31
Mar
Daga BASHIR ISAH Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya bayyana cewa, ya gaji ɗimbin basussuka daga gwamnatin da ya gada, lamarin da ya ce taliƙe kaso mai tsoka daga kason wata-wata da jihar ke samu a wajen Gwamnatin Tarayya. Basussukan da ya ce ya gada faga gwamnatin Nasir El-Rufai sun haɗa da Dala Miliyan 587 da Naira Biliyan 85 sai kuma kwangiloli guda 115. Gwamna Sani ya bayyana haka ne a wajen taron jin ra'ayoyin jama'ar gari dangane da shugabancinsa da aka shirya ranar Asabar. Ya ce, ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen yin amfani da ɗan…
