13
Apr
Daga BASHIR ISAH 'Yan sanda a Jihar Kano sun fara bincike kan badaƙalar fille kan wani ƙaramin yaro mai suna Mohammed Saidu da ake zargin wani ɗan almajiri da aikatawa a ƙauyen Kanwa da ke yankin Ƙaramar Hukumar Madobi a jihar. Kwamishinan 'Yan Sandan Kano, Usaini Gumel ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) hakan ranar Juma'a a Kano. Jami'in ya ce ana zargin ɗan al'majirin mai suna Abdullahi mai shekara 16 da kisan Saidu ɗan shekara 6 da haihuwa. A cewar Gumel, wani mutum ne ya ga Abdullahi wanda ɗan asalin Jihar Zamfara ne a ƙauyen…
