Editor

9513 Posts
A karon farko cikin shekaru 120 Bayer Leverkusen ta zama zakaran gasar Bundesliga

A karon farko cikin shekaru 120 Bayer Leverkusen ta zama zakaran gasar Bundesliga

Daga IBRAHIM HAMISU Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga na Jamus na shekarar 2023/2024, karon na farko da kafa ƙungiyar shekara 120 da ta gabata, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0. Nasarar da suka samu ta kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich ta yi tana lashe gasar. Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar. Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara…
Read More
Ƙungiyar matasa ta naɗa Ado Ahmad muƙamin ‘Sarkin Mawallafan Arewa’

Ƙungiyar matasa ta naɗa Ado Ahmad muƙamin ‘Sarkin Mawallafan Arewa’

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Arewa Youth And Women For Change ta naɗa shahararren marubucin nan, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON, daga Jihar Kano a matsayin 'Sarkin Mawallafan Arewa na Farko' kuma 'Jakadan Zaman Lafiyar Arewa'. Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Babbar Sakatariyar Ƙungiyar, Ambasada Sadiya Ahmed Birniwa. Ƙungiyar ta ce ta naɗa Ado wannan muƙamin ne duba da irin gudunmawar da yake bayarwa ga cigaban al'umma, musamman ga rayuwar mata da matasa. Ta ƙara da cewa, sai da ta yi nazari mai zurfi tare da tantance wasu ɗaiɗaikun…
Read More
Dala ta sake shan kaye a hannun Naira, Dala 1 ta koma N1000

Dala ta sake shan kaye a hannun Naira, Dala 1 ta koma N1000

Daga BASHIR ISAH Kawo yanzu, Dalar Amurka na ci gaba da shan kashi a hannun Naira ta Nijeriya. Bayanai sun ce a wannan Litinin ɗin, an sayar da Dala 1 kan N1000 a kasuwar canji. Idan za a iya tunawa, a Litinin ta makon jiya Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya saida wa 'yan canji (BDC) Dala miliyan $15.88 a kan N1,101 ga kowace Dala 1. 'Yan Nijeriya na ci gaba da fatan ganin Naira ta yi wa Dala rugugu ko sa samu sauƙin tsadar rayuwar da ake alƙanta ta da tashin Dala.
Read More
Ƙarin kuɗin lantarki: Dole ku sake nazari – Dattawan Arewa ga gwamnati

Ƙarin kuɗin lantarki: Dole ku sake nazari – Dattawan Arewa ga gwamnati

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta bayyana ƙarin kuɗin wutar lantarki da Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu ta yi a matsayin cin amanar da ’yan Nijeriya suka danƙa mata. A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai Abdulazeez Suleiman a ranar Alhamis, ta nuna matukar damuwa da takaici kan matakin da gwamnatin Tinubu ta ɗauka na ƙara farashin wutar lantarki a Nijeriya. Sanarwar ta ce, “Wannan matakin na Tinubu yana nuna rashin mutunta jin daɗin al’ummar Nijeriya. “NEF ta fahimci cewa, wannan gagarumin ƙarin kuɗin wutar lantarkin zai…
Read More
Mutum 3 sun mutu, 12 sun jikkata sakamakon rikici tsakanin sojoji da matasa a Yobe

Mutum 3 sun mutu, 12 sun jikkata sakamakon rikici tsakanin sojoji da matasa a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Biyo bayan wata hatsaniyar da ta ɓarke tsakanin sojoji da 'Yan Adai-daita Sahu (Napep) a garin Gashuwa, shalkwatar ƙaramar hukumar Bade dake jihar Yobe, ya jawo asarar rayukan mutum uku tare da raunata mutum 12 a ranar Lahadi. Bayanan da wakilinmu ya tattaro sun nuna cewa, hatsaniyar ta ɓarke ne sakamakon wata rashin jituwar da ta ɓarke tsakanin sojojin da Yan Adai-daita Sahun bayan nuna rashin jin daɗi kan matakin da sojojin suka ɗauka na halaka wani matuƙin Keke Napep. Wata majiya a Babbar Asibitin Ƙwararru da ke garin Gashuwa ta bayyana cewa, an kawo…
Read More
Sau uku ina kama matata da aikata baɗala — Zango

