Editor

9513 Posts
Bikin Sallah: Duk gidan wasan da ya aikata ba daidai ba a Kano zai rasa lasisinsa — El-Mustapha

Bikin Sallah: Duk gidan wasan da ya aikata ba daidai ba a Kano zai rasa lasisinsa — El-Mustapha

Daga RABIU SANUSI A ƙoƙarin sa na tabbatar da ana bin dokoki sau da ƙafa, Shugaban Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta jihar Kano. Abba El-mustapha, ya kafa wani kwamiti na musamman wanda zai lura da yadda gidajen wasanni a Kano zasu gudanar da shagul-gulan bikin ƙaramar sallah. El-mustapha ya wannan jawabin ne a ranar Litinin yayin ƙaddamar da shugabancin kwamitin da mambobinsa, ƙarƙashin jagoranci daraktan kuɗi da mulki na Hukumar, Alh. Abdulkarim Badamasi, sai darakta mai lura da sashin shirya fina-finai, Alh. Idiris Zakari Ya'u Zaura. Sauran sun haɗa da Daraktan kula da sashen ɗab'i, Alh Abubakar Zakari Garin…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Laraba Saudiyya za ta yi Ƙaramar Sallah

Da Ɗumi-ɗumi: Laraba Saudiyya za ta yi Ƙaramar Sallah

Daga BASHIR ISAH Ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa, ya zuwa ranar Laraba, 10 ga watan Afrilun 2024 za a yi Ƙaramar Sallah a ƙasar. Ta ce hakan ya faru ne sakamakon rashin ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Litinin wanda hakan ya sa za a yi azumin Ramadan 30 a ƙasar. Kafin wannan lokaci, masana da masu bincike a fagen ilimin taurari sun ce da wahala a ga jinjirin watan Shawwal a ranar Litinin saboda yanayin tafiyar duniyar wata da ta rana. Da wannan, ya tabbata Laraba ce 1 ga watan Shawwal, 1445AH a ƙasar Saudiyya.
Read More
Yanzu-yanzu: Shaibu ya yi watsi da tsige shi da aka yi a muƙamin Mataimakin Gwamnan Edo

Yanzu-yanzu: Shaibu ya yi watsi da tsige shi da aka yi a muƙamin Mataimakin Gwamnan Edo

Daga BASHIR ISAH Tsigaggen Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Philip Shaibu, ya yi watsi da matakin da Majalisar Dokokin Jihar ta ɗauka na tsige shi a matsayin mataimakin gwamnan jihar. Shaibu ya bayyana haka ne cikin wani faifan bidiyon da ya wallafa a shafinsa na X jim kaɗan bayan da majalisar jihar ta sige shi. A ranar Litinin Majalisar Dokokin Jihar Edo ta tsige Shaibu daga muƙamin nasa bayan da ta karɓi rahoto kan binciken da aka gudanar a kansa, kana ta maye gurbinsa matashi ɗan shekara 38, Omobayo Marvellous Godwins, a matsayin sabon Matakin Gwamnan Jihar Edo. Majalisar ta kafa…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan shekara 38 ya zama sabon Mataimakin Gwamnan Edo

Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan shekara 38 ya zama sabon Mataimakin Gwamnan Edo

Daga BASHIR ISAH An naɗa matashi ɗan shekara 38, Omobayo Marvellous Godwins, a matsayin sabon Matakin Gwamnan Jihar Edo. Naɗin nasa ya biyo bayan tsige Mataimakin Gwamnan mai barin gado, Philip Shaibu da Majalisar Dokokin Jihar ta yi ne. Omobayo injiniya ne a fannin lantarki kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar Akoko-Edo da ke jihar. An tsige Shaibu a muƙamin mataimakin gwamnan jihar ne yayin zaman da majalisar ta yi a ranar Litinin. Majalisar ta ɗauki matakin tsige Shaibu ne bisa shawarwarin Kwamitin Binciken da ya gudana ƙarƙashin Justice S.A. Omonua-led mai murabus, binciken da aka gudanar bayan da Majalisar jihar…
Read More
Hajji kiran Allah!

Hajji kiran Allah!

