Editor

9513 Posts
Ko kun san tarihin fadar Aso Rock Villa?

Ko kun san tarihin fadar Aso Rock Villa?

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Fadar Gwamnatin Tarayya wadda ake kira State House a Turance. Wannan fada, ayari ne na ofisoshi da suka haɗa da Fadar Shugaban Ƙasa wadda ake kira Presidential Villa a Turance; ofishin mataimakin shugaban ƙasa, da sauransu. Haka nan kuma a cikin fadar ta shugaban ƙasa akwai ma’aikatan da suke gudanar da ayyukan da suka shafi ayyukan gudanarwa, tsare-tsare bisa ƙa’ida, harkar tsaron lafiyar shugaban ƙasa da fadar tasa da kuma harkokin yaɗa labarai, waɗanda dukkan su suke ƙarƙashin kulawar shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin Tarayya, wato Chief of Staff kenan, muƙamin da a yanzu haka (2024), Femi…
Read More
Da Ɗumi:ɗumi: An rantsar da Bassirou Faye a matsayin sabon Shugaban Ƙasar Senegal

Da Ɗumi:ɗumi: An rantsar da Bassirou Faye a matsayin sabon Shugaban Ƙasar Senegal

*Ya zama Shugaban Ƙasa mafi ƙarancin shekaru a Afirka Daga BASHIR ISAH An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa don ci gaba da jan ragamar mulkin ƙasar. Da wannan Faye mai shekara 44, ya zama shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a nahiyar Afirka. Bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe babban zaɓen ƙasar, Faye ya sha alwashin yin sauye-sauye da dama a ɓangarori daban-daban na ƙasar. An rantsar da Faye ne a ranar Talata a birnin Diamniadio da ke kusa da Dakar babban birnin ƙasar.
Read More
Ba mu ci bashin N14.26bn ba — Gwamnatin Zamfara

Ba mu ci bashin N14.26bn ba — Gwamnatin Zamfara

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Dauda Lawal ta bayyana cewa, ba ta ci bashin Naira biliyan 14.26 ba, amma cewa abin da ake gani yanzu ɓangare ne na bashin biliyan N20 da gwamnatin da ta gabata ta ranto. Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya faɗa a sanar da ya fitar cewa babu wani bashi da jihar ta ci, a gida ko ƙetate, tun bayan da Gwamna Dauda Lawal ya karɓi ragamar mulkin jihar. Ya ce, “Za mu so mu yi ƙarin haske kan rahoton Ofishin Kula da Bashi (DMO), Jihar Zamfara ba ta ci bashin biliyan…
Read More
‘Yan bindiga sun sace wasu ɗalibai a Delta

‘Yan bindiga sun sace wasu ɗalibai a Delta

Daga BASHIR ISAH Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu ɗalibai da ba a san adadinsu ba a Jihar Delta. Lamarin ya faru ne a ranar Litini a lokacin da ɗaliban ke kan hanyarsu ta tafiya a yankin Ughelli da ke jihar. Duk da dai babu wani cikakken bayani kan batu, sai dai Kakakin 'yan sandan jihar, Bright Edafe, ya ce jami'an tsaro sun samu lamrin aukuwar lamarin. Jami'in ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Rundunar 'yan sanda jihar ta samu labarin aukuwar wannan mummunan al'amari, kuma muna bakin ƙoƙarinmu don kuɓutar da…
Read More
An kashe malamin Jami’ar Maiduguri ta hanyar daɓa masa wuƙa

An kashe malamin Jami’ar Maiduguri ta hanyar daɓa masa wuƙa

Daga BASHIR ISAH Lamarin ya auku ne a ranar Lahadin da ta gabata inda aka bi Dokta Kamar Abdulkadir har cikin ofishinsa aka daɓa masa wuƙa wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa. Marigayin na malanta ne a Sashen Physical Health Education na jami'ar, kuma shi ne Jami'in Kula da Jarrabawa na tsangayarsu. Mai magana da yawun jami'ar, Farfesa Danjuma Gambo, ya tabbatar wa da Jaridar News Point Nigeria da faruwar lamarin. Inda ya ce, da yammacin ranar Lahadi ne aka kashe malamin. Ya ƙara da cewa, duk dai ba a kai ga tsare kowa ba kan batun, amma 'yan sanda…
Read More
Ma’aikatar jinƙai: An karkatar da N1.4bn tsakanin zamanin Sadiya da Edu – Bincike

