07
Jan
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Lokacin na ƙara ƙurewa tawagar Kamaru ta ’yan qasa da shekara 17 domin bayar da sunayen ’yan wasan da za su buga mata wasannin share fage na Gasar Kofin nahiyar Afrika. Wannan ya biyo bayan matsawar da Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasar, Samuel Eto’o ya yi, kan cewa sai an yi wa ko wanne ɗan wasa gwaji, wanda da yawa suka gaza tsallake gwajin. Tsohon ɗan wasan Barcelona da Inter Milan ya dage sai an yi amfani da na’urar gwajin shekaru ta (MRI) domin tantance ’yan wasan a filin atisayensu da ke Mbankomo, a wajen…
