Editor

9513 Posts
Gwamna Namadi ya dakatar da kwamishinansa kan zargin almundahana

Gwamna Namadi ya dakatar da kwamishinansa kan zargin almundahana

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Gwamna Jihar Jigawa Umar Namadi, ya dakatar da Kwamishinan Harkokin Kasuwanci na Jihar, Hon Aminu Kanta, bisa zargin karkatar da kuɗaɗen jama'a. Ana zargin Aminu Kanta da wawushe kuɗaɗen da gwamnatin jihar ta ware domin tallafa wa al'ummar Ƙaramar Hukumar Ɓabura da abinci a lokacin azumin watan Ramadan. Bayanin dakatarwar na ƙunshene a cikin wata takardar sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Alhaji Bala Ibrahim Mamsa wadda aka raba wa manema labarai. Sanarwar ta ce gwamnatin Jihar ta dakatar da Aminu Kanta daga muƙaminsa na Kwamashinan Harkokin Kasuwancin Jihar Jigawa…
Read More
Ci gaba da ba da tallafin wutar lantarki na kashi 85 na nuni da gwamnatin Tinubu ta al’umma ce –Idris

Ci gaba da ba da tallafin wutar lantarki na kashi 85 na nuni da gwamnatin Tinubu ta al’umma ce –Idris

Daga BASHIR ISAH Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, ci gaba da ba da tallafin lantarki da kashi 85 da Gwamnatin Tarayya ke yi hakan ya ƙara tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta al'umma ce. Ministan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a lokacin da yake yi wa 'yan jarida jawabi a Abuja. Ta bakinsa, “Kwanaki kaɗan da suka gabata Gwamnatin Tarayya ta bayyana sabon tsarinta don cigaban fannin lantarki mai ƙudurin samar da wadatacciyar wutar lantarki a faɗin ƙasa. "Ɓangare mafi muhimmanci a tsarin shi ne, gwamnatin Tinubu za ta ci…
Read More
Gwamna Abba Kabir ya biya wa ɗalibai 6,500 kuɗin JAMB ‘yan asalin Jihar Kano

Gwamna Abba Kabir ya biya wa ɗalibai 6,500 kuɗin JAMB ‘yan asalin Jihar Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya biya wa ɗalibai maza da mata da suka gama sakandire 'yan asalin Jihar Kano kuɗin jarrabawar share fagen shiga jami'a kimanin 6,500 don ci gaba da karatun su a kwalejoji da jami'o'i a ƙasar nan dama duniya gaba ɗaya. Gwamnan wanda ya fara da godiya ga iyayen yara bisa jajircewarsu wajen bai wa yaransu tarbiyya da tsayawa don ci gaban su ta hanyar ilimi. Maigirma Gwamna ya ce daga lokacin da aka zaɓi wannan gwamnati sun gudanar da ayyuka da dama ya zuwa yanzu, inda ya ce…
Read More
PSG ta kai wasan ƙarshe a gasar kofin Faransa

PSG ta kai wasan ƙarshe a gasar kofin Faransa

Daga MAHDI M. MUH'D Ƙungiyar ƙwallon koafa ta PSG ta samu kaiwa wasan ƙarshe na kofin Faransa wato French Cup bayan ƙwallon ɗaya tilo da Kylian Mbappe ya zura a ragar Rennes daren ranar Laraba a wasan daf da na ƙarshe da suka doka tsakaninsu. A minti na 40 daf da tafiya hutun rabin lokaci ne Mbappe ya zura ƙwallon bayan tun farko mai tsaron ragar Rennes Steve Mandanda ya varar da fenaritin da tauraron na Faransa ya buga a minti na 33. Mbappe wanda ke matsayin mafi zurawa PSG ƙwallo na taka leda ne a kakarsa ta ƙarshe a…
Read More
An kama matashi kan zargin kashe yayansa a Bauchi

An kama matashi kan zargin kashe yayansa a Bauchi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sanda jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Isyaku Babale, bisa zargin daɓa wa yayansa wuƙa har lahira. Wata sanarwa da mai magana da yawun 'yan sandan jihar SP Ahmed Wakili ya fitar, ta ce binciken farko da suka gudanar, ya nuna cewa wanda ake zargin ya yi amfani da wuƙa wajen daɓa wa babban wansa mai suna Abubakar Ɓalewa ranar Lahadi, 31 ga watan Maris bayan cacar-baki da ta ɓarke tsakaninsu. Wakili ya ce bayan samun rahoton abin da ya faru ne, sai suka tura jami’ansu zuwa wurin, abin da…
Read More
Hajjin 2024: Gwamnatin Kebbi ta fitar da Naira biliyan 3.34 don tallafa wa maniyyatan jihar 3,344