Sau uku ina kama matata da aikata baɗala — Zango

Daga BASHIR ISAH Jarumi a masana'antar Kannywood, Adam A. Zango, ya bayyana cewa sau uku yana kama matarsa da aikata baɗala, amma duk da haka ya yi haƙuri ya ci gaba da zama da ita. An ji jarumin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo.mai tsawo da aka yaɗa a soshiyal midiya. A cikin bidiyon, jarumin ya taɓo batutuwa da dama, daga ciki har da yadda wasu abokan sana'arsa waɗanda ya taɓa bai wa gudunmawa a rayuwa ba sa ba shi kariya ga mutuncinsa da kuma irin rashin haɗin kan da ke Kannywood. Haka nan, Jarumin ya taɓo…
Read More
‘….Mu taimaka wa Adam Zango da soyayya a halin da yake ciki’

‘….Mu taimaka wa Adam Zango da soyayya a halin da yake ciki’

Daga FAUZIYYA D. SULAMAIN Ban taɓa magana a kan wani ɗan fim ba, amma halin da Adam Zango ke ciki yana buƙatar mu nuna masa soyayya irin ta addini. Yana buƙatar mu ja shi a jiki, abubuwan da ya ke yi a yanzu akwai damuwa. Don Allah a samu waɗanda za su je kusa da shi don Allah, komai zai iya faruwa da shi, domin a yanzu yana ruguza gidansa da rayuwar yaransa da danginsa da 'yan'uwansa. Amma don Allah mu ja shi a jiki, kar mu ji haushinsa yana buƙatar kulawar duk wani musulmi hakan zai dawo da shi…
Read More
Walin Zazzau kuma Hakimin Ikara, Aminu Umar ya kwanta dama

Walin Zazzau kuma Hakimin Ikara, Aminu Umar ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Majalisar Masarautar Zazzau ta sanar da rasuwar Walin Zazzau kuma Dagacin Ikara, Engineer Aminu Umar. Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne bayan kammala bukukuwan sallar da masarautar ta shirya albarkacin Ƙaramar Sallah. Marigayi Umar ya fito ne daga zuriyar marigayi Sarki Dalhat daga daular Barebari ta Masarautar Zazzau. A halin rayuwarsa, ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Hukumar Ruwar ta Jihar Kaduna. Da yake tabbatar da rasuwar marigayin, mai magana da yawun masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, Marigayin ya halarci Hawan Daushen da Masarautar Zazzau ta shirya a ranar Juma'a. Kuma yana ɗaya daga cikin sarakan da suka…
Read More
Gwamna Lawal ya zama ‘Wakilin Ƙauran Namoda’

Gwamna Lawal ya zama ‘Wakilin Ƙauran Namoda’

Daga BASHIR ISAH An naɗa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, sarautar Wakilin Ƙauran Namoda. Wannan na zuwa ne biyo bayan Hawan Daushen da Gwamna Lawal ya halarta a ranar Lahadi wanda Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda a jihar ta saba shiryawa duk shekara lokacin bikin sallah. Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya ce hawan daushe a lokacin bikin sallah kan haɗo kan jama'a wuri guda don gudanar da bukukuwa da raya gargajiya. Sanarwar manema labarai da Sulaiman ya fitar ta ce, an naɗa Gwamna Lawal a matsayin 'Wakilin Ƙaura', wanda ke nufin mai wakilcin wanda ya kafa masarautar. A cewar sanarwar,…
Read More
Bayan shekara 10 da sace ‘yan matan Chibok: Wani abu da ya kamata a sani

Bayan shekara 10 da sace ‘yan matan Chibok: Wani abu da ya kamata a sani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jaridar News Point Nigeria ta samu damar haɗuwa da Lisu a sirrance, yayin da ta ce wasu na ƙoƙarin hana ta magana da ‘yan jarida. Lisu na ɗaya daga cikin 'yan mata 276 da aka sace daga makarantar sakandare ta 'yan mata a garin Chibok shekaru goma da suka wuce - satar da ta girgiza duniya kuma ta haifar da zangar-zangar neman a dawo da 'yan matan mai taken: #BringBackOurGirls, wanda har ya haɗa da uwargidan tsohon Shugaban Ƙasar Amurka, Michelle Obama. Sama da 180 ne dai suka kuɓuto ko kuma aka sake su,…
Read More