09
Apr
Daga BASHIR ISAH Shugaban Kwamitin Amintattu na Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Sani Muazu, ya bayyana alhini da kaɗuwarsa dangane da rasuwar jarumar Kannywood, Saratu Giɗaɗo wadda aka fi sani da Daso. Ya bayyana haka ne cikin bayanin da ya fitar dangane da rasuwar marigayiyar a ranar Talata. Ya ce, “Cike da alhini na bi sahun ‘yan uwa wajen sanar da rasuwar ɗaya daga cikin fitattun jaruman Kannywood, Hajiya Saratu Giɗaɗo, wacce masoyanta suka fi kira da Daso. “Rasuwarta ta zo da kaɗuwa saboda ƙalau take ba ta fama da wani rashin lafiya. Cikin ƙoshin lafiya ta…
