Editor

9513 Posts
Tinubu ya karrama sosjojin da aka kashe da lambar MON

Tinubu ya karrama sosjojin da aka kashe da lambar MON

*Ya ɗauki nauyin karatun 'ya'yansu Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karrama sojoji 17 da aka kashe kwanan nan a Jihar Delta da lambar yabo ta ƙasa (MON). Huɗu daga cikin marigayan aka karrama da lambar MON, yayin da sauran 13 suka samu lambar 'Officers of the Federal Republic'. Haka nan, Tinubu ya sanar da ɗaukar nauyin karatun 'ya'yan marigayan da kuma kyautar muhalli ga iyalansu. Shugaban ya bayyana haka ne yayin jana'izar marigayan wadda aka gudanar a ma koabartar sojoji da ke Abuja. Sojojin sun cimma ajali ne ranar 14 ga Maris a hannu ɓata-garin yankunan Okuama…
Read More
Abure ya zama Shugaban Jam’iyyar Labour na Ƙasa karo na biyu

Abure ya zama Shugaban Jam’iyyar Labour na Ƙasa karo na biyu

Daga BASHIR ISAH An sake zaɓan Mr Julius Abure, a matsayin Shugaban Jam'iyyar Labour na ƙasa karo na biyu. Daliget ne suka sake bai wa Abure wannan dama ba tare da hamayya ba. An zaɓe shi ne duk da hamayya daga ɓangaren Jam'iyyar NLC. Shugaban babban taron jam'iyyar kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Abia, Mr Ikechukwu Emetu, shi ne ya ayyana Abure a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugabancin jam'iyyar wanda ya gudana ranar Laraba a Nnewi, Jihar Anambra. Kafin wannan lokacin, an kai ruwa rana tsakanin Abure da NLC ƙarƙashin jagorancin leadership Joe Ajaero. Inda NLC ta buƙaci Abure ya…
Read More
Yanzu-yanzu: Gwamnati ta sanar da ranar hutun Easter

Yanzu-yanzu: Gwamnati ta sanar da ranar hutun Easter

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar 29 ga Maris da 1 ga Afrilu a matsayin ranakun hutun bukukuwan Good Friday da Easter Monday na bana. Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya bayyana haka a madadin Gwamnatin Tarayya a ranar Laraba. Ya bayyana hakan ne a ciki wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babbar Sakatariyar Ma'aikatar, Aishetu Ndayako. Tunji-ojo ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga mabiya addinin Kirista da ma 'yan ƙasa baki ɗaya kan a yi koyi da karantarwa Yesu kamar yadda ya nunar a halin rayuwarsa.
Read More
Sojoji sun ga bayan Dogo Gide

Sojoji sun ga bayan Dogo Gide

Daga BASHIR ISAH Rahotanni sun ce dakarun ƙasar Nijar sun ga bayan gawurtaccen ɗan bindigar nan, Dogo Gide, na mayaƙan ANSARU da sauran ƙungiyoyin 'yan ta'adda. MANHAJA ta kalato cewar, Dogo Gide ya mutu ne sakamakon raunin da ya ji biyo bayan musayar wutar da aka yi tsakanin rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) a dajin Madada da yankin Ƙaramar Hukumar Maru a ranar 12 ga Maris, 2024. An ce duk da raunin da aka yi injuries, Dogo Gide, sai da aka san yadda aka yi aka saci jiki aka shigar da shi asibiti a yankin Mabera a…
Read More
Lawal ya nemi taimakon Tinubu kan yaƙi da matsalar tsaro a Zamfara

Lawal ya nemi taimakon Tinubu kan yaƙi da matsalar tsaro a Zamfara

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu inda suka tattauna batun tsaron Jihar Zamfara. A ranar Talata suka yi ganawar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja kuma cikin sirri. Mai magana da yawun Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa Lawal ya yi wa Shugaba Tinubu bayani game da halin tsaron jihar Zamfara ke ciki, musamman sake dawowar hare-haren ta'addanci a jihar. Idris ya ce shugannin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi kan tsare-tsare da matakan da suka dace a ɗauka domin tunkarar matsalar tsaron da ta addabi Zamfara. Daga…
Read More
Gwamnati ba ta da wani hanzari kan rashin samar wa al’umma sauƙin rayuwa

Gwamnati ba ta da wani hanzari kan rashin samar wa al’umma sauƙin rayuwa

Daga NAFI'U SALISU Duk wanda yake kishin ƙasarsa da al'umma tare da ci gaban ƙasa, to shakka babu tilas ne ya nuna kishinsa ta hanyar da zai iya yin hakan, ko da kuwa hakan zai zame masa barazana a rayuwa, domin dai ita gaskiya guda ɗaya ce, kuma ko ka faɗe ta ko ka yi shiru, to gaskiya tana nan a mazauninta na gaskiya don ba za ta tava zamowa ƙarya ba. Na yi rubuce-rubuce da dama a kan halin da ƙasar nan ta samu kanta a jiya da yau, hakazalika, na sha yin maganganu na jan hankali a kan…
Read More
Mata ne jaruman watan Ramadan!

Mata ne jaruman watan Ramadan!

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU A wannan makon tunatarwar mu za ta mayar da hankali ne kan irin gudunmawar da iyayenmu mata, matanmu na aure, da ƙannenmu mata suke bayarwa a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, wanda a cikinsa mabiya addinin Musulunci a ko'ina a duniya suke gudanar da azumi, da wasu ayyuka na ibada, don neman ƙarin kusanci ga Allah. Azumi, ɗaya ne daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar wanda Allah Ya farlantawa kowanne mumini, mace ko namiji, don ya kiyaye su a matsayinsa na wanda ya karɓi addinin Musulunci a matsayin hanyar gudanar da rayuwarsa.…
Read More
Matan aure barka da Ramadan!

Matan aure barka da Ramadan!

Tare da AMINA YUSUF ALI Zuwa ga matan aure da suke bibiyar wannan shafinmu na Zamantakewa mai zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako shafin na matan aure ne. Duba da watan da muke ciki na Ramadan mai albarka. 'Yanuwana mata barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya. Allah ya karɓi ibadunmu ameen. To a wannan mako mun kawo muku wasu dabaru ta hannun ƙanwata Sakina Yazid yadda uwargida da amarya za su kauce wa wahalar azumi, ko ma na ce za su rage wahalar azumi. A wannan yanayi da…
Read More
A kawo ɗauki don magance tsadar kuɗin zuwa aikin Hajjin Bana

A kawo ɗauki don magance tsadar kuɗin zuwa aikin Hajjin Bana

Daga ABUBAKAR IBRAHIM A kowace shekara, al'ummar Musulmi suna gudanar da aikin Hajji domin cika ɗaya daga cikin shikashikan addininsu guda biyar. Abu ne wanda kowane Musulmi ke son cimmawa, aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa, yayin da kuma wani mai ƙumbar susa yake da burin ya sake komawa ya ƙara yi. Duk da haka, wanda ke da hali ne kaɗai aka wajabta wa yin wannan tafiya zuwa ƙasa mai tsarki don sauke farali. A Nijeriya, tuni shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2024 suka kankama. Sai dai kuma ana ta samun wani babban ƙalubale, musamman na kuɗin tafiya aikin na…
Read More
Gwamna Abba ya kama hanyar naɗa ɗan gidan Kwankwaso muƙamin kwamishina

Gwamna Abba ya kama hanyar naɗa ɗan gidan Kwankwaso muƙamin kwamishina

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabiru Yusuf, ya aika da sunan ɗan gidan Rabi'u Kwankwaso, Mustapha Rabi’u Kwankwaso, zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa kafin naɗa shi muƙamin kwamishina a jihar. Shugaban Manalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar a ranar Talata. A cewar Falgore, sunayen da Gwamnan ya aike sun haɗa da: 1- Adamu Aliyu Kibiya2- Usman Shehu Aliyu3- Mustapha Rabiu Kwankwaso4- Abduljabbar Garko Ana sa ran waɗanda lamarin ya shafa su bayyana a gaban Majalisar a ranar Talata, 2 ga watan Afrilun 2024, don a tantance su.
Read More