Editor

9513 Posts
‘Yan bindiga sun kashe ‘yan siyasa 5 a Inugu

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan siyasa 5 a Inugu

Daga WAKILINMU A ƙalla mutum biyar ake fargabar sun mutu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai wa wata mota ƙirar Sienna mallakar ɗan takarar sanata na Jam'iyyar a shiyyar Inugu ta Gabas, wato Barista Oyibo Chukwu. Majiyarmu ta ce harin ya auku ne ranar Laraba a yankin Amechi Awkunanaw da ke cikin Ƙaramar Hukumar Inugu ta Kudu a jihar. Wani ganau ya ce maharan sun banka wa motar wuta ne alhali akwai mutane a cikinta. Bayanai sun nuna waɗanda lamarin ya shafa suna kan zagayen tallata ɗan takararsu ne inda suka gamu da ajalin nasu. Sai dai babu cikakken…
Read More
Zaɓen 2023: Lokacin huce haushin talaka

Zaɓen 2023: Lokacin huce haushin talaka

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Kusan kowa a ƙasar nan, a kusa yake! Ma'ana a cikin fushi ko matsuwa yake, saboda yadda abubuwa suke tafiya a ƙasar nan. Hatta waɗanda suka taka wani mataki a Tudun Mun Tsira da waɗanda ke kusa da gwamnati, su ma ba lallai suna ganin yadda suke so ba. Rayuwa ta zama wani iri, 'yan Nijeriya sun samu kansu a wata irin rayuwa marar tabbas! Rashin tabbas ya zama shi ne kaɗai tabbas a ƙasar nan!! Ƙarfi da yaji talaka ya koyi wata irin rayuwa da a baya bai san da ita ba, wani ma ko…
Read More
BIDIYO: ‘Yan takarar shugabancin ƙasa sun haɗu wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

BIDIYO: ‘Yan takarar shugabancin ƙasa sun haɗu wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Daga BASHI ISAH Domin tabbatar da zaman lafiya yayin zaɓe mai zuwa, 'yan takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam'iyyu 18, sun haɗu a Abuja don rattaba hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya. Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci sauran mamabobin kwamitin zaman lafiya zuwa wajen taron. An ga manyan 'yan takarar Shugaban Ƙasa, irin su Bola Tinubu na APC da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na jam'iyyar Labour da Omoyele Sowore na AAC da Rabiu Kwankwaso NNPP da sauransu, sun hallara. Ga bidiyon sashen taron:
Read More
BIDIYO: An gano tulin Katin Zaɓe ɓoye a dajin Anambra

BIDIYO: An gano tulin Katin Zaɓe ɓoye a dajin Anambra

Daga WAKILINMU Yayin da ya rage kwana uku kafin zaɓen 2023, an gano tulin Katin Zaɓe da aka ɓoye a daji a yankin Ƙaramar Hukumar Nnewi ta Arewa a Jihar Nnewi Anambra. Wani faifan bidiyon da aka yaɗa ya nuna wasu mahauta biyu suka gano katin a cikin jaka a dajin ƙauyen Akamili da ke yankin a ranar Talata inda suka ɗauka suka kai tashar Authority FM da ke yankin. Bayanai sun ce galibin katin na jama'ar yankin Ƙaramar Hukumar Nnewi ta Arewa ne. Kuma cewa, an kwashi katin an kai an miƙa wa shugabannin yankin. Da aka nemi jin…
Read More
Canjin kuɗi: Kotun Ƙoli ta tafi hutu

Canjin kuɗi: Kotun Ƙoli ta tafi hutu

Daga WAKILINMU Kotun Ƙoli mai sauraron shari’ar sauyin kuɗi tsakanin gwamnatocin jihohi 13 da Gwamnatin Tarayya ta tafi hutu. Alƙalan kotun su bakwai ƙarƙashin Mai Shari’a Inyang Okoro sun ce sun tafi hutu domin bai wa lauyoyin ɓangarorin da ke shari’ar damar yin musayar takardu. Hakan na zuwa ne bayan Jihar Ribas ta shiga jeri a matsayin ta 13 a cikin jihohin da ke ƙalubalantar sauyin kuɗin da gwamnati ta yi. Tun da farko, Mai Shari’a Inyang Okoro, ya ce ya zama tilas kotun ta cimma matsaya a kan shari’ar a zamanta na yau. Wannan shi ne zama na biyu…
Read More
HOTUNA: INEC ta fara raba kayan zaɓe

