04
Apr
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Fitaccen marubucin littattafan Hausa da finafinan Kannywood, Malam Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi sani da ANKA ya zama shugaban ƙungiyar Hausa ta Jami'ar Bayero da ke Kano, a wani zaɓe da ƙungiyar ta gudanar ranar Jumma'ar da ta gabata 22 ga watan Maris, 2024 a zangon karatu na 2022/2023. Marubucin wanda yake ɗalibta a Sashin Nazarin Harsunan Najeriya, inda yake karatun digirinsa na farko a fannin Harshen Hausa, ya zama shugaban ƙungiyar ne bayan zaven da aka yi masa tare da wasu masu dafa masa su goma sha ɗaya. Da suka haɗa da shi, Kabiru…
