Editor

9513 Posts
An samu ƙaruwar satar ɗanyen mai cikin wata biyar a Nijeriya – NNPC

An samu ƙaruwar satar ɗanyen mai cikin wata biyar a Nijeriya – NNPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Kamfanin Mai na Nijeriya NNPC, Malam Mele Kyari ya bayyana cewa an samu ƙaruwar satar ɗanyen mai a Nijeriya cikin watanni biyar, kamar yadda ya faɗa ranar Talata a Abuja, inda ya ce jami'an tsaron ƙasar sun gano aƙalla wurare 295 da aka fasa bututun don satar man a cikin tafiyar kilomita 200. Ya sanar da hakan ne yayin wani taron manema labarai a Fadar Shugaban ƙasar. A cewar Mele Kyari an kama mutane 122 da hannu a satar man tsakanin watan Afrilun bana da wannan watan na Agusta da ake ciki kaɗai.…
Read More
NIMET ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohin Arewa biyar

NIMET ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohin Arewa biyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa, NIMET ta yi hasashen fuskantar ƙaƙƙarfan ruwan sama na tsawon kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa a wasu jihohin arewacin ƙasar 5, da kuma birnin Abuja, fadar gwamnatin Nijeriya. Cikin rahoton hasashen yanayin da hukumar ta NIMET ta fitar, ta ce jihohin da za su fuskanci wannan ruwa na tsawon kwanaki 4 ba tare da ƙaƙƙautawa ba sun haɗa da Kaduna, Neja, Bauchi, Filato da kuma Jihar Nasarawa, baya ga birnin tarayyar ƙasar. Rahoton na NIMET ya kuma yi hasashen fuskantar madaidaicin ruwan sama a wasu jihohin Nijeriya daga Kudanci…
Read More
Halin ha’ula’i da makarantar Turaki da ke cikin birnin Sakkwato ke ciki

Halin ha’ula’i da makarantar Turaki da ke cikin birnin Sakkwato ke ciki

…Mun bada umarnin kawo ƙarshen matsalar cikin gaggawa, cewar Shugaban SUBEB Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Makarantar ta Turaki dai na ɗaya daga cikin makarantun firamari a Sakkwato dake da daɗaɗɗen tarihi kasantuwar bayanai sun nunar da cewa an kafata ne tun a lokacin mulkin gwamnan soji na wancan lokacin Gado Nasko kimanin shekaru 40 da suka gabata. Duk da daɗaɗɗen tarihin da makarantar firamarin ke da halin rashin magudanun ruwa dake damun makarantar ke fuskanta na cigaba da zama wani babban ƙalubale ga muhallin karatu ga ɗaliban makarantar dake karatu a ciki. Manhaja ta samu damar kai ziyara a…
Read More
Sin ta yi watsi da rahoton MƊD game da batun kare haƙƙin bil Adama a Xinjiang

Sin ta yi watsi da rahoton MƊD game da batun kare haƙƙin bil Adama a Xinjiang

Daga CMG HAUSA Ƙasar Sin ta yi watsi da rahoton da MƊD ta fitar, game da batun kare haƙƙoƙin bil Adama a jihar Xinjiang ta ƙasar Sin, tana mai bayyana rahoton da tarin ƙarairayi, waɗanda aka kitsa domin amfani da su a matsayin makamin siyasar Amurka da ƙasashen yamma. Da yake tsokaci game da hakan a yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya ce fitar da rahoton mai cike da rashin gaskiya, da ofishin babban kwamishinan MƊD mai lura da kare haƙƙoƙin bil Adama ya yi, ya tozarta darajar ofishin. Mai fassara: Saminu
Read More
Kwamitin sulhun MƊD ya yi kira da a ƙara ƙaimi wajen inganta ƙwarewa a Afirka

Kwamitin sulhun MƊD ya yi kira da a ƙara ƙaimi wajen inganta ƙwarewa a Afirka

Daga CMG HAUSA Kwamitin sulhu na MƊD ya yi kira da a ƙara daidaita tsarin hadin gwiwa a tsakanin dukkan abokan hulɗa masu ruwa da tsaki, musamman ta hanyar inganta ƙwarewa wajen tinkarar matsalar tashe-tashen hankula, da wanzar da zaman lafiya da sauran ƙalubale a nahiyar Afirka. A cikin sanarwar da shugaban kwamitin sulhun majalisar na karɓa-karɓa na watan Agusta, kana zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD Zhang Jun ya gabatar, kwamitin mai wakilai 15 ya amince da buƙatar ƙara karfin ƙwarewar ƙasashen Afirka yadda ya kamata, da haɗa kai, da daidaita al'amura, da matakan da suka dace da yanayin…
Read More
Tashar samaniya ta Sin: ‘Yan sama jannati na kumbon Shenzhou-14 sun fara tattaki a wajen tashar

