Editor

9513 Posts
Nijeriya ta gurfanar da Shugaban Kamfanin Binance a kotu

Nijeriya ta gurfanar da Shugaban Kamfanin Binance a kotu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta gurfanar da kamfanin Binance Holdings Limited da manyan jami’anta biyu, Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla da ya gudu a gaban kotu bisa zargin ƙin biyan haraji. An gurfanar da kamfanin da shugabannin biyu a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja. Ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhumar Tigran Gambaryan ya isa kotun ne da misalin qarfe 9:15 na safiyar ranar Alhamis yayin da abokin aikinsa, Anjarwalla ba ya nan saboda an ce yana gudu. Waɗanda ake tuhumar dai suna fuskantar tuhume-tuhume biyar na halasta kuɗaɗen haram, da…
Read More
Zargin Dakatarwa: Magaji ya ɗaukaka kara kan hukuncin CCT

Zargin Dakatarwa: Magaji ya ɗaukaka kara kan hukuncin CCT

Daga BASHIR ISAH Shugaban Hukumar Sauraren Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Rashawa na Jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji, ya ɗaukaka ƙara bayan da Kotun Ɗa'ar Ma'aikata (CCT) ta dakatar da shi. Kwamitin alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Danladi Umar a Abuja, shi ne ya ba da umarnin dakatar da Magaji biyo bayan zargin rashin ɗa'a daga Hukumar Ɗa'ar Ma'aikata (CCB). Sa'ilin da yake yanke karanto hukuncin, Alƙali Umar ya yi watsi da ƙarar Magaji inda ya ce kotun na da hurimin sauraren shari'ar. Haka nan, ya unarci Gwamnan Kano, Abba Yusuf da Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) da su naɗa jami'in…
Read More
Yaƙi da dabanci: Duk yaron da aka gani da makami a halbe shi — Gwamnatin Neja ga jami’an tsaro

Yaƙi da dabanci: Duk yaron da aka gani da makami a halbe shi — Gwamnatin Neja ga jami’an tsaro

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Neja ƙarƙashin jagorancin Umaru Mohammed Bago, ta bai wa jami'an tsaro umarnin halbin duk wani tsageran da ya fito da makami da sunan daba ko hana al'umma sukuni a sassan jihar. Shugaban Ƙaramar Hukumar Chanchaga, Hon. Aminu Ladan, shi ne ya faɗi haka bayan taron masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar wanda aka yi a fadar Mai Martaba Sarkin Minna, Dokta Umar Faruk Bahago a yammacin ranar Asabar. Shafin Tsalle Ɗaya mai bibiyar harkokin gwamnatin jihar ya rawaito Aminu Ladan ya ce, Gwamnan ya bada damar jami'an tsaro su yi amfani da bindiga a…
Read More
Burinmu shi ne haɗa kan ƙasashen ECOWAS – Barau Jibril

Burinmu shi ne haɗa kan ƙasashen ECOWAS – Barau Jibril

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mataimakin shugaban amajalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce suna da ƙuduri na ganin sun haɗa kan ƙungiyar ECOWAS. Ya ce, “Kafin zuwan Turawa, ƙasashen Afirka ta Yamma ko ECOWAS sun kasance ƙasa ɗaya. Ana yin Hausa a kowane yanki ka je kama daga Nijar, Mali, Ghana da sauransu haka ma ga duka sauran yaruka”. Barau ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da BBC, inda ya ce ya zama wajibi ECOWAS ta haɗa kai domin samun ci gaban da ya kamata. “Bayan zuwan Turawa ne suka raba kawunanmu, kuma ya kamata mu haɗa kai yanzu,”…
Read More
’Yan Sanda sun kashe ɓarayin daji biyar, sun kuɓutar da mutum 100 da aka yi garkuwa da su a Katsina

’Yan Sanda sun kashe ɓarayin daji biyar, sun kuɓutar da mutum 100 da aka yi garkuwa da su a Katsina

Daga BASHIR ISAH Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Katsina ta bayyana cewa, ta samu nasarar ganin bayan wasu ’yan fashin daji su biyar sannan ta kuɓutar da sama da mutum 100 kanata ƙwato dabbobi 658 da aka sace a jihar duk a cikin watan Maris da ya gabata. Rundunar ta ce a cikin watan Maris ɗin da ya gabata, ta samu rahoto daban-daban har guda 51 a kan aikata manyan laifuka da suka haɗa da garkuwa da mutane, fashi da makami, satar shanu, kisan kai da dai sauransu. Ta ƙara da cewa, ta samu tura kes 30 zuwa kotu daga…
Read More
Manyan ɓarayi ma ba za su tsira ba a hannunmu – EFCC