HOTUNA: INEC ta fara raba kayan zaɓe

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fara raba kayan zaɓe zuwa sassan ƙasa domin gudanar da zaɓe ranar Asabar mai zuwa. Hutunan da aka yaɗa a ranar Laraba sun nuna yadda ma'aikata ke ƙoƙarin loda kayan zaɓe a motoci a harababr Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ke Marina a Legas yayin da jami'an tsaro suka kewaye su.
Read More
Ƙwaƙwalwar yaro ta fi buƙatar kulawa daga wata shida na haihuwa zuwa shiga firamare – Hauwa Mustapha Babura

Ƙwaƙwalwar yaro ta fi buƙatar kulawa daga wata shida na haihuwa zuwa shiga firamare – Hauwa Mustapha Babura

"A ƙasashen da suka cigaba suna fara ba yara tarbiyya tun suna ciki" Daga ABUBAKAR M. TAHIR Tabiyyar yara na ɗaya daga cikin manyan buƙatun da kowacce ƙasa mai son cigaba ta ke da buƙata, domin da yara ne ake samun manya, kamar yadda bahaushe ya ce, "yara manyan gobe", kuma daga manyan ne ake samun ingantacciyar ƙasa ko akasin haka. Duk da muhimmancin yara a rayuwar al'umma bai sa wasu mutane ɗaukar reno tare da tarbiyyantar da zu a matsayin wani babban aiki ko abinda ke buƙatar sa ido ba, idan ka ɗauki bahaushe a misali, za ka tarar…
Read More
Lokacin farkawar Arewa ya yi!

Lokacin farkawar Arewa ya yi!

Daga ZAINAB AHMAD BINT HIJAZI Sau da yawa, nakan zauna na yi wa kaina wasu tambayoyi masu ɗaure kai kamar haka: Anya da gaske muke idan muka ce muna son gyara ƙasar nan kuwa? Anya mu 'yan Arewa mun san ciwon kanmu kuwa? Yaushe za mu yi wa kanmu faɗa a kan abin da ya dace da mu da wanda bai dace da mu ba? Yaushe za mu daina zama kamar mayunwatan kaji masu jiran a watsa musu tsabar su tsattsaga? Ba mu ganin yadda al'ummomin wasu yankunan na Nijeriya suke yi ne? Waɗannan tambayoyin sun ƙara ƙaimi a zuciyata…
Read More
Me ya ɗimauta El-Rufa’i?

Me ya ɗimauta El-Rufa’i?

Daga Muhammad Bello Sharaɗa Nasir El Rufai ya fada wa BBC lokaci zai yi cewa zai bayyana sunayen ƙarara na mutanen da suke yi wa Buhari maƙarƙashiya kuma suke ba shi muguwar shawara. Kuma ya ce zai bayyana waɗanda basa son Tinubu ya yi nasara. A kwanan nan kuma El-Rufa'i ya gaya wa jama'a kowa ya ɓoye takardar nairori da yake da ita, da zarar Sanata Uba Sani ya zama gwamnan jihar Kaduna za su tsaya da shi da Tinubu su dawo wa da kowa kuɗinsa, babu kuɗin kowa da za su yi ciwon kai. El Rufai fa da shi…
Read More
Yadda cinikin bayi ya shafi Arewacin Nijeriya

Yadda cinikin bayi ya shafi Arewacin Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Cinikin bayi wani lamari ne mai ɗumbin tarihi wanda ya samo asali shekaru aru-aru. A duk lokacin da baƙar fata suka tuna da yanayin da kaka da kakanninsu suka shiga a zamanin cinikin bayi, akasarin su suna fuskantar ɓacin rai. An shafe sama da shekaru 400 ana gudanar da cinikin bayi inda akasarin bayin ana ɗibarsu ne daga nahiyar Afrika a tafi da su sauran nahiyoyi musamman yankin Amurka da Turai. Nijeriya na daga cikin ƙasashen yammacin Afrika da ke da guraren da aka mayar cibiyoyin hada-hadar bayi kamar Badagry da ke wajen birnin Legas a…
Read More