Tashar samaniya ta Sin: ‘Yan sama jannati na kumbon Shenzhou-14 sun fara tattaki a wajen tashar

Daga CMG HAUSA ‘Yan sama jannatin ƙasar Sin na kumbon Shenzhou-14, sun fara tattakin da aka tsara zai kai na sa’o’i 7, a wajen tashar binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin, tun daga karfe 6:26 na yammacin Alhamis din nan, bisa agogon birnin Beijing, daidai da ƙarfe 10:26 agogon GMT. Dan samajannti Chen Dong ne ya buɗe ƙofar fita, ta ɓangaren ɗakin binciken samaniya na Wentian dake tashar ta samaniya. Kana Chen Dong da Liu Yang suka fita wajen ɗakin, yayin da Cai Xuzhe ke tallafa musu da wasu hidimomi ta cikin tashar. Ana sa ran ‘yan sama jannatin za…
Read More
Na gaba ya yi gaba….

Na gaba ya yi gaba….

Daga IBRAHIM YAYA Da alamu dai haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka, tana ci gaba da tsolewa wasu ƙasashe ido, waɗanda a baya suke ta yunƙurin ƙirƙiro bayanai na ƙarya da nufin ɓata wannan alaƙa mai dimbin tasiri da fa’ida ga ɓangarorin biyu. Amma bakin alƙalami ya riga ya bushe. Ƙasa ta baya-bayan nan da ta bijiro da maitarta a fili wajen ganin ta ƙulla alaƙa da ƙasashen Afirka, ita ce ƙasar Japan, inda ta shirya taron raya ƙasashen Afirka karo na 8 a kasar Tunusiya daga ranar 27 zuwa ta 28 ga watan Agustan shekarar 2022…
Read More
Tomas Bach ya taya CMG murna

Tomas Bach ya taya CMG murna

Daga CMG HAUSA Tomas Bach, shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya, ya aike da wasiƙa zuwa ga babban rukunin gidan rediyo da telabijin na ƙasar Sin CMG, a jiya Talata, inda ya taya shi murnar samun izinin watsa shirye-shiryen telabijin game da gasar Olympics da za ta gudana a birnin Paris na ƙasar Faransa a shekarar 2024. Fassarawar Bello Wang.
Read More
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ƙarfafa wa kamfanonin ƙasar gwiwar halartar baje kolin CIIE

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ƙarfafa wa kamfanonin ƙasar gwiwar halartar baje kolin CIIE

Daga CMG HAUSA Wani jami'in gwamnatin Afirka ta Kudu ya sanar da cewa, kamfanonin ƙasar za su halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje na ƙasar Sin (CIIE) na shekarar 2022, inda suke sa ran samun fa'ida mai kyau, kuma gwamnati za ta taimaka musu wajen ganin hakan ya tabbata. Mataimakin babban darakta mai kula da bunƙasa fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje da samun bunƙasuwa da zuba jari a ma’aikatar cinikayya, da masana’antu da yin takara na ƙasar Lerato Mataboge ne, ya bayar da wannan sanarwa, yayin da yake amsa tambayar wakilin kamfanin…
Read More
Rashin shugabannni masu kishin al’ummarsu ne babban ƙalubalenmu – Hajiya Zulaihat Abdullahi

Rashin shugabannni masu kishin al’ummarsu ne babban ƙalubalenmu – Hajiya Zulaihat Abdullahi

"Rayuwar mace a siyasa na da haɗari sosai" "Addu'ar mijina ce ta sa nake ganin nasara a siyasata" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Dimukraɗiyya tsari ne da yake bai wa kowanne ɗan ƙasa ýanci ya zaɓi shugaban da yake so ya jagoranci al'amarin ƙasar sa ko yankinsa, haka kuma yana da ýancin shiga takara don neman goyon bayan jama'a shi ma a zave shi. Shi ya sa jama'a ke murna da zuwan lokacin zave, domin kowa ya shiga a dama da shi. Sai dai ba kasafai tsarin dimukraɗiyya da yanayin gudanar da siyasa musamman a yankin Arewa yake bai wa mata…
Read More