawan wakilan jam’iyyu

2023: Kano ta zarce ko’ina yawan wakilan jam’iyyu

•Yayin da APC, PDP da NNPP suka tura sama da wakilai 1.5 Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, a ranar Litinin ta fitar da adadin wakilan jam'iyyu a rumfunan zaɓe da wajen tattara sakamako kamar yadda jam’iyyu suka miqa wa INEC sunayensu don babban zaɓen 2023. Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, jimillar wakilan rumfunan zaɓe na jam'iyya 1,574,301 da kuma wakilai 68,057 ne jam'iyyun siyasar ƙasar suka miƙa wa INEC. A taƙaice dai, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta tura wakilai 176,223 rumfunan zaɓe a duk faɗin ƙasar;…
Read More
INEC ta fara raba muhimman kayan zabe a Yobe

INEC ta fara raba muhimman kayan zabe a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da fara rarraba muhimman kayayyakin zaɓe a faɗin Jihar Yobe. Da yake sanar da fara raba kayan, Kwamishinan Hukumar Zaɓen a Jihar Yobe (REC), Alhaji Ibrahim Abdullahi, a sa'ilin da yake ganawa da manema labarai a reshen Babban Bankin Nijeriya (CBN) dake Damaturu, da safiyar ranar Alhamis. Ya ce, “A daidai lokacin da ya rage saura kwana biyu a gudanar da zaɓen, abin da suka dace mu aiwatar a halin yanzu shi ne mu tabbatar mun fara raba waɗannan kayayyakin zaɓen zuwa cibiyoyin da muke da…
Read More
HOTUNA: INEC na ci gaba da raba kayan zaɓe

HOTUNA: INEC na ci gaba da raba kayan zaɓe

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) na ci gaba da raba kayayyakin zaɓe zuwa jihohi don shirye-shiryen zaɓuɓɓukan da ke tafe. Ga hutunan kaɗan daga yanayin yadda rabon kayayyakin ke gudana: Jihar Imo: Jihar Kaduna: Jihar Adamawa: Jihar Ekiti: Jihar Ribas:
Read More
‘Yan bindiga sun kashe ɗan takarar sanata a Inugu

‘Yan bindiga sun kashe ɗan takarar sanata a Inugu

Daga BASHIR ISAH 'Yan sanda a Jihar Inugu sun tabbatar da 'yan bindiga sun kashe ɗan takarar sanata na Jam'iyyar Labour a shiyyar Inugu ta Gabas, Oyibo Chukwu. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Inugu, Daniel Ndukwu, ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis. Ya ce lamarin ya faru ne ranar Laraba bayan da 'yan bindigar suka yi wa motar marigayin kwanton-ɓauna suka banka mata wuta, kamar yadda jaridar News Point ta rawaito. A cewar jami'in, “sun kai hari tare da ƙona motar kamfe ɗin Jam'iyyar Labour a Eke-Otu Amechi-Awkunanaw da ke Inugu, inda…
Read More