Editor

9513 Posts
Alfanun zuwan Turawa ƙasar Hausa

Alfanun zuwan Turawa ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wannan cigaba ne daga rubutun makon da ya gabata. Duk da cewa, Bature ya zo ya samu Bahaushe da cikakkiyar wayewar addini, sarauta, sutura, karatu da rubutu da kuma wayewar kasuwanci da sauransu. Amma duk da irin wannan cigaba da Bahaushe yake da shi kafin zuwan Turawa, an samu ƙarin cigaba a fannonin da dama sakamakon zuwan nasu. Wannan cigaban kuwa ya sauya yanayin yadda Bahaushe yake gudanar da harkokinsa na rayuwa kusan baki ɗaya sai dai ‘yan abubuwan da ba za a rasa ba. Idan muka kalli yanayin yadda Bahaushe yake gudanar da harkokinsa na…
Read More
NDLEA ta damƙe masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi 51,000, ta gurfanar da 9000 a cikin shekara uku

NDLEA ta damƙe masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi 51,000, ta gurfanar da 9000 a cikin shekara uku

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Miyagun ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), ta ce a tsakanin shekaru uku da suka gabata, ta samu nasarar damƙe masu ta'ammali da miyaƙun ƙwayoyi mutum 50,901 kana ta gurfanar da 9000. Shugaban Hukumar na Ƙasa, Buba Marwa ne ya bayyana hakan a wajen bikin ƙaddamarwa da kuma miƙa ginin da Gwamnatin Birtaniya ta bai wa hukumar a matsayin gudunma wanda aka gudanar a ranar Litinin. Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi ya fitar, ta rawaito Marwa na cewa, daga cikin mutum 50,901 da aka kama bisa zargin ta'ammali da…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe Sakataren PDP a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe Sakataren PDP a Zamfara

Daga BASHIR ISAH Wasu 'yan bindiga da ake zargin ɓarayin daji ne a Jihar Zamfara, sun kashe Sakataren Jam'iyyar PDP na Ƙaramar Hukumar Tsafe a jihar, Musa Ille. Majiyarmu ta ce an kashe marigayin ne a ƙofar gidansa bayan da da 'yan bindigar suka yi wa gidan ƙawanya a ranar Litinin da daddare. Shugaban PDP na yankin, Garba Garewa, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai a ranar Talata. Ya ce, “Muna zargin makisan 'yan fashin daji ne, jiya (Litinin) suka shiga gidansa suka halbe shi." Wani mazaunin yankin, Abubakar Tsafe, ya shaida wa jaridar News Point…
Read More
Shugabancin APC na Jihar Kano ya dakatar da waɗanda suka dakatar da Ganduje a matakin Gunduma

Shugabancin APC na Jihar Kano ya dakatar da waɗanda suka dakatar da Ganduje a matakin Gunduma

Daga BASHIR ISAH Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar APC na Jihar Kano, ya saka wa shugabannin jam'iyyar na gundumar Ganduje c'da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa takunkumi bisa dakatar da Shugaban APC na Ƙasa Umar Abdullahi Ganduje, da suka yi a ranar Litinin. Shugabancin APC na ƙaramar hukumar ya daƙile matakin dakatarwar da aka yi wa Gandujen ne tare da sauke waɗanda ke da hannu a korar daga muƙamansu. Shugaban APC na Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, Inusa Dawanau, ya shaida wa manema labarai cewa, an samu waɗanda suka dakatar da Ganduje da yi jam'iyya zagon ƙasa, tare da cewa an samu…
Read More
Raɗɗa ya raba wa jami’an tsaro motocin aiki a Katsina

Raɗɗa ya raba wa jami’an tsaro motocin aiki a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, ya miƙa wa jami’an tsaro motocin yaƙi masu sulke guda 10 domin gudanar da aiki a ƙananan hukumomi takwas dake fama da matsalar rashin tsaro a jihar Katsina don ƙarfafa tsaron al'uma. Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da motocin ne don inganta tsaron jihar wanda sojoji da 'yan sanda da kuma jami'an tsaron da gwamnatin jihar ta kafa ke jagoranta a ƙananan hukumonin da matsalar ta fi ta'azzara. Taron miƙa motocin ya gudana ne ranar Talata a gidan gwamnatin jihar. A jawabinsa, Gwamnan ya nanata cewa zai ci gaba da…
Read More
Me ya jawo mutuwar auren G-Fresh da Sadiya Haruna? 

