Editor

9513 Posts
Ni ɗan wasa ne na musamman, inji Ronaldo

Ni ɗan wasa ne na musamman, inji Ronaldo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Cristiano Ronaldo ya bayyana kansa a matsayin ɗan wasa na musamman, sannan ya haƙiƙance cewa, zamaninsa bai ƙare ba a daidai lokacin da ya koma sabuwar ƙungiyarsa ta Al Nassr da ke ƙasar Saudiyya. Ɗan wasan gaban na Portugal mai shekaru 37, ya rattaba hannu kan gagarumar yarjejeniyar da aka kiyasta darajarta kan Yuro miliyan 200 bayan ya kammala zamansa a Manchester United da Real Madrid da Juventus. "Ni ɗan wasa ne na musamman. Na ji daɗin zuwa nan, na kafa dukkanin tarihi a nahiyar Turai, kuma ina son na kafa a Saudiyya,” inji Ronaldo. Ɗan…
Read More
Ba mu da ikon hana mahandama sake mallakar kadarorinsu da EFCC ta yi gwanjonsu – Majalisar Wakilai

Ba mu da ikon hana mahandama sake mallakar kadarorinsu da EFCC ta yi gwanjonsu – Majalisar Wakilai

Daga AMINA YUSUF ALI Kwamitin Majalisar Wakilai na Musamman kan tantance kadarorin da aka sata na gwamnati masu motsawa da girkakku tun daga shekarar 2000 zuwa 2022 sun bayyana cewa, ba su da ikon hana barayin gwamnati daga sake mallakar kadarorinsu da gwamnati ta ƙwace ba, a wannan gwanjo da ake yi na dukkan kadarorin da gwamnati ta ƙwace daga jami'an gwamnati da suka yi sama-da-faɗi da su.  Shugaban kwamitin gaggawa na 'yan majalisar na gwanjon kayan gwamnati Honarabul Adejoro Adeogun ya bayyana cewa, da ma tuntuni kwamitin da yake jagoranta ya faɗa wa hukumar yaƙi da cin Hanci da…
Read More
Dubai ta soke harajin sayar da barasa domin jan hankalin baƙi

Dubai ta soke harajin sayar da barasa domin jan hankalin baƙi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumomin Dubai sun soke harajin da ake biya na kashi 30 cikin 100 na sayen barasa a wani yunƙurin zawarcin ’yan yawon buɗe ido. Jama'a za su daina biyan kuɗin harajin da suke bayarwa na ƙa'ida na samun izinin barasa a gida, wanda sai sun yi haka ne suke da damar sha ba tare da cewa sun keta doka ba. A baya-bayan nan Dubai na ta sassauta dokokinta inda take bayar da damar sayar da barasa a fili kuma a rana tsaka hatta a cikin watan azumi na Ramadan, tare kuma da amincewa da kai barasar…
Read More
2023: INEC ta fara tantace ‘yan jarida

2023: INEC ta fara tantace ‘yan jarida

Daga BASHIR ISAH A matsayin ɓangare na shirye-shiryen zaɓen 2023, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta fara tantance 'yan jarida da kafafen yaɗa labaran da ke da sha'awar yin aiki da ita yayin zaɓen. Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na intanet, inda ta ce za ta gudanar da tancewar ce ta intanet kaɗai. INEC ta ce za ta buɗe shafin yin rijistar ne daga ranar Alhamis, 5 ga Janairu zuwa Lahadi, 5 ga Fabrairu na 2023. Ta ƙara da cewa, kafafen yaɗa labaran da ke da sha'awar tura wakilansu yayin zaɓen, suna iya shigar da…
Read More
An naɗa Uba Kari Wazirin Bauchi bayan badaƙalar tuɓe Muhammadu Kirfi

An naɗa Uba Kari Wazirin Bauchi bayan badaƙalar tuɓe Muhammadu Kirfi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Masarautar Bauchi ta naɗa Alhaji Muhammad Uba Ahmed Kari a matsayin sabon Wazirinta kuma ɗan Majalisar Masarautar. A wata sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na Masarautar Bauchi, Babangida Hassan Jahun ya fitar a ranar Alhamis, ya sanar da cewa Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu ya naɗa Alhaji Muhammadu Uba Ahmad Kari a matsayin sabon Wazirin Bauchi.  Kan wannan matakin, Uba Ahmed Kari ya maye gurbin Muhammadu Bello Kirfi da aka samu da rashin biyayya wa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad. Wani yanki na sanarwa na cewa: "Majalisar Mai Martaba Sarkin Bauchi…
Read More
Bayyana kadara: Kotu ta haramta wa DSS tsare shugaban INEC

