Editor

9513 Posts
Kisan Okuama: Basaraken da ake nema ruwa a jallo ya miƙa kansa

Kisan Okuama: Basaraken da ake nema ruwa a jallo ya miƙa kansa

*Sojoji sun tabbatar 'yan sanda sun miƙa shi gare su Daga BASHIR ISAH Rundunar 'Yan Sandan Jihar Delta ta miƙa Basaraken da aka nema ruwa a jallo, Clement Ikolo Ogenerukeywe, ga sojoji. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Bright Edafe, shi ne ya tabbatar da hakan. Ana zargin Sarkin Masarautar Ewu ɗin ne da hannu a kisan sojoji 17 da ya auku kwanan nan a jihar ta Delta. MANHAJA ta naƙalto Ogenerukeywe ya miƙa kansa ne bayan da Babban Ofishin Tsaro ya fitar da sanarwar ya nemansa ruwa a jallo a ranar Alhamis, kamar yadda Kwamishin 'Yan Sandan Jihar,…
Read More
Cikakken bayanin yadda Tinubu ya kafa Majalisar Havaka Tattalin Arzikin Nijeriya

Cikakken bayanin yadda Tinubu ya kafa Majalisar Havaka Tattalin Arzikin Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A wani muhimmin mataki na ƙarfafa tsarin tafiyar da tattalin arzikin qasa da tabbatar da tsayayyen tsare-tsare da aiwatar da tattalin arzikin ƙasa cikin aminci, Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ya kafa Kwamitin Kula da Tattalin Arzikin Ƙasa na Shugaban Ƙasa (PECC) da kuma samar da Ƙungiyar Kula da Tattalin Arziki ta Gaggawa (EET). A cewar wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Ajuri Ngelale, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan kafafen yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, kwamitin kula da tattalin arzikin shugaban ƙasa (PECC) ya ƙunshi fitattun shugabanni…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Tinubu ta ware N90bn don cikata wa maniyyata kuɗin Hajji

Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Tinubu ta ware N90bn don cikata wa maniyyata kuɗin Hajji

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta ware Naira biliyan 90 domin cikata wa maniyyata kuɗin Hajjin Bana. Tallafin na zuwa ne biyo bayan ƙarin kuɗin Hajji da aka yi bayan sama da Naira miliyan huɗu da maniyyatan suka yi da farko. A farkon wannan makon ne Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ba da sanarwar cewa, an yi ƙarin kuɗin Hajjin bana da Naira Miliyan 1.9 wanda kuma ake buƙatar kowane maniyyaci ya biya a cikin ƙankanin lokaci ko kuma ya haƙura da tafiya Hajji bana. Tun bayan sanarwar ƙarin da NAHCON ta yi,…
Read More
Yunwa ta sanya Falasɗinawa fara cin wata ciyawa a matsayin abinci

Yunwa ta sanya Falasɗinawa fara cin wata ciyawa a matsayin abinci

Sakamakon ƙarancin abinci da kuma barazanar ɓarkewar yunwar ga al'ummar Falasɗinawa, hakan ya tilasta wa wasu da dama dafa ganyen wani haki da suke kira da Khubaiza, don ci a matsayin abinci. Wani magidanci Mohammad Shehadeh ya ce, ya na yin kasada da rayuwarsa ne wajen ɗebo ganyen don ciyar da iyalansa da kuma sayarwa a kasuwa. Ita ma Maryam Al-Attar da ta ce sojojin Isra'ila sun tava harbin su ita da mai gidanta a lokacin da su ka je ɗebo ciyawar ta Khubaiza a gabashin Gaza, ta ce lokacin da ƙananan 'ya'yanta suka ce mata suna jin yunwa, hankalinta…
Read More
Zan bayyana makomata bayan gasar kofin Turai – Mbappe

Zan bayyana makomata bayan gasar kofin Turai – Mbappe

Sga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan wasan gaba na PSG Kylian Mbappe ya ce zai bayyana matsayarsa na gaba bayan gasar kofin nahiyar Turai ta 2024. Ɗan wasan na Faransa ya yi magana a karon farko game da raɗe-raɗin da ake yi na yarjejeniyarsa da Real Madrid a bazara. A yayin da yake magana a gidan jaridar Faransa, ya ce “Ban sanar da komai ba saboda babu abin da zan sanar. "Zan bayyana makomata kafin gasar kofin Turai." Dangane da gasar Olympics ta Paris, Mbappe ya ce: “A koyaushe ina da wannan buri, abu ne na musamman kuma a koyaushe ina…
Read More
Jam’iyyun siyasa a Nijeriya ba su da aƙida – Ganduje

