04
Sep
Gidauniyar Tallafawa Mabuƙata Daga Tushe, wato Grassroot Care and Aid Foundation ƙarƙashin jagorancin shugaban gidauniyar Amb Auwal Muhd Ɗanlarabawa ta yi kira ga Gwamnatin Jihar ta Kano a kan wannan yanayi da ake ciki a wannan lokaci na damuna. Muna kira ne ga Gwamnatin Jihar da ta duba mummunan yanayin da Jihar ke ciki na ambaliyar ruwa a kusan kowanne sassa na titunan Jihar wanda ya hada da kasuwanni har ma da unguwanni, kuma hakan na barazana da makomar Jihar tare da asarar rayuka da Kuma dukiyoyin al'umma. Tabbas wannan yanayi ya tayar da hankula sosai duba ga ba'a taɓa…
