Editor

9513 Posts
Sama da shanu 300 aka sace mana cikin makonni uku a Jihar Filato – Makiyaya

Sama da shanu 300 aka sace mana cikin makonni uku a Jihar Filato – Makiyaya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Makiyaya a Ƙaramar Hukumar Bokkos da ke Jihar Filato, sun koka cewa ɓarayin shanu sun arce musu shanu sama da 390 da kudin su ya kai aƙalla Naira miliyan 300. Makiyayan sun ce an yi awon gaba da shanun a lokacin da suke kiwo a Bot, Faranti, Anguwan Abuja, Makada da Wumat. Manhaja ta buga cewa shugaban ƙungiyar ci gaban Fulani na ‘Gan Allah’ dake qaramar hukumar Bokkos Saleh Adamu ya ce sun kai ƙarar abinda aka yi musu zuwa ga kwamandan sashin ‘Operation Safe Haven’ da ke yankin. “A ranar 4 ga Maris,…
Read More
Falastinawa 32,200 aka kashe a Gaza – Ofishin Jakadancin Falastinu a Nijeriya

Falastinawa 32,200 aka kashe a Gaza – Ofishin Jakadancin Falastinu a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ofishin Jakadancin Falastinu a Nijeriya ya bayyana cewa, a ranar 174 na yaƙin kisan ƙare dangi da ake yi wa al'ummar Palastinu, kimanin Falastinawa 32,200 ne sojojin mamaya na Isra'ila suka kashe. Jakadan Falastinu a Nijeriya, Abu Shawesh ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta ce, "a da Gaza ta kasance kurkuku ga al'ummarta, a yau kuwa ta zamo maƙabarta ga al'ummarta. Maƙabarta ga dubun dubatar mutane kuma maƙabarta ta hana 'yancin ɗan adam." "Babu wata hujja ta cigaba da sayar da makamai ga Isra'ila. A cikin watanni…
Read More
Cibiyar Horti ta horar da masu saida kayan amfanin gona a Kano

Cibiyar Horti ta horar da masu saida kayan amfanin gona a Kano

Daga MAHDI M. MUH’D A ƙoƙarinta na bunƙasa noman kayan lambu, Cibiyar Horti Nijeriya wacce ƙasar Dutch ta ke tallafawa ta horas da masu sayar da kayan amfanin gona a Jihar Kano. Taron bitar ya gudana ne a ranar Larabar da ta gabata, a inda aka zaƙulo ’yan kasuwar a qananan hukumomi daban-daban na Jihar Kano waƙanda suka haƙa da Kumbotso, Rimin Gado, Dawakin Kudu, Dawakin Tofa, Tofa, Garko, Bichi da kuma Minjibir. Wannan horaswa dai wani yunƙuri ne na ƙarfafa noman kayan lambu da kuma ilimantar da kananan masu sayar da kayan amfanin gona. Taro dai ya mayar da…
Read More
Sabuwar manhajar KIPPIS za ta bada cikakkun bayanai akan ma’aikatan Kano – AG Abdulkadir

Sabuwar manhajar KIPPIS za ta bada cikakkun bayanai akan ma’aikatan Kano – AG Abdulkadir

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Akanta Janar na Jihar Kano, Abdulqadir Abdulsalam ya bayyana cewa ƙirƙiro da manhaja KIPPIS da gwamnatin Jihar Kano ta yi zai taimaka wajen samun cikakkun bayanan ma'aikatan jihar. Abdulsalam ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske bayan kammala taron kwana biyu kan yadda sabuwar manhajar tattara bayanai na ma'aikatan Kano da ake kira KIPPIS da aka yi a jihar Kano wanda ya ƙunshi ofishin Akanta Janar da Ofishin kula da ma'aikatan Kano da ofishin binciken kuɗi na Kano da ofishin kula da biyan albashi da gwamnan Jihar…
Read More
Super Eagles ta taki sabon matsayi a jadawalin FIFA

