Editor

9513 Posts
Sarkin Kano ya yi kira kan zaɓen shugaba nagari

Sarkin Kano ya yi kira kan zaɓen shugaba nagari

Daga RABIU a SANUSI Kano Mai Martaba Sarkin Kano, Dr. Aminu Ado Bayero, ya bukaci al'umma da su zaɓi cancanta a wannan zaɓen. Dr. Aminu Ado Bayero ya yi wannan kira ne jim kaɗan bayan ya dangwala ƙuri'arsa a akwatinsa da ke cikin Ado Bayero Islamiyya a fadar sa, birnin Kano. Sarkin ya ce kamar yadda kowa ya sani yau ce ranar da ake zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar tarayya. "Kamar yadda kowa ya fito yake zaɓe mu ma yau ya dace mu fito mu gudanar da namu zaɓen ga wanda muka san ya cancanta da muke ganin…
Read More
Shettima ya fice daga rumfar kaɗa ƙuri’a sakamakon rashin ma’aikatan INEC

Shettima ya fice daga rumfar kaɗa ƙuri’a sakamakon rashin ma’aikatan INEC

Daga AISHA ASAS Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC, Kashim Shettima, a yau Asabar ya isa mazaɓar sa ta Shettimari mai lamba 001 a unguwar Lawan Bukar da ke cikin birnin Maiduguri, sai dai ya kasa kaɗa ƙuri'arsa sakamakon rashin isowar kayan aiki da ma'aikatan INEC. An ruwaito cewa, Shettima ya isa mazaɓar tasa tun misalin goma na safe, sai dai ya tarar da tarin layi na masu jefa ƙuri'a suna tsumayin zuwan ma'aikatan zaɓe tare da kayan aiki, duk da cewa an fara kaɗa ƙuri'a a mazaɓu da yawa da ke faɗin garin. Ɗan takarar, wanda ya…
Read More
Sojoji sun bindige ɓarawon akwatin zaɓe a Kogi

Sojoji sun bindige ɓarawon akwatin zaɓe a Kogi

Daag MAHDI M. MUHAMMAD Sojojin Nijeriya sun bindige wani ɓarawon akwatin zaɓe da ba a san ko wane ne ba a hanyar Ogege, sashin zaɓe na Odaba a gundumar Dekina da ke Jihar Kogi. An tattaro cewa, masu kaɗa ƙuri’a a yankin sun tsere daga filin kaɗa ƙuri’a sakamakon ayyukan ’yan bangar siyasa da suka zo da yawa domin lalata kayayyakin zaɓe. ’Yan barandan da suka bayyana ɗauke da adduna da bindigu sun yi awon gaba da akwatunan zaɓe tare da karya kujeru tare da tarwatsa masu kaɗa ƙuri’a. Bayan harin, an soke zaɓen mazaɓu bakwai na mazaɓar Kogi ta…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Atiku ya lashe zaɓe a rumfar Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan a Yobe

Da Ɗumi-ɗumi: Atiku ya lashe zaɓe a rumfar Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, a rumfar da Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya jefa ƙuri'arsa, ya nuna jam'iyyar PDP tare da dan takararta na shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya doke abokin takarar sa a jam'iyyar APC, Bota Ahmed Tinubu, da tazara mai yawa. Rumfar zaɓen wadda take a makarantar Firamaren Katuzu mai lamba 001B, inda sakamakon ya nuna dan takarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na APC ya samu kuri'u 107, yayin da Sanata Rabi'u Kwankwaso na NNPC ya samu ƙuri'u 41, sai Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP mai ƙuri'u 186.…
Read More
Wasu ‘yan takarar siyasar Nijeriya da suka rasa rayukansu gab da zaɓen 2023