Jam’iyyun siyasa a Nijeriya ba su da aƙida – Ganduje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Dr Abdullahi Ganduje, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, ya ce jam’iyyun siyasa a Nijeriya ba su da asali da aƙida, wanda ke haifar da sauya sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa waccan. Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya ƙaddamar da kodinetocin jam’iyyar na shiyyoyi a faɗin ƙasar nan. Ya ce dole ne lamarin ya canza da kyau. Ya ce kodinetocin shiyyar ne za su kula da shiyyoyin siyasa shida na ƙasar nan. Gwamna Ganduje ya naɗa Gwamna Hope Uzodimma na Imo a matsayin kodinetan shiyyar Kudu Maso Gabas, yayin da Gwamna…
Read More
Ko a mayar da ni nan da kwana bakwai ko mu haɗu a kotu – Sanata Ningi ga Majalisa

Ko a mayar da ni nan da kwana bakwai ko mu haɗu a kotu – Sanata Ningi ga Majalisa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Ahmed Ningi, ya rubutawa shugaban majalisar, Godswill Akpabio wasiƙa, yana neman a ɗage dakatarwar da aka yi masa. Ningi, wanda ya rubuta wa Akpabio wasiƙa ta hannun lauyansa, Femi Falana (SAN), ya bayyana cewa idan ba a ɗage dakatarwar da aka yi masa ba nan da kwanaki bakwai masu zuwa zai kai majalisar dattawa gaban babbar kotun tarayya. Majalisar dattawa, a ranar 12 ga watan Maris, ta aika wa Ningi dakatarwar watanni uku saboda iƙirarin da ya yi na cewa an yi cushe a kasafin…
Read More
DHQ na neman Farfesa da wasu mutum 7 ruwa a jallo bisa zargin kashe sojoji a Delta

DHQ na neman Farfesa da wasu mutum 7 ruwa a jallo bisa zargin kashe sojoji a Delta

Daga BASHIR ISAH Babban Ofishin Tsaro (DHQ) da ke Abuja, ya ce yana beman wasu mutum 8, ciki har da Farfesa kan zarginsu da hannu cikin kashe sojoji 17 da aka yi kwanan nan a yankin Okuama, Jihar Delta. A ranar Alhamis Ofishin ya bayyana sunaye da hotunan waɗanda yake farauta ɗin domin jama'a su taimaka da bayanan da za su taimaka a damƙe su. Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da: Alevwru Daniel, Farfesa Ekpokpo Arthur, Andaowe Deniss Bakriri, Igboli Ebi, Akata Malawa David, Sinclear Oliki, Clements Okoli, Oghenerhukehve da kuma Rueben Baru.
Read More
Rashin haɗin kai ne ke hana tasirin marubutan Jihar Sakkwato – Zarah BB

Rashin haɗin kai ne ke hana tasirin marubutan Jihar Sakkwato – Zarah BB

"Rubutu madubi ne da ke haska gobe" Daga AISHA ASAS Jihar Sakkwato na ɗaya daga cikin jihohin da ke ɗauke da kwararrun marubuta duk da cewa ba kasafai ake sanin su ba, wataƙila hakan ba ya rasa nasaba da daidaitacciyar Hausa da suke amfani da ita, wadda ke hana a gane su da Hausa irin ta Sakwatawa, har sai dai idan su ne suka faɗa. A yau shafin adabi ya ɗauko ma ku ɗaya daga cikin jajirtattun marubuta da suka fito daga Birnin Shehu, Fatima Bello Bala, wacce aka fi sani da Zarah BB. Matashiyar marubuciya ce da ke bada…
Read More
Gwamna Lawal ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta hanzarta kammala ayyukan madatsun ruwa a Zamfara

Gwamna Lawal ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta hanzarta kammala ayyukan madatsun ruwa a Zamfara

Daga BASHIR ISAH A matsayin ɓangare na ƙoƙarin da Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ke don wadata jiharsa da tsaftataccen ruwan sha, hakan ya sa Gwamnan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta kammala ayyukan madatsin ruwa da ke gudana a jihar. Lawal ya yi wannan kira ne a ranar Talata sa'ilin da ya ziyarci Ministan Albarkatun Ruwa, Injiniya Fatgesa Joseph Terlumun Utsav. Sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, tattaunawa jagororin ta ta'allaƙa ne kan ayyukan samar da ruwan sha a Zamfara. Suleiman ya ce yayin tattaunawar tasu, Gwamna Lawal ya yi…
Read More