Super Eagles ta taki sabon matsayi a jadawalin FIFA

Daga MAHDI M. MUH'D A yanzu haka tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta taki matsayi na 33 inda ta sha gaban abokiyar hamayyarta ta yammacin Afirka a sabon jadawalin FIFA bayan da ta doke ta da ci 2-1 a wasan sada zumunta da suka yi a watan jiya. Duk da cewa sau biyu tawagar Super Eagles ta Nijeriya tana faɗuwa ƙasa a sabuwar kimar hukumar ta FIFA, amma har yanzu zakarun Afirkan na gaban Ghana da ke yammacin Afirka. Super Eagles dai ta kasance ta 28 a duniya a jadawalin watan Fabrairu amma ta koma mataki na 30 a kimar…
Read More
 Rashin ganin gwamna

 Rashin ganin gwamna

Daga THALITHU ƘOƘI Ni ba na ganin laifin masu ƙorafi a kan rashin samun ganin gwamna ko muƙarrabansa, magana ta gaskiya! Iya ra'ayinsu kenan bisa la'akari da abinda suke tsammani da suka rataya wa kansu da kuma yarjejeniyar zuci da suka ƙulla tsakaninsu da waɗanda suke ganin sun kama madafun iko a yanzu. Kamar ko yaushe, mu riƙa yi wa juna uzuri. Na san mutane da dama a wannan Gwamnatin, sani na kut-da-kut, kuma mun dama sosai kafin a samu Gwamnati da su. Rashin ganinsu, ko rashin jinsu, ko rashin mu'amalantuwa da su a yanzu sam ba ya daga ni ya…
Read More
Wai hukumar Hisba ta yi amfani da ƙarfi!

Wai hukumar Hisba ta yi amfani da ƙarfi!

Daga DAKTA MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI 1) Wannan shi ne mafi girman rainin hankalin da ya jawo wannan babbar matsalar. Wai ana amfani da ƙarfi, kuma wannan maganar ta ruɗi ruɗaɗɗu, har ma da wasu masu hankalin. To yanzu sai ku je ku yi amfani da "banana" da "apple" da "carrot" da "honey" ku hana su, tun da ku 'ya'yan masu amfani da daɗi ne. In ka ce ana amfani da qarfi, to sai ka faɗi yadda za a yi, in ba a yi amfani da ƙarfin ba. 2) Malam Sheikh Daurawa ya faɗa ya nanata cewa mutanen nan da ake ƙoƙarin…
Read More
Jerin wuraren da za a tantace masu neman aikin ɗan sanda

Jerin wuraren da za a tantace masu neman aikin ɗan sanda

Daga BASHIR ISAH Hukumar kula da shirin ɗaukar sabbin jami’an ’yan sanda ta fitar da jerin cibiyoyi guda 20 wanda a nan za a gudanar da shirin tantance masu neman aikin ɗan sanda a faɗin ƙasa. Hukumar Kula da Harkokin ’Yan Sanda (PSC) ce ta kafa wannan hukumar don taimaka mata wajen gudanar da shirin ɗaukar sabbin ƙananan jami’ai da ke gudana. Jaridar Daily Trust ta rawaito Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ‘Yan Sanda, Ikechukwu Ani, ya faɗa cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis cewa, yanzu ana kan matakin tantance lafiyar masu neman shiga aikin…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan daudu, Bobrisky ya faɗa a komar EFCC

Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan daudu, Bobrisky ya faɗa a komar EFCC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da Rashawa ta EFCC, ta tsare ɗan daudun nan, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky, bisa zargin wulaƙanta takardun kuɗi na Naira. Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, shi ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an tsare Bobrisky ne ranar Laraba da misalin ƙarfe 3 na rana a rukunin gidaje na Pinnock Estate da ke Legas bisa zargin watsa takardun Naira a wajen taro wanda hakan cin mutuncin kuɗin ƙasa ne
Read More
Mun haramta shirya fina-finan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu a Kano — El-mustapha

Mun haramta shirya fina-finan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu a Kano — El-mustapha

Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano ta ce dag yanzu ta haramta shirya fina-finai masu nuna faɗan 'yan daba da harkokin 'yan daudu a jihar. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Jami'in Yaɗa Labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman da kuma kwanan wata 3 ga Afrilun da ake ciki. Sanarwar ta ce: "Biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da al'umma ke yi a kan shirya fina-finan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu a jihar Kano, Shugaban Hukumar tace fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano, Abba El-mustapha, ya bada umarnin dakatarwa tare…
Read More