12
Apr
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa ta yi kira da a sake nazari a kan ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka yi a baya-bayan nan, inda ta yi barazanar shiga yajin aiki. A cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar, Adebiyi Adeyeye, ya yi gargaɗin yiwuwar shiga yajin aikin matuƙar ba a sauya ba. Hukumar da ke sa ido kan wutar lantarki ta Nijeriya ta kara haraji ga kwastomomin da ke samun wutar lantarki na sa’o’i 20 a kullum, lamarin da ya haifar da ƙarin farashin. Adeyeye ya bayyana rashin daidaiton tsarin a matsayin hanyar da ke kashe…
