Editor

9513 Posts
Diawara ya soke kwataraginsa da Faransa bayan haramta wa ’yan wasa yin azumi

Diawara ya soke kwataraginsa da Faransa bayan haramta wa ’yan wasa yin azumi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Ƙwallon Ƙafar Ƙasar Faransa ta gayyaci Dehmaine Tabibou Assoumani na ƙungiyar Nantes a matsayin wanda zai maye gurbin ɗan wasan tsakiyar tawagar ’yan ƙasa da shekara 19 ta ƙasar. Ɗan wasan tsakiyar Mahamadou Diawara ya yanke shawarar barin tawagar ne bayan da hukumar ƙawallon ƙafa ta ƙasar ta kafa wasu sabbin dokoki waɗanda suka haramtawa 'yan wasa Musulmi yin azumin watan Ramadan a lokacin da suke atisaye. Diawara bai ji dadin sabbin dokokin ba, waɗanda aka fara aiwatar da su tun daga matakin tawagar ’yan qasa da shekaru 16 har zuwa babbar tawagar ƙasar. Wannan…
Read More
Yadda aka sace wani limami a Jihar Kogi

Yadda aka sace wani limami a Jihar Kogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace babban limamin yankin Iyara da ke Ƙaramar Hukumar Jimu a Jihar Kogi, Sheikh Quasim Musa. ’Yan bindigar sun kai farmaki gidan malamin ne a ranar Litinin 25 ga Maris, 2024, inda suka yi awon gaban da shi kuma har yanzu babu amo ballantana labarinsa. Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun fara harbe-harbe, jim kaɗan da isa gidansa da ƙarfe 10 na daren ranar Litinin. Jami’in hulɗa da jama’a a ƙungiyar ci gaban Iyara, Mista E.K. Adebayo ya ce ’yan bindigar sun…
Read More
Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka ta maka shugaban MTN a kotu

Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka ta maka shugaban MTN a kotu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka ta Nijeriya, NCC, ta gurfanar da Kamfanin Sadarwar MTN da wasu mutane huɗu a gaban kotu bisa zarginsu da keta haƙƙin mallaka. An shigar da aarar mai lamba FHC/ABJ/CR/111/2024 a babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Litinin. Sauran mutane huɗu da ake tuhuma a shari’ar su ne; Karl Toriola, shugaban MTN na Nijeriya, Nkeakam Abhulimen da Yahaya Maibe. A cikin tuhume-tuhume uku, NCC ta yi zargin cewa waɗanda ake tuhumar, a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2017, “sun amfani da fasahar da ba tasu ba”, sun keta ayyukan waƙa na wani mawaƙi,…
Read More
Harin Mairuwa: Gwamnan Raɗɗa zai tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa

Harin Mairuwa: Gwamnan Raɗɗa zai tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa na jihar Katsina ya yi Allah wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai a garin Mairuwa da ke Ƙaramar Hukumar Faskari a jihar, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin tausayi. Harin wanda ya afku a yammacin ranar Asabar ɗin da ta gabata a lokacin sallar magariba a watan Ramadan da muke ciki, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu biyu. Gwamna Raɗɗa, ta bakin sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari ya yi Allah wadai da harin tare da jajantawa. Ya kuma yi…
Read More
Gwamna Inuwa ya ƙaddamar da rabon abinci karo na 17 a Gombe

Gwamna Inuwa ya ƙaddamar da rabon abinci karo na 17 a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya kaddamar da rabon kayan abinci a karo na 17 ga marasa galihu da nakasassu kimani dubu ɗari biyu da sha huɗu da ɗari biyar. Za a yi rabon kayan abincin ne a rumfunar zaɓe guda dubu 2,218 da ke mazaɓu 114 a faɗin jihar. Gwamnan ya ce, ya fara ba da irin wannan tallafin ne tun a zangonsa na farko, inda ya raba sau 15. Ya ce a yanzu bayan dawowarsa wannan shi ne karo na biyu kuma jimilla na 17 idan an haɗa da wanda…
Read More
Abinda ya sa ba a cika satar ɗalibai ba a Borno — Zulum

