02
Sep
Daga FATIMA IBRAHIM GARBA DAN-BORNO Ci gaba daga makonnjiya… Sulaiman yana komawa gida kai tsaye ɗakin da ya ware domin Salima ya shiga. Tana zaune ta yi tagumi. Duk da ledan fitsarin da ke jikinta hakan bai hana ɗakin ɗaukan zarni ba. Gaba ɗaya ta susuce ta zama tamkar mahaukaciya. Yadda ta zura mashi idanu yasa ya haɗe rai, "Me ya sa kike yi mini irin kallon nan?" Ta saki murmushinta da take yawan jifansa da shi a duk lokacin da tijararsa ta motsa masa. "Na gaya maki zan ƙara aure ko?"Ta ɗaga kai alamun "Eh." Ya sake cewa, "Ko…
