18
Apr
Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ma'aikatar Ilimi ta Ƙasa da ta saka ɗaliban da suka kammala karatu a Jami'ar National Open University (NOUN) a tsarin yi wa ƙasa hidima da aka fi sani da NYSC a taƙaice. Haka nan, Shugaban ya amince a lamunce wa ɗaliban da suka kammala NOUN halartar Makarantar Lauyoyi, wato Law School domin. Tinubu ya ɗauki wannan mataki ne domin samun daidaito wajen baiwa 'yan ƙasa damar cin gajiyar damammakin da ake da su a ƙasa. Shugaba Tinubu ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wajen taron bikin yaye ɗalibai karo…