Abinda ya sa ba a cika satar ɗalibai ba a Borno — Zulum

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana riko da tsarin nan na “safe school initiative” a matsayin sirrin da ya sa ba cika samun labarin satar ‘yan makaranta ba a jihar. Tsarin na “safe school initiative” dai wani shiri ne da ya wajabta gina katanga da ɗaukar ma’aikata masu ɗauke da makamai domin kare lafiya da dukiya a makarantu. Zulum ya bayyana ne Fadar Gwamnatin Nijeriya jim kaɗan bayan fitowarsa daga wani taro na shuwagabanni a ƙasar nan. Zulum ya ce “Mun kai akƙalla shekara bakwai zuwa takwas da ƙaddamar da tsarin…
Read More
Yadda gayyatar da jami’an tsaro suka yi min ta gudana — Sheikh Gumi

Yadda gayyatar da jami’an tsaro suka yi min ta gudana — Sheikh Gumi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shahararren malamin addinin Musluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya bayyana cewa jami’an tsaron Nijeriya sun gayyace shi ya amsa wasu tambayoyi cikin girmamawa. Duk da cewa, Sheikh bai bayyana waɗanne ɓangare na jami’an tsaron ba ne suka gayyace shi, ya tabbatar da cewa an gayyace shi sun tattauna cikin mutunci da sanin ya kamata. A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Ministan Labarai na Nijeriya Mohammed Idris ya bayyana cewa babu wanda ke gaba da doka sai dai wanda bai yi laifi ba. “Gwamnati ba za ta yi…
Read More
Babu batun rage farashin fetur da gas, inji NNPC

Babu batun rage farashin fetur da gas, inji NNPC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPCL, ya musanta rahotannin da ake yaɗawa ya cewa ya rage farashin man fetur da iskar gas. NNPCL ya mayar da martanin ne kan wasu rahotanni da wasu kafafen watsa labaran Nijeriya ke yaɗawa cewar ya rage farashin man fetur da gas. Babban jami'in sadarwa na kamfanin Olufemi Soneye ne ya yi watsi da jita-jitar a wata sanarwar da ya rabawa manema labarai. Ya kuma buƙaci jama'a da su yi watsi da rahotannin. Sanarwar ta ce, "Kamfanin NNPCL na so ya yi wa al'umma ƙarin haske kan wasu rahotannin da ke…
Read More
Duk da taɓarɓarewar tattalin arziki, CBN ya ƙara kuɗin ruwa da kashi 24.75

Duk da taɓarɓarewar tattalin arziki, CBN ya ƙara kuɗin ruwa da kashi 24.75

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya ya ɗaga darajar manufofin hada-hadar kuɗi da aka fi sani da 'kuɗin ruwa' da kashi 200 cikin 100 zuwa kashi 24.75 daga kashi 22.75 cikin 100 a ƙoƙarin da ake na magance hauhawar farashin kayayyaki. Gwamnan babban bankin ƙasar CBN, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wajen taron manema labarai na kwamitin kula da harkokin kuɗi karo na 294 a Abuja. Sabon kuɗin ruwa shi ne  kashi 2% daga kashi 22.75 cikin dari da MPC ta sanar kusan wata daya da ya gabata da kuma hauhawar farashi na biyu…
Read More
Hukumar Zakka da Waƙafi ta karɓi Naira miliyan 12 a matsayin zakka a Katsina

Hukumar Zakka da Waƙafi ta karɓi Naira miliyan 12 a matsayin zakka a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Naira miliyan 12 ne ke a asusun Hukumar Zakka da Waƙafi da mawadata suka bayar a matsayin zakka a jihar Katsina. Shugaban hukumar a jihar Dr Ahmed Musa Filin Samji ya faɗi haka a wata hira da ya yi da manema labarai a Katsina. Ya ce cikin kuɗin Gwamna Dikko Raɗɗa ne ya bada zakka mafi tsoka ta Naira miliyan goma. Dr Ahmed Filin Samji ya kuma bayyana cewa hukumar na nan na tantance waɗanda za su amfana da zakka a cikinsu kamar yadda ya ce sun haɗa da nakasassu da 'yan gudun hijira da…
Read More