Hajjin 2024: Gwamnatin Kebbi ta fitar da Naira biliyan 3.34 don tallafa wa maniyyatan jihar 3,344

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin jihar Kebbi ta ce ta amince da bayar da tallafin Naira biliyan 3.34 ga maniyyata 3,344 da ke son zuwa aikin Hajjin bana daga jihar. MANHAJA ta rawaito cewa an fitar da kuɗin ne don kammala biyan ƙarin kuɗin aikin Hajjin bana da ya kai kimanin Naira miliyan 1.9 da hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON ta sanar. An cimma wannan matsayar ne a wani taron gaggawa na Majalisar Zartaswa da Mataimakin Gwamna, Umar Abubakar Tafida ya jagoranta, a Birnin Kebbi a ranar Litinin. Da ya ke jawabi ga manema labarai kan sakamakon taron,…
Read More
An kama mai sayar da yalo kan zargin yi wa yaro fyaɗe a Bauchi

An kama mai sayar da yalo kan zargin yi wa yaro fyaɗe a Bauchi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami'an 'yan sandan jihar Bauchi da ke aiki ƙarƙashin rundunar maido da zaman lafiya sun kama matashi mai shekara 23 da ake zargin ya yi wa wani yaro ɗan shekara goma fyaɗe. Matashin da ake zargi ya yaudari yaron da naira 30 da alawa inda ya nemi yaron ya raka shi wani kango da ke bayan wani gidan mai a kan titin Kofar Ran domin ya yi bahaya. Sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar ta ce bayan ya yi bahayar ne kuma, matashin ya bukaci yaron da…
Read More
Gwamnati ta ba wa jaruma Rahama Sadau muƙami a kwamitin IDICE

Gwamnati ta ba wa jaruma Rahama Sadau muƙami a kwamitin IDICE

Daga AISHA ASAS Gwamnatin Tarrayya ta ba wa jaruma Rahama Sadau muƙami a sabon kwamiti ƙarƙashin ƙungiyar zuba jari a harkar ƙirƙira da sadarwar zamani, wato IDICE. Kwamitin wanda ya kasance a layi na biyu a muhimmanci kan abinda ya shafi ƙirƙira da fasaha. Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin ne don ƙaddamar da ƙungiyar ta bunƙasa harkokin fasaha da ƙirƙira tare da saka hannun jari. Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jinjina wa wannan mataki na cigaba a Nijeriya. Shirin IDICE haɗaka ce da gwamnati, abokanan cigaban duniya kamar African Development Bank, French Development Agency, da Islamic Development Bank. Burin…
Read More
Yanzu-yanzu: NERC ta ci AEDC tarar N200m kan saɓa dokar sabon farashin wutar lantarki

Yanzu-yanzu: NERC ta ci AEDC tarar N200m kan saɓa dokar sabon farashin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC), ta ci kamfanin raba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution Plc, (AEDC), tarar Naira miliyan 200 saboda saɓa dokar sabon farashin wutar lantarki. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da NERC ta wallafa a shafinta na X a ranar Juma'a. A cewar NERC, an ci AEDC tara ne saboda ƙin yin aiki da ƙa'idojin sabon farashin wutar lantarki wanda hakan ya haifar da ruɗani a tsakanin kostomomi da masu ruwa da tsaki a masana'antar lantarki. Ta ƙara da cewa, ta ɗauki wannan mataki ne biyo bayan bibiyar da…
Read More
Hajjin 2024: Gwamnan Jigawa ya bada tallafin Naira miliyan ɗaya ga kowane maniyyacin jihar

Hajjin 2024: Gwamnan Jigawa ya bada tallafin Naira miliyan ɗaya ga kowane maniyyacin jihar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan ɗaya ga maniyyata aikin Hajji daga jihar. Kakakin hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Jigawa Murtala Usman ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Litinin. Usman ya ce an bayar da tallafin ne ga maniyyatan Jigawa da suka fara ajiyar kuɗaɗen aikin Hajjin su na 2024 tun a baya. “Kowane maniyyaci yanzu zai biya cikon Naira 900,000 kawai saɓanin Naira miliyan 1.9 da Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta sanar. “Tun da farko hukumar ta NAHCON ta ware…
Read More