Me ya jawo mutuwar auren G-Fresh da Sadiya Haruna? 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Tun bayan da jarumar Tiktok ɗin nan, kuma tsohuwar matar G-Fresh Al-Ameen, Sayyida Sadiya Haruna ta fitar da sanarwar cewa, aurenta da tsohon mijinta Abubakar Ibrahim (G-Fresh Al-Ameen) ya zo ƙarshe, sakamakon biyansa kuɗi Naira dubu 500 da ta yi, mutane ke ta tofa albarkacin bakinsu. Daga masu cewa dama mun san a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, sai masu cewa gara ma haka, an sayar da gonar rago an saya mai fura!  Za ku iya tunawa tun da sanyin safiyar wata ranar 16 ga Yuni na shekarar 2023 ne zaurukan sada zumunta suka wayi…
Read More
Kotu ta umurci Jaruma Halima Abubakar da ta biya Apostle Suleman tarar miliyan 10

Kotu ta umurci Jaruma Halima Abubakar da ta biya Apostle Suleman tarar miliyan 10

Daga AISHA ASAS Babbar Kotun Tarayya ta umurci jaruma a masana’antar Nollywood Halima Abubakar da ta biya tarar Naira miliyan 10 ga Apostle Johnson Suleman kan kalaman ɓata suna da ta yi a shafinta na Instagram. Baya ga haka, kotun ta haramtawa jarumar yin kowanne irin kalamai kan faston. Suleman ya zargi jarumar da wallafa kalaman cin zarafi gare shi ciki kuwa har da kiransa da mutumin banza da kuma mabiɗi mata. Duk da cewa kotun ta ba wa jaruma Halima damar kare kanta tare da bayar da hujjar da za ta wanke ta daga zargin na limamin Cocin, sai…
Read More
An kori Ganduje daga Jam’iyyar APC

An kori Ganduje daga Jam’iyyar APC

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jam'iyyar APC ta mazaɓar Dr. Abdullahi Umar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta sanar da dakatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin mamaba a jam'iyyar. Mai bai wa Jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a mazaɓar Ganduje, Hon. Halliru Gwanzo ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin. Halliru Gwanzo ya ce sun yanke shawarar dakatar da Ganduje daga jam’iyyar ne sakamakon zarge-zargen da gwamnatin Jihar Kano ta yi masa na karɓar cin hanci da rashawa. Ya ce dakatarwar ta fara ne daga daga ran 15…
Read More
Mun samu nasarar taƙaita ayyukan rashin ɗa’a a gidajen wasanni a Kano – Hukumar Tace Finafinai

Mun samu nasarar taƙaita ayyukan rashin ɗa’a a gidajen wasanni a Kano – Hukumar Tace Finafinai

Daga WAKILINMU Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba El-mustapha, ta bayya nasarar da ta samu wajen taƙaita ayyukan rashin ɗa'a a gidajen wasanni yayin bikin Ƙaramar Sallah da ya gabata. Hukumar ta bayyana hakan ne cikin sanarwar manema labarai da ta fitar a ranar Litinin. Sanarwar ta ce, "Babbar Nasarar mu a bana ita ce yadda ayyukan rashin ɗa'a suka ragu a gidajen wasanni yayin bikin Ƙaramar Sallah." Ta ƙara da cewa, "Mun yi gargaɗi tare da bada shawarwari ga wasu daga cikin gidajen wasannin a faɗin Kano. "Kwamitin bin dig-digi kan yadda gidajen wasanni a faɗin…
Read More