14
Apr
Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa kan yaƙi da ta'addanci a Jihar Zamfara. Tinubu ya ba da odar tura ƙarin sojoji zuwa jihar a matsayin mataki na ƙarfafa wa sojoji gwiwa wajen yaƙi da ɓarayin daji a jihar. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai wadda mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Asabar. Sanarwar ta ƙara da cewa, Tinubu ya ƙarɓi baƙuncin wasu gwamnonin jihohi da kuma shugabancin Majalisar Tarayya a gidansa da ke Legas. Ta ce, gwamnonin sun kai ziyarar ne a ranar Juma'a…
