08
Jan
Wani rahoto na baya-bayan nan da Insider Monkey ya fitar ya nuna cewa Nijeriya ba ta cikin jerin ƙasashe 12 da suka fi samun ci gaba a nahiyar Afirka. A cewar rahoton mai taken, “ƙasashe 12 Mafi Cigaba a Afirka”, Afirka na ɗaya daga cikin nahiyoyin da suka fi arziki a duniya wajen samar da albarkatun qasa. Abin ban mamaki kuma, nahiyar na ɗaya daga cikin yankuna mafi ƙarancin ci gaba a duniya. Ƙasashen da suka shiga jerin sun yi amfani da albarkatun qasarsu wajen inganta tattalin arzikinsu. Irin waɗannan qasashe su ne; Ghana, Zimbabwe, Masar, Maroko, Afirka ta Kudu,…
