Soja ya faɗa komar ‘yan sanda kan daɓa wa ɗan acaɓa wuƙa a mashaya

Daga BASHIR ISAH

Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Legas ta tabbatar da tsare wani sojan Nijeriya bisa zargin daɓa wa wani ɗan acaɓa a wuƙa a mashaya.

Rundunar ta ce sojan na aiki ne tare da 159 Battalion da ke Yobe, kuma ya luma wa ɗan acaɓan wuƙar ce a ciki.

Kakakin ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da tsare sojan a ranar Litinin. Inda ya ce an kama sojan ne da misalin ƙarfe 3:00 na asubahin Asabar a yankin Ikorodu da ke Legas.

Hundeyin ya ce lamarin ya auku ne sakamakon saɓanin da ya shiga tsakanin sojan da ɗan acaɓan kan dalilin da ba a bayyana ba a wata mashaya.

Ya ƙara da cewa, harin wuƙar da sojan ya kai wa ɗan acaɓan hakan ya haifar masa da raunuka, kuma barazana ce ga rayuwar ɗan acaɓan.

“’Yan sanda sun ziyarci wurin da ya faru, kuma an ɗauki ɗan acaɓan zuwa asibiti don yi masa magani.

“An tsare wanda ake zargi ɗauke da wuƙar da ya aikata aika-aikar, sannan ana ci gaba da zurfafa bincike kan lamarin,” in ji jami’in.