Bayyana kadara: Kotu ta haramta wa DSS tsare shugaban INEC

Daga WAKILINMU Babbar Kotun Tarayya a Abujata dakatar da karar da aka shigar gabanta na neman tsige Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, daga mukaminsa kan zargin ba da bayanan karya dangane da kadarorinsa. Alƙalin Kotun, M. A. Hassan, ya ce bayanan gaskiya Yakubu ya bayar dangane da kadarorin da ya mallaka kuma daidai da doka, don haka ya ƙi amincewa da ƙarar da aka shigar kan shugaban na INEC. A zaman kotun na ranar Laraba, alƙalin ya hana hukumar DSS da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Hukumar Da'ar Ma'aikata (CCB) kama Yakubun. Ya yanke hukuncin ne…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Uba Kari ya zama sabon Wazirin Bauchi

Da Ɗumi-ɗumi: Uba Kari ya zama sabon Wazirin Bauchi

Masarautar Bauchi ta naɗa Alhaji Muhammad Uba Ahmed Kari a matsayin sabon Wazirinta kuma ɗan Majalisar Masarautar. Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da Masarautar ta fitar ranar Alhamis ta hannun jami'in labaranta, Babangida Hassan Jahun. Sanarwar ta ce za a yi wa sabon Wazirin Bauchin naɗi ne a ranar Juma'a, 6 ga watan da ake ciki a Fadar Masarautar Bauchi. Wannan na zuwa ne bayan da masarautar ta tuɓe Muhammadu Bello Kirfi a matsayin wazirinta saboda rashin da’a ga Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.
Read More
Rubutu mai inganci ne tushen cigaban marubuci – Yusuf Gumel

Rubutu mai inganci ne tushen cigaban marubuci – Yusuf Gumel

"Adabi ba zai taɓa mutuwa ba har sai an wayi gari babu wanda ya rage a duniya" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wani salo da ya bambanta marubuta maza da mata, shi ne batutuwan da kowanne ɓangare ya fi mayar da hankali a kansa don faɗakar da al'umma. A yayin da a ɗaya vangaren akasarin marubuta mata ke rubutu kan batutuwan da suka shafi zamantakewar aure da rayuwa, maza sun fi baje basirarsu ne ta ɓangaren jarumta da almara ko abubuwa masu tsoratarwa, da kuma a wani batutuwan da suka shafi sarauta da siyasa. Ko da yake kowanne daga cikin waɗannan…
Read More
NERC ta yi ƙarin kuɗin wuta a ɓoye

NERC ta yi ƙarin kuɗin wuta a ɓoye

Daga WAKILINMU Hukumar Kula da Rarraba Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC), ta ƙara kuɗin wutar lantarki a ɓoye ba tare da sanin 'yan ƙasa ba. NERC ta yi haka ne ta hanyar bai wa kamfanonin rarraba lantarki umarnin su ƙara kuɗun wutar da suke bai wa jama'a. Kamfanin Rarraba Lantarki na Abuja (AEDC), ya tabbatar da ƙarin farashin a saƙonsa da ya wallafa a shafinsa na Tiwita ranar Laraba. Saƙon ya ce, “Barka dai, a sani cewa ƙarin farashin lantarki umarni ne daga NERC.” Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani bayani a hukumance daga daga NERC kan batun.
Read More
Wanda ya ka harin bom yayin ziyarar Buhari Kogi ya fada a komar DSS

Wanda ya ka harin bom yayin ziyarar Buhari Kogi ya fada a komar DSS

Daga WAKILINMU Hukumar tsaro ta DSS ta sanar cewa ta cafke wanda ake zargi ya jagoranci dana bom din da ya tashi a yayin da Shugaba Buhari ke ziyarar aiki a Jihar Kogi.  A ranar 29 ga Disamba, 2022 ne bom ya tashi kusa da Fadar Sarki Ohinoyi na Kasar Ibira a Okene, Jihar Kogi yayin da Shugaba Buhari ke ziyarar aiki a masarautar. Mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya faɗa a ranar Laraba cewa, "Yayin bincikensu an gano wanda aka cafken babban kwamanda ne a ISWAP. "Ya jagoranci ko yana da hannu a hare-haren da aka kai…
Read More