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ko da mutum ya na da lafiya da guzurin tafiya aikin hajji sai Allah ya sa da rabon zai gudanar da aikin. Aikin hajji da ke cikin rukunan musulunci biyar na da matsayin mai iko ya samu damar gudanar da shi sau ɗaya a rayuwa. Wasu kan samu dama duk shekara su je aikin hajji. Wani wanda ba shi da halin zuwa ko don rashin lafiya ko rashin guzuri har ƙarshen rayuwar sa ba shi da wani laifi. A tarihi an samu bayanan yadda wasu kan ɗau haramar tafiya hajji da ƙafa su ɗau shekaru…
Read More
Ƙaramar Sallah: NSCIA ta miƙa saƙon taya murna ga al’ummar Musulmi

Ƙaramar Sallah: NSCIA ta miƙa saƙon taya murna ga al’ummar Musulmi

*Ta buƙaci a nemi wata ranar Litinin Daga BASHIR ISAH Majalisar Ƙolin Harkokin Musulunci ta Ƙasa (NSCIA), ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni, ta miƙa saƙon taya murna ga al’ummar Musulmin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya dangane da bikin Ƙaramar Sallah na bana. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da majalisar ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 7 ga Afrilu, 2024 da sa hannun sakataren Majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede, CON, FNAL. Majalisar ta ce, “Muna roƙon Allah Ya maimaita mana mu shaida hakan na shekaru masu yawa kuma cikin ƙoshin lafiya.” Ta…
Read More
Dambarwar bashin Kaduna za ta farraƙa El-Rufai da Sani?

Dambarwar bashin Kaduna za ta farraƙa El-Rufai da Sani?

*’Ya’yan El-Rufai sun shata daga a junansu Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A cikin ’yan kwanakin nan Jihar Kaduna ta ɗau zafi a siyasance kan kukan da gwamnan jihar Malam Uba Sani ya yi kan tulin bashin da ya gada daga tsohuwar gwamnati ta Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, wanda sanadiyyar haka ɗan tsohon gwamnan, Bashir El-Rufai, ya fito fili ya caccaki batun gwamnan cikin kakkausan lafazin, yayin da a ɓangare guda kuma yayansa, Bello El-Rufai, wanda ɗan majalisar tarayya na Kaduna ne, ya fito ya barranta da sukar da ya yi masa. Haka kuma dambarwar ta kuma ci Shugabar…
Read More
’Yan Nijeriya sun kaɗu da ƙarin kuɗin lantarki

’Yan Nijeriya sun kaɗu da ƙarin kuɗin lantarki

•NLC da CHRIceD sun ce akwai rashin tausayi a ƙarin kuɗin*Ba kowa ƙarin zai shafa ba, cewar gwamnati*Ƙarin zai haifar da satar wuta, inji tsohon jami'in NERC Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A daidai lokacin da al'ummar Nijeriya ke fama da raɗaɗin tashin farashin kayayyakin masarufi da tsadar rayuwar da, sai ga shi Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta fitar da sanarwar amincewa da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga kwastomomin da ke ƙarƙashin rukunin samun wuta na Band A, wato waɗanda suka fi samun wutar lantarki. A wani taron manema labarai a wannan Larabar a Abuja,…
Read More
Ɗan Majalisar Dokokin Kano, Ibrahim Kundila ya rasu

Ɗan Majalisar Dokokin Kano, Ibrahim Kundila ya rasu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono, Alhaji Halilu Ibrahim Kundila ya rasu. Majiyar Blueprint Manhaja ta nuna cewa ɗan majalisar wanda ya raba kayan agaji ga al’ummar mazaɓarsa a makon jiya, ya rasu ne a gidansa da yammacin Asabar. An gudanar da sallar jana’izar Alhaji Halilu Ibrahim Kundila ɗan jam’iyyar APC a safiyar Lahadi a unguwar Kundila da ke ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano. Daga cikin waɗanda suka halarci sallar jana’izar akwai ɗan majalisar wakilai ta ƙasa mai wakiltar Shanono/Ɓagwai, Honarabul Yusuf Ahmad Badau da sauransu. Marigayin mai…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutun bikin Ƙaramar Sallah

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutun bikin Ƙaramar Sallah

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba masu zuwa a matsayin ranakun hutun bikin Ƙaramar Sallah. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya ba da sanarwar hakan a rabar Lahadi. Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen taya al'ummar Muslmi na faɗin Nijeriya bisa kammala azumin watan Ramadan na bana, tare da fatan za a yi bikin Ƙaramar Sallah cikin lumana.
Read More