31
Aug
Daga AMINU ƊAN ALMAJIRI Zuwa ga Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Da Fatan kana nan cikin ƙoshin Lafiya. Dalilin Rubuta Maka Wannan saƙo shi ne, a yau na ci karo da wani labari na wani gini da kake mai suna 'Kano Emirate Mega Secondary School'. Haƙiƙa kam ginin ya yi kyau, ga shi na ga an ce sauran gundumomin Kano duk ana irin wannan gini, Allah Ya taimaka. Sai dai hanzari ba gudu ba ya Malam Gwamna… A Kano muna da makarantu daban-daban da suka lalace, wasu gyaran nasu kaɗan ne, wasu kuwa ginin ne yake…