Ma’aikatar jinƙai: An karkatar da N1.4bn tsakanin zamanin Sadiya da Edu – Bincike

Daga BASHIR ISAH Sakamakon binciken Jaridar Premium Times ya nuna cewa, Ma’aikatar Jinƙai da Bunƙasa Walwala ta karkatar da kuɗaɗe sama da Naira biliyan 1.4 zuwa asusun wasu ma’aikata su takwas a ma’akatar a cikin sama da shekaru huɗu. Bayanan da aka tattaro sun fallasa yadda aka yi ta hada-hadar kuɗi ta haramtacciyar hanya a ma’aikatar a zamanin shugabancin Sadiya Farouq da Betta Edu waɗanda a yanzu suke fuskantar bincike daga hukumar EFCC bisa zargin almundahana. Idan za a iya tunawa, a lokutan baya-bayan nan ne Shugaban Bola Tinubu ya dakatar da Betta Edu bayan da ta ba da damar…
Read More
Yadda labaran ƙarya suka kusa kashe min aure – Lai Mohammed

Yadda labaran ƙarya suka kusa kashe min aure – Lai Mohammed

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Lai Mohammed, ya bayyana yadda labaran ƙarya a shafukan sada zumunta suka kusan raba shi da matarsa da suka shafe sama shekara 40 suna tare. Tsohon ministan ya bayyana hakan ne a Legas a wani taron tunawa da cika shekaru 90 na wanda ya tava lashe kyautar rubuta a fannin adabi a Afirka, Farfesa Wole Soyinka. Mista Mohammed, abokin tafiyar da kamfanin Bruit Costard, mai fafutuka kuma kamfanin hulɗa da jama’a, ya tuna cewa ɗaya daga cikin ƙalubalen da ya fuskanta a ofis a matsayinsa na minista shi…
Read More
Tattalin arziki: Tinubu ya fara haifar da ɗa mai ido – Ministan Labarai

Tattalin arziki: Tinubu ya fara haifar da ɗa mai ido – Ministan Labarai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta sun fara samar da ɗa mai ido. Ya bayar da misali da cigaba aka samu a cikin 'yan kwanakin nan. Ministan ya yi wannan jawabi ne a wajen babban taron ƙoli na masu magana da yawun hukumomi, wanda Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) ta shirya a Abuja. Ya ce, “Abin farin ciki ne a lura da cewa sauye-sauyen tattalin arziki da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na samun ƙarin…
Read More
Gargaɗin NDLEA kan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

Gargaɗin NDLEA kan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

A baya-bayan nan Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Muggan Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Mohamed Buba Marwa, ya ce, a cikin watanni 22 hukumar ta kama fiye da ƙwayoyin tramadol miliyan 100 na haramtacciyar hanya da sauran muggan ƙwayoyi masu cutarwa. Yawan shan waɗannan ƙwayoyi na varna da rayuwar al'umma musamman matasa, wanda ake saran al’umma za su fahimci ɓarnar da matsalar ke haifarwa. Shugaban NDLEA, wanda ya bayyana hakan a yayin bikin bayar da lambar yabo da kuma ƙawata sabbin jami’an da aka ƙara wa girma a Abuja, ya ce, “A cikin qanqanin lokaci, hukumar ta kama masu…
Read More
‘Ba ka da ƙwarewa, sai tarin hadimai mara kan-gado’ — martanin ɗan gidan El-Rufa’i ga Gwamnan Kaduna

‘Ba ka da ƙwarewa, sai tarin hadimai mara kan-gado’ — martanin ɗan gidan El-Rufa’i ga Gwamnan Kaduna

Daga BASHIR ISAH A wani yanayi mai kama da martani, ɗan gidan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Bashir El-Rufai, ya zargi Gwamnan Kaduna, Uba Sani, da rashin zama a jiharsa don yi talakawansa aiki sannan ya koma ya tare a Abuja. Haka nan, ya zargi Gwamna Sani wanda aboki ne ga mahaifinsa, da cewa ya tara hadimai mara kan-gado waɗanda ba su da ƙwarewa balle kuma su suka shi a hanya. Ya ci gaba da cewa, maimakon Gwamnan Kaduna ya yarda da rashin ƙwarewarsa, amma ya ɓuge da yin ƙorafi kan cewa ya gaji tulin bashi daga gwamnatin El-Rufai. Tun da…
Read More