Wasu ‘yan takarar siyasar Nijeriya da suka rasa rayukansu gab da zaɓen 2023

Daga AMINA YUSUF Wasu daga cikin waɗannan 'yan takarar ana gab da zaɓen 2023 'yan bindiga suka halaka su, wasu daga ciki kuma suka rasu ta hanyar wasu dalilan. Halin rashin tsaron da ƙasar nan ya yi sanadiyyar kisan ba wai 'yan takarar kaɗai ba har ma da masu tsaron lafiyarsu. Haka ma magoya bayansu sun sha shiga irin wannan ibtila'in a wannan kakar zaɓen. Rahotanni dai suna nuna zargin cewa, waɗannan 'yan siyasa vangaren da suke adawa ne da su suke kashe su saboda suna ganinsu a matsayin barazana ga siyasarsu. Duk kuwa da cewa, a cikin 'yan kwanakin…
Read More
An samu dishashewa a wasu takardun ƙuri’a a Kano

An samu dishashewa a wasu takardun ƙuri’a a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano An samu disashewar Jam'iyyar NNPP a takarar ƙuri'a na mazaɓun Kankarofi da gidan makama da ke cikin birnin Kano, Jami'in sa-ido na jam'iyyu, Mukhtar Ishak Dogarai, ya ce "babbar matsalar da muka fara fuskanta ita ce tambari (Logo) na Jam'iyyar NNPP inda ya gita dishi-dishi akwai sunan kowace jam'iyya amma babu na NNPP, kuma logon ma ya fita dishishi." Ya ci gaba da cewa, "inda muke ɗauko kayan zaɓen nan, wato SAS, akwai abin da babu musamman a zaɓen shugaban ƙasa yanzu haka akwai akwatu 14 waɗanda ballot paper ɗin su ba ta cika ba…
Read More
Na’urar BAVS za ta taimaka wajen hana maguɗin zaɓe – Gaduje

Na’urar BAVS za ta taimaka wajen hana maguɗin zaɓe – Gaduje

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya bayyana cewa, samar da na'urar zaɓe ta BVAS da hukumar zaɓe ta yi a wannan karo zai taimaka matuƙa wajen rage maguɗin zaɓe. Ganduje ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri'arsa a mazaɓarsa da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar kano. Dokta Ganduje ya ƙara da cewa, tun daga malaman zaɓen da jami'an tsaro kowa yana ƙoƙarinsa wajen gudanar da aikinsu a wannan zaɓe. Yayin da ake tantance Gwamna Ganduje "Cigaba da aka samu a zaɓen nan shi ne amfani da na'urar zaɓe, kuma…
Read More
El-Rufa’i ya koka da yadda talakawa suka ƙi fitowa zaɓe a Kaduna

El-Rufa’i ya koka da yadda talakawa suka ƙi fitowa zaɓe a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Kaduna Bayan shafe sama da sa'o'i biyar akan layin kaɗa ƙuri'a a mazaɓarsa, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya jefa ƙuri'arsa, inda ya bayyana damuwarsa kan rashin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar. Da yake jawabi a wata hira da manema labarai a lokacin da yake jiran kaɗa ƙuri’arsa a mazaɓar PU 024 da ke Unguwan Sarki Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, gwamnan ya yi kira ga jama’a da su fito su kaɗa ƙuri’a. Ya yabawa INEC kan inganta harkokin zaɓe, yana…
Read More
Masu kaɗa ƙuri’a sun koka da yadda aka warwatsa rumfunan zaɓe

Masu kaɗa ƙuri’a sun koka da yadda aka warwatsa rumfunan zaɓe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Masu kaɗa ƙuri’a a yau Asabar sun koka da warwatsa rumfunan zaɓe wuri-wuri da aka yi musu na kaɗa ƙuri’a tare da bayyana lamarin a matsayin abin takaici. An samu rabe-raben rumfunan zaɓe a wasu wuraren zaɓe, amma wataƙila hukumar INEC na ganin hakan zai kawo sauƙi ga masu kaɗa ƙuri'a ne. Wakilinmu wanda ya sa ido a kan zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a Jahi 1 da Jahi 2 a Ƙaramar Hukumar Abuja (AMAC), ya bayyana cewa masu kaɗa ƙuri’a da suka yi rajista a makarantar firamare ta Jahi…
Read More