Manyan ɓarayi ma ba za su tsira ba a hannunmu – EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC ya tabbatar da cewa ba za su bar manyan ɓarayi ba a yaqin da suke yi da masu alaqa da cin hanci da rashawa a ƙasar. Mista Ola Olukoyede ya ce ba za su bar kowa ba a aikin da suke yi. Ya ce a daidai lokacin da suke bin manyan varayi, za kuma su ci gaba da bin sawun ƙananan ɓarayi. Ya ce aikin da EFCC take yi zai ci gaba da karaɗe ko'ina, da kuma kan kowa da kowa ba tare…
Read More
Masu hannu da shuni su rinƙa tallafa wa mabuƙata a Ramadan – Sarkin Hausawan Amuwo Odofin

Masu hannu da shuni su rinƙa tallafa wa mabuƙata a Ramadan – Sarkin Hausawan Amuwo Odofin

Daga DAUDA USMAN a Legas An shawarci masu kuɗi da sauran attajiran ƙasar nan da su ci gaba da taimakon talakawa marasa shi da gajiyayyu da sauran makamantansu. Mai martaba Sarkin Hausawan Ƙaramar Hukumar Amuwo Odofin dake cikin jihar Legas Alhaji Adamu Aliyu ɗan asalin jihar Jigawa mazaunin Legas, ya nemi hakan a lokacin gudanar da wa'azin watan Ramadan na karshen makon jiya. Taron gudanar da wa'azin wanda ya gudana a harabar Qaramar Hukumar Amuwo Odofin dake cikin garin Legas wanda ya ƙunshi malamai da waɗansu daga cikin sarakunan Hausawa al'ummar Musulmi mazauna unguwarni daban-daban na yankin Qaramar Hukumar Amuwo…
Read More
Boko Haram ta kashe sojoji shida a Borno

Boko Haram ta kashe sojoji shida a Borno

Daga BASHIR ISAH Aƙalla sojojin Nijeriya shida sun riga mu gidan gaskiya sakamakon kwanton-ɓaunan da mayaƙan Boko Haram suka yi musu a hanyar Biu-Buni Yadi a Jihar Borno. Majiyarmu ta ce lamarin ya auku ne a ƙauyen Kamuya da ke kusa da Buratai, mahaifar tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Lt. Gen Tukur Buratai (mai murabus). Majiya ta kusa da rundunar tsaro ta ce, jami'an sun cimma ajali ne a kan hanyarsi ta zuwa Damaturu don shan mai. “Abin baƙin ciki ne ainun, sojojin runduna ta 135 Special Force BN FOB ne da ke Buratai. An yi musu kwanton-ɓauna ne a…
Read More
‘A Legas Tinubu zai yi Ƙaramar Sallah’ – Fadar Shugaban Ƙasa

‘A Legas Tinubu zai yi Ƙaramar Sallah’ – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH A wannan Lahadin ake sa ran Shuganq Ƙasa Bola Tinubu zai bar birnin tarayya Abuja zuwa Legas gabanin bikin Ƙaramar Sallah na bana. Kakakin Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken 'Shugaba Tinubu zai Idil Fiɗr a Legas' wadda ya fitar a ranar Asabar. A cewar Ngelale, “Yayin bikin wanda ke nuni da ƙarewar watan Ramadan, Shugaban zai yi wa Nijeriya addu'o'i tare da ahalinsa." Sai dai sanarwar ba ta fayyace ranar Tinubun zai koma Abuja ba, amma cewa Shugaban zai ci gaba da gudanar harkokinsa lokacin hutun bikin sallar…
Read More
Ƙarin kuɗin wutar lantarki dakushe tattalin arzikin ƙasa ne – Atiku

Ƙarin kuɗin wutar lantarki dakushe tattalin arzikin ƙasa ne – Atiku

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na babbar jam'iyyar hamayya, PDPD, Alhaji Atiku Abubakar, ya shiga sahun 'yan Nijeriya da ke ci gaba da sukar matakin ƙarin kuɗin wutar lantarki da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka. Atiku ya ce, ya yi amannar wannar ƙarin kuɗin wutar babu abin da zai tsinana in ba da ƙara dakusar da tattalin arzikin ƙasar nan tare da ƙara tsananta wa 'yan ƙasa tsadar rayuwa. Kwanan nan aka ji Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta sanar da ƙarin wuta amma a kan masu amfani da lantarkin na rukunin farko, 'Band A', a…
Read More