Editor

9513 Posts
Mamu ya nemi gwamnati ta janye ayyana shi da aka yi a matsayin mai taimaka wa ‘yan ta’adda

Mamu ya nemi gwamnati ta janye ayyana shi da aka yi a matsayin mai taimaka wa ‘yan ta’adda

Daga BASHIR ISAH Mawallafin Jaridar Desert Herald, Tukur Mamu, ya buƙaci gwamnati ta janye ayyana shi da ta yi a cikin jerin masu taimaka wa 'yan ta'adda a ƙasar nan. Mamu ya buƙaci hakan ne a cikin wasiƙar da ya aike wa Babban Lauyan Nijeriya mai ɗauke da kwanan wata 25 ga Maris, 2024. Lauyansa, J.J. Usman (SAN), shi ne ya rubuta wasiƙar a madadinsa, wanda a ranar Talata Jaridar News Point Nigeria ta samu ganin shaidar karɓar kwafin wasiƙar da aka aike wa AGF a Kaduna. Kwanan nan ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana sunayen wasu mutum 15 ciki har…
Read More
Ɗan shekara 44, Bassirou ya lashe zaɓen Senegal

Ɗan shekara 44, Bassirou ya lashe zaɓen Senegal

Shugaba Sall ya taya Bassirou murnar lashe zaɓe Daga BASHIR ISAH Bassirou Diomaye Faye ɗan shekara 44, ya zama sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Senegal bayan da ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ƙasar. Tuni dai Shugaban Ƙasar mai narin gado, Mavky Sall ya taya Bassirou murnar lashe zaɓen. Bayan ayyana shi a matsayin sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Senegal, Bassirou ya yi wa ‘yan ƙasar bayani game da abubuwan da za su sa ran gani bayan ya karɓi ragamar mulkin ƙasar. Haka nan, ya ce gwamnatinsa za ta yi tafiya ne cike da tsare-tsare masu inganci ba tare…
Read More
Dalilin fuskantar ƙarancin bizar Umara a Ramadan – NAHCON

Dalilin fuskantar ƙarancin bizar Umara a Ramadan – NAHCON

Daga BASHIR ISAH Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), ta bayyana cewa, rashin amfani da bizar da Saudiyya ta bai wa wasu 'yan Nijeriya tun farko, shi ne ya haifar da cikas wajen samun sabuwar biza ga masu shirin tafiya Umara a wannan wata na Ramadan. Rahotanni sun nuna yadda 'yan Nijeriya ke fama ainun wajen neman bizar da za ta ba su damar tafiya Umara a Saudiyya a watan Azumin Ramdan. Sanarwar da NAHCON ta faitar a ranar Talata ta bakin kakakinta, Fatima Sanda Usara, ta ce Saudiya kan ba da bizar Umara ga ƙasashe ne gwargwadon yawan mabuƙata,…
Read More
Ɗan takarar Gwamnan Ondo, Dokta Akintelure ya kwanta dama

Ɗan takarar Gwamnan Ondo, Dokta Akintelure ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar gwamnan Jihar Ondo ƙarƙashin jam'iyyar APC, Dr Paul Akintelure, ya kwanta dama. An tabbatar da mutuwarsa ne da safiyar Talata, 26 ga Maris, 2024. Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata marigayi Akintelure ya yi ƙorafi kan barazanar kisa da yake fuskanta. Bayanai sun ce likitan da ya duba shi ya ce, Akintelure ya rasu ne a Legas. Kafin wannan lokaci, mai magana da yawun marigayin, Oladapo Akintelure, ya faɗa a cikin wata sanarwa da ya fitar cewar yana da yaƙinin barazanar da ake yi wa maigin nasa zai gushe. Sai dai…
Read More
Tsaro: Lawal ya buƙaci a tura ƙarin dakaru zuwa Zamfara

Tsaro: Lawal ya buƙaci a tura ƙarin dakaru zuwa Zamfara

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yi kira da a ƙara yawan sojojin da ke aiki a jiharsa domin ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaro a jihar. Lawal ya yi wannan kira ne a ranar Litinin yayin da da ya ziyarci Babban Hafsan Tsaro, Christopher Gwabin Musa, a ofishinsa da ke Abuja. Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya faɗa cikin sanarwar da ya fitar cewa, Lawal ya ziyarci Babban Hafsan ne domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a Jihar Zamfara. Ya ce, yayin ganawar tasu, Gwamna Lawal ya nuna damuwa kan…
Read More
Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa ɗan China hukuncin kisa kan kisan Ummita a Kano

Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa ɗan China hukuncin kisa kan kisan Ummita a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Babbar Kotun Jihar Kano, ta yanke wa ɗan Chinan nan, Frank Geng Quarong hukuncin kisa ta hanyar rataya. Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ne ya yanke masa hukuncin, bayan tabbatar da hujjojin da masu gabatar da ƙara suka yi a gaban kotun. Idan za a iya tunawa Manhaja ta rawaito tun a ranar 16 ga watan Satumba 2022, Frank Geng, ya hallaka Ummita a unguwar Janbulo da ke jihar Kano.
Read More
Rundunar Soji za ta saki mutum 200 da ke tsare bayan wanke su daga zargin alaƙa da Boko Haram

Rundunar Soji za ta saki mutum 200 da ke tsare bayan wanke su daga zargin alaƙa da Boko Haram

Daga BASHIR ISAH Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta shirya sakin sama da mutum 200 da taje tsare da bayan wanke su da aka yi faga zargin samun alaƙa Boko Haram. A tsare waɗanda lamarin ya shafa ne a mabambantan hare-hare da sojoji suka kai a wurare daban-daban game da yaƙi da mayaƙan Boko Haram. MANHAJA ta kalato cewar, za a miƙa mutanen ne ga Gwamnatin Jihar Borno domin yin abin da ya dace kafin a sake sada su da 'yan uwansu. A wannan Talatar ake sa ran lamarin zai wakana a Barikin Sojoji da Giwa a Maiduguri, babban birnin…
Read More
Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ahmed Baba ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai na Afirka a ƙarni na 16. Marubuci kana masanin addinin Islama, ya yi aiki game da shari'a kan batun bauta da rubuta tarihin mashahuren mutane. Lokacin da Ahmed Baba ya rayu: An haifi Ahmed Baba a shekarar 1556. Wasu majiyoyi sun ce a Araouane, kimanin kilomita 250 Arewa maso Yammacin Timbuktu, birnin da ke arewacin Mali. Akwai kuma yiwuwar an haife shi a Timbuktu lokacin birnin na bunƙasa a matsayin cibiyar binciken addinin Islama da harkokin kasuwanci na yankin Sahara. Baba ya yi karatu a birnin Timbuktu…
Read More
Sarari ya ɗaukaka darajar MOPPAN zuwa ƙololuwa, inji Habibu Barde

Sarari ya ɗaukaka darajar MOPPAN zuwa ƙololuwa, inji Habibu Barde

“Muna son samar da tsarin shugabancin da zai saita masana'antar Kannywood” Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Alhaji Habibu Barde Muhammad shi ne sabon shugaban haɗaɗiyar ƙungiyar kwararru ta masu shirya fim ta ƙasa, wato MOPPAN, da ya kama mulki bayan saukar da tsohon shugaban Dakta Ahmad Muhammad Sarari ya yi a ƙarshen watan Janairun da ya gabata, wanda kafin hakan shi ne mataimaki na Arewa ta Tsakiya . Domin jin wanene Habibu Barde Muhammad da kuma irin gudunmawar da ya bayar a harkar fim, jaridar Blueprint Manhaja ta tattauna da shi, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta…
Read More
Yanzu-yanzu: Gwamnati ta gayyaci Sheikh Gumi don amsa tambayoyi kan ayyukan ‘yan ta’adda

Yanzu-yanzu: Gwamnati ta gayyaci Sheikh Gumi don amsa tambayoyi kan ayyukan ‘yan ta’adda

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta gayyaci fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, don ya zo ya amsa mata tambayoyi dangane da maganganunsa a kan ayyukan 'yan ta'adda. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin. Idris ya ce Gumi bai fi ƙarfin doka ba, yana mai cewa ganin dacewar hakan ya sa gwamnati ta yanke shawarar ta gayyaci malamin don ya amsa mata tambayoyi.
Read More