04
Sep
Sama da watanni shida kenan da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta tsunduma yajin aikin makonni huɗu da farko inda daga baya suka fara na gama-gari domin neman a biya musu buƙatunsu. A fili ƙarara dole a nuna rashin jin daɗi da rashin jajircewa da gwamnatin tarayya da ƙungiyar suka yi wajen cimma yarjejeniya da kawo ƙarshen yajin aikin. Gwamnati da ASUU sun kuma nuna rashin tausayawa halin da iyaye da ɗalibai ke ciki da kuma neman ilimi mai inganci ga matasanmu. A ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne ƙungiyar malaman jami'o'i ta Nijeